< Deuteronomii 28 >

1 Si autem audieris vocem Domini Dei tui, ut facias atque custodias omnia mandata eius, quae ego praecipio tibi hodie, faciet te Dominus Deus tuus excelsiorem cunctis gentibus, quae versantur in terra.
In kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuka bi dukan umarnan da na ba ku a yau, Ubangiji Allahnku zai sa ku bisa dukan al’ummai a duniya.
2 Venientque super te universae benedictiones istae, et apprehendent te: si tamen praecepta eius audieris.
Dukan waɗannan albarku za su sauko muku, su zama naku, in kuka yi biyayya ga Ubangiji Allahnku.
3 Benedictus tu in civitate, et benedictus in agro.
Za ku zama masu albarka a cikin birni, za ku kuma zama masu albarka har a ƙauye.
4 Benedictus fructus ventris tui, et fructus terrae tuae, fructusque iumentorum tuorum, greges armentorum tuorum, et caulae ovium tuarum.
’Ya’yanku za su zama masu albarka, haka ma hatsin gonakinku da kuma’ya’yan dabbobinku, wato,’ya’yan shanu da’yan tumakinku.
5 Benedicta horrea tua, et benedictae reliquiae tuae.
Za a albarkaci kwandonku da kwanon kwaɓan kullunku.
6 Benedictus eris tu ingrediens et egrediens.
Za ku zama masu albarka sa’ad da kuka shiga, za ku kuma zama masu albarka sa’ad da kuka fita.
7 Dabit Dominus inimicos tuos, qui consurgunt adversum te, corruentes in conspectu tuo: per unam viam venient contra te, et per septem fugient a facie tua.
A gabanku, Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gāban da za su taso suna gāba da ku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.
8 Emittet Dominus benedictionem super cellaria tua, et super omnia opera manuum tuarum: benedicetque tibi in terra, quam acceperis.
Ubangiji zai aika da albarka a rumbunanku da kuma a bisa kome da kuka sa hannunku a kai. Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a ƙasar da yake ba ku.
9 Suscitabit te Dominus sibi in populum sanctum, sicut iuravit tibi: si custodieris mandata Domini Dei tui, et ambulaveris in viis eius.
Ubangiji zai kafa ku kamar mutanensa masu tsarki, kamar yadda ya yi alkawari da rantsuwa, in kun kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi tafiya a hanyoyinsa.
10 Videbuntque omnes terrarum populi quod nomen Domini invocatum sit super te, et timebunt te.
Sa’an nan dukan mutane a duniya za su ga cewa ana kiranku da sunan Ubangiji, za su kuwa ji tsoronku.
11 Abundare te faciet Dominus omnibus bonis, fructu uteri tui, et fructu iumentorum tuorum, fructu terrae tuae, quam iuravit Dominus patribus tuis ut daret tibi.
Ubangiji zai azurta ku sosai, a’ya’yan cikinku, a’ya’yan dabbobinku da kuma a hatsin gonarku, a cikin ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku.
12 Aperiet Dominus thesaurum suum optimum, caelum, ut tribuat pluviam terrae tuae in tempore suo: benedicetque cunctis operibus manuum tuarum. Et foenerabis gentibus multis, et ipse a nullo foenus accipies.
Ubangiji zai buɗe sammai, wurin ajiyarsa mai yalwa, don yă aika da ruwan sama a gonarku a lokacinsa, yă kuma albarkaci dukan aikin hannuwanku. Za ku ba wa al’ummai masu yawa rance, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba.
13 Constituet te Dominus in caput, et non in caudam: et eris semper supra, et non subter: si tamen audieris mandata Domini Dei tui quae ego praecipio tibi hodie, et custodieris et feceris,
Ubangiji zai sa ku zama kai, ba wutsiya ba. In kun mai da hankali ga umarnan Ubangiji Allahnku da nake ba ku a wannan rana, kuka kuma lura, kuka bi su, kullum za ku kasance a bisa, ba a ƙasa ba.
14 ac non declinaveris ab eis nec ad dexteram, nec ad sinistram, nec secutus fueris deos alienos, neque colueris eos.
Kada ku kauce zuwa dama ko zuwa hagu daga umarnan da na ba ku a yau, har ku bi waɗansu alloli kuna yin musu sujada.
15 Quod si audire nolueris vocem Domini Dei tui, ut custodias, et facias omnia mandata eius et ceremonias, quas ego praecipio tibi hodie, venient super te omnes maledictiones istae, et apprehendent te.
Amma fa, in ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku ba, ba ku kuma lura kun bi dukan umarnansa da ƙa’idodin da nake ba ku a yau ba, dukan la’anan nan za su zo a bisanku, su kuma same ku.
16 Maledictus eris in civitate, maledictus in agro.
Za ku zama la’anannu a birni da kuma a ƙauye.
17 Maledictum horreum tuum, et maledictae reliquiae tuae.
Za a la’anta kwandonku da kwanon kwaɓan kullunku.
18 Maledictus fructus ventris tui, et fructus terrae tuae, armenta boum tuorum, et greges ovium tuarum.
Za a la’anta’ya’yan cikinku, haka ma hatsin gonarku, da’ya’yan shanunku da’yan tumakinku.
19 Maledictus eris ingrediens, et maledictus egrediens.
Za a la’anta ku sa’ad da kuka shiga da sa’ad da kuka fita.
20 Mittet Dominus super te famem et esuriem, et increpationem in omnia opera tua, quae tu facies: donec conterat te, et perdat velociter, propter adinventiones tuas pessimas in quibus reliquisti me.
Ubangiji zai aiko muku da la’ana, da ruɗewa, da damuwa cikin dukan abin da za ku yi, har ya hallaka ku, ku lalace da sauri saboda mugayen ayyukanku, domin kuma kuka rabu da ni.
21 Adiungat tibi Dominus pestilentiam, donec consumat te de terra, ad quam ingredieris possidendam.
Ubangiji zai aiko muku da annoba wadda za tă manne muku, tă cinye ku cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta.
22 Percutiat te Dominus egestate, febri et frigore, ardore et aestu, et aere corrupto ac rubigine, et persequatur donec pereas.
Ubangiji zai buga ku da cuta mai lalacewa, da zazzaɓi, da ƙuna, da zafin rana, da fāri, da burtuntuna, da fumfuna, waɗanda za su azabtar da ku sai kun hallaka.
23 Sit caelum, quod supra te est, aeneum: et terra, quam calcas, ferrea.
Girgijen da yake bisanku zai zama tagulla, ƙasar da take ƙarƙashinku za tă zama ƙarfe.
24 Det Dominus imbrem terrae tuae pulverem, et de caelo descendat super te cinis, donec conteraris.
Ubangiji zai juye ruwan saman ƙasarku yă zama ƙura da gari; zai sauko daga gizagizai har sai kun hallaka.
25 Tradat te Dominus corruentem ante hostes tuos. per unam viam egrediaris contra eos, et per septem fugias, et dispergaris per omnia regna terrae.
Ubangiji zai sa a rinjaye ku a gaban abokan gābanku. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya.
26 sitque cadaver tuum in escam cunctis volatilibus caeli, et bestiis terrae, et non sit qui abigat.
Gawawwakinku za su zama abincin dukan tsuntsayen sarari da namun duniya, ba kuwa wanda zai kore su.
27 Percutiat te Dominus ulcere Aegypti, et partem corporis, per quam stercora egeruntur, scabie quoque et prurigine: ita ut curari nequeas.
Ubangiji zai buge ku da maruran Masar, da ƙazuwa, da kuma ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba
28 Percutiat te Dominus amentia et caecitate ac furore mentis,
Ubangiji zai buge ku da hauka, makanta, da rikicewar hankali.
29 et palpes in meridie sicut palpare solet caecus in tenebris, et non dirigas vias tuas. Omnique tempore calumniam sustineas, et opprimaris violentia, nec habeas qui liberet te.
Da tsakar rana za ku riƙa lallubawa kamar makaho. Za ku zama marasa nasara a cikin kome da kuka yi; kowace rana za a zalunce ku, a kuma yi muku ƙwace, ba tare da wani ya cece ku ba.
30 Uxorem accipias, et alius dormiat cum ea. Domum aedifices, et non habites in ea. Plantes vineam, et non vindemies eam.
Za ku yi tashin yarinya, amma wani ne zai ɗauke ta yă kwana da ita. Za ku gina gida amma wani ne zai zauna a ciki. Za ku shuka inabi, amma ba za ku ma fara jin daɗin’ya’yansa ba.
31 Bos tuus immoletur coram te, et non comedas ex eo. Asinus tuus rapiatur in conspectu tuo, et non reddatur tibi. Oves tuae dentur inimicis tuis, et non sit qui te adiuvet.
Za a yanka sanku a idanunku, amma ba za ko ci wani abu a cikinsa ba. Za a ƙwace jakinku ƙiri-ƙiri, amma ba za a mayar muku da shi ba. Za a ba da tumakinku ga abokan gābanku, kuma ba kowa da zai cece su.
32 Filii tui et filiae tuae tradantur alteri populo, videntibus oculis tuis, et deficientibus ad conspectum eorum tota die, et non sit fortitudo in manu tua.
Za a ba da’ya’yanku maza da mata ga wata al’umma, za ku kuma yi ta zuba idanunku kuna neman su kullayaumi, amma a banza, domin ba ku da ikon yin kome.
33 Fructus terrae tuae, et omnes labores tuos comedat populus, quem ignoras: et sis semper calumniam sustinens, et oppressus cunctis diebus,
Mutanen da ba ku sani ba za su ci kayan gonarku da amfanin wahalarku, za a yi ta cucinku, ana kuma danne ku kullum.
34 et stupens ad terrorem eorum quae videbunt oculi tui.
Abubuwan da za ku gani za su sa ku yi hauka.
35 Percutiat te Dominus ulcere pessimo in genibus et in suris, sanarique non possis a planta pedis usque ad verticem tuum.
Ubangiji zai buge gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai masu zafi da ba za a iya warkar da su ba, za su yaɗu daga tafin ƙafafu zuwa bisa kanku.
36 Ducet te Dominus, et regem tuum, quem constitueris super te, in gentem, quam ignoras tu et patres tui: et servies ibi diis alienis, ligno et lapidi.
Ubangiji zai kore ku, ku da sarkin da kuka naɗa a bisanku zuwa al’ummar da ku, ko kakanninku ba su sani ba. A can za ku yi wa waɗansu alloli sujada, allolin itace da na dutse.
37 Et eris perditus in proverbium ac fabulam omnibus populis, ad quos te introduxerit Dominus.
Za ku zama abin ƙi, abin dariya, da kuma abin habaici ga dukan al’ummai inda Ubangiji zai kore ku zuwa.
38 Sementem multam iacies in terram, et modicum congregabis: quia locustae devorabunt omnia.
Za ku shuka iri da yawa a gona, amma za ku girbe kaɗan, domin fāra za su cinye su.
39 Vineam plantabis, et fodies: et vinum non bibes, nec colliges ex ea quippiam: quoniam vastabitur vermibus.
Za ku shuka inabi ku kuma yi musu banƙasa, amma ba za ku sha ruwan inabin ba, domin tsutsotsi za su cinye su.
40 Olivas habebis in omnibus terminis tuis, et non ungeris oleo: quia defluent, et deperibunt.
Za ku kasance da itatuwan zaitun ko’ina a ƙasarku, amma ba za ku yi amfani da mansu ba, domin’ya’yan zaitun za su kakkaɓe.
41 Filios generabis et filias, et non frueris eis: quoniam ducentur in captivitatem.
Za ku haifi’ya’ya maza da mata, amma za su zama naku ba, domin za a kai su bauta.
42 Omnes arbores tuas et fruges terrae tuae rubigo consumet.
Tarin fāra za su mamaye dukan itatuwanku da kuma hatsin gonarku.
43 Advena, qui tecum versatur in terra, ascendet super te, eritque sublimior: tu autem descendes, et eris inferior.
Baƙin da suke tare da ku, za su yi ta ƙaruwa, ku kuwa za ku yi ta komawa baya-baya.
44 Ipse foenerabit tibi, et tu non foenerabis ei. Ipse erit in caput, et tu eris in caudam.
Za su ba ku bashi, amma ba za ku ba su bashi ba. Za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya.
45 Et venient super te omnes maledictiones istae, et persequentes apprehendent te, donec intereas: quia non audisti vocem Domini Dei tui, nec servasti mandata eius et ceremonias, quas praecepit tibi.
Dukan waɗannan la’anoni za su sauko a kanku. Za su bi ku, su same ku, sai an hallaka ku, domin ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da ya ba ku ba.
46 Et erunt in te signa atque prodigia, et in semine tuo usque in sempiternum:
Za su zama alamu da al’ajabi gare ku da kuma zuriyarku har abada.
47 eo quod non servieris Domino Deo tuo in gaudio, cordisque laetitia, propter rerum omnium abundantiam:
Gama ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da farin ciki da kuma murna a lokacin wadata ba,
48 servies inimico tuo, quem immittet tibi Dominus, in fame, et siti, et nuditate, et omni penuria: et ponet iugum ferreum super cervicem tuam, donec te conterat.
saboda haka a cikin yunwa da ƙishirwa, cikin tsiraici da mugun talauci, za ku bauta wa abokan gāban da Ubangiji ya aiko muku. Zai sa karkiyar ƙarfe a wuyanku har sai ya hallaka ku ƙaf.
49 Adducet Dominus super te Gentem de longinquo, et de extremis terrae finibus in similitudinem aquilae volantis cum impetu: cuius linguam intelligere non possis:
Ubangiji zai kawo al’umma daga nesa, daga iyakar duniya, ta sauko a kanku kamar gaggafa, al’ummar da ba ku san yarenta ba,
50 Gentem procacissimam, quae non deferat seni, nec misereatur parvuli,
al’umma mai zafin hali wadda ba ta ba wa tsofaffi girma, kuma ba ta tausayin yara.
51 et devoret fructum iumentorum tuorum, ac fruges Terrae tuae: donec intereas, et non relinquat tibi triticum, vinum, et oleum, armenta boum, et greges ovium: donec te disperdat,
Za su cinye’ya’yan dabbobinku da hatsin gonarku sai an hallaka ku. Ba za su rage ko ƙwayar hatsi, ko sabon ruwan inabi, ko mai ba, ba kuwa za a bar’yan tumakinku ba, sai an lalatar da ku.
52 et conterat in cunctis urbibus tuis, et destruantur muri tui firmi atque sublimes, in quibus habebas fiduciam in omni Terra tua. Obsideberis intra portas tuas in omni Terra tua, quam dabit tibi Dominus Deus tuus:
Za su kuwa kewaye ku a dukan garuruwanku, har sai katangarku masu tsayi wadda kuke dogara gare su, sun fāɗi ko’ina a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.
53 et comedes fructum uteri tui, et carnes filiorum tuorum et filiarum tuarum, quas dederit tibi Dominus Deus tuus, in angustia et vastitate qua opprimet te hostis tuus.
Saboda wahalar da abokan gābanku za su gasa muku a lokacin kwanto, za ku ci’ya’yan cikinku, naman’ya’yanku maza da mata waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku.
54 Homo delicatus in te, et luxuriosus valde, invidebit fratri suo, et uxori, quae cubat in sinu suo,
Kai, har da mutumin da ya fi hankali da kuma kirki a cikinku, ba zai ji tausayi ɗan’uwansa, ko matar da yake ƙauna, ko’ya’yansa da suka ragu ba,
55 ne det eis de carnibus filiorum suorum, quas comedet: eo quod nihil aliud habeat in obsidione et penuria, qua vastaverint te inimici tui intra omnes portas tuas.
ba kuwa zai ba waninsu wani naman’ya’yansa da yake ci ba. Gama dukan abin da ya rage masa ke nan saboda wahalar da abokan gābanku za su gasa muku a lokacin da ake kwanton wa dukan biranenku.
56 Tenera mulier et delicata, quae super terram ingredi non valebat, nec pedis vestigium figere propter mollitiem et teneritudinem nimiam, invidebit viro suo, qui cubat in sinu eius, super filii et filiae carnibus,
Mace mafi hankali da kuma kirki a cikinku, kai, mafi hankali da kirki da ba ta ma karambanin taɓa ƙasa da tafin ƙafarta, za tă hana wa mijinta da take ƙauna, da kuma ɗanta, ko’yarta abinci.
57 et illuvie secundinarum, quae egrediuntur de medio feminum eius, et super liberis qui eadem hora nati sunt. comedent enim eos clam propter rerum omnium penuriam in obsidione et vastitate, qua opprimet te inimicus tuus intra portas tuas.
A ɓoye za tă ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da’ya’yan da za tă haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da abokan gābanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani.
58 Nisi custodieris, et feceris omnia verba legis huius, quae scripta sunt in hoc volumine, et timueris nomen eius gloriosum et terribile, hoc est, Dominum Deum tuum:
In ba ku lura kuka bi dukan kalmomi wannan doka, waɗanda an rubuta a wannan littafi ba, ba ku kuma girmama wannan suna mai ɗaukaka da kuma mai banrazana na Ubangiji Allahnku ba,
59 augebit Dominus plagas tuas, et plagas seminis tui, plagas magnas et perseverantes, infirmitates pessimas et perpetuas.
Ubangiji zai aika da annoba masu zafi a kanku da zuriyarku, masifu masu zafi waɗanda za su daɗe, da mugayen cututtuka waɗanda ba sa kawuwa.
60 et convertet in te omnes afflictiones Aegypti, quas timuisti, et adhaerebunt tibi:
Zai kawo muku dukan cututtukan Masar da kuke tsoro, za su kuwa manne muku.
61 Insuper et universos languores, et plagas, quae non sunt scriptae in volumine legis huius, inducet Dominus super te, donec te conterat:
Ubangiji kuma zai kawo muku kowane irin ciwo da masifar da ba a rubuta a cikin wannan Littafin Doka ba, har sai an hallaka ku.
62 et remanebitis pauci numero, qui prius eratis sicut astra caeli prae multitudine, quoniam non audisti vocem Domini Dei tui.
Ku da kuke da yawa kamar taurari a sarari za ku ragu ku zama kaɗan, domin ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku ba.
63 Et sicut ante laetatus est Dominus super vos, bene vobis faciens, vosque multiplicans: sic laetabitur disperdens vos atque subvertens, ut auferamini de Terra, ad quam ingredieris possidendam.
Kamar yadda ya gamshi Ubangiji ya sa kuka yi arziki kuka kuma ƙaru, haka zai gamshe shi yă lalatar yă kuma hallaka ku. Za a tumɓuke ku daga ƙasar da kuke shiga ku mallaka.
64 Disperget te Dominus in omnes populos a summitate terrae usque ad terminos eius: et servies ibi diis alienis, quos et tu ignoras et patres tui, lignis et lapidibus.
Sa’an nan Ubangiji zai watsar da ku cikin dukan al’ummai, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. A can za ku bauta waɗansu alloli, allolin itace da na dutse, waɗanda ko ku, ko kakanninku, ba ku sani ba.
65 In gentibus quoque illis non quiesces, neque erit requies vestigio pedis tui. Dabit enim tibi Dominus ibi cor pavidum, et deficientes oculos, et animam consumptam moerore:
A cikin waɗancan al’ummai ba za ku sami hutu ba, ba wurin hutu wa tafin ƙafanku. A can Ubangiji zai sa fargaba a zuciyarku, yă sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu.
66 Et erit vita tua quasi pendens ante te. Timebis nocte et die, et non credes vitae tuae.
Za ku yi zama cikin damuwa kullum, cike da tsoro, dare da rana, ba tabbacin abin da zai faru da ranku.
67 Mane dices: Quis mihi det vesperum? et vespere: Quis mihi det mane? propter cordis tui formidinem, qua terreberis, et propter ea, quae tuis videbis oculis.
Da safe za ku ce, “Da ma yamma ne!” Da yamma kuma ku ce, “Da ma safiya ce!” Saboda tsoron da ya cika zukatanku da kuma abubuwan da idanunku za su gani.
68 Reducet te Dominus classibus in Aegyptum per viam, de qua dixit tibi ut eam amplius non videres. Ibi venderis inimicis tuis in servos et ancillas, et non erit qui emat.
Ubangiji zai komar da ku cikin jiragen ruwa zuwa Masar, tafiyar da na ce kada ku ƙara yi. A can za ku ba da kanku don sayarwa ga abokan gābanku a matsayin bayi maza da mata, amma ba wanda zai saye ku.

< Deuteronomii 28 >