< Ii Samuelis 16 >

1 Cumque David transisset paululum montis verticem, apparuit Siba puer Miphiboseth in occursum eius, cum duobus asinis, qui onerati erant ducentis panibus, et centum alligaturis uvae passae, et centum massis palatharum, et duobus utribus vini.
Sa’ad da Dawuda ya yi ɗan nesa da ƙwanƙolin, sai ga Ziba mai hidimar Mefiboshet, yana jira yă tarye shi. Yana da jerin jakuna da sirdi suna ɗauke da dunƙulen burodi ɗari biyu, da ƙosai busasshen inabi ɗari ɗaya, da kosan’ya’yan itace ɓaure guda ɗari, da salka ruwan inabi.
2 Et dixit rex Sibae. Quid sibi volunt haec? Responditque Siba: Domine mi rex, asini pro domesticis regis sunt, ut sedeant: panes et palathae ad vescendum pueris tuis: vinum autem ut bibat siquis defecerit in deserto.
Sarki ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo waɗannan?” Ziba ya ce, “Jakuna domin iyalin gidan sarki su hau ne, burodi da’ya’yan itace domin mutane su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suka gaji a hamada.”
3 Et ait rex: Ubi est filius domini tui? Responditque Siba regi: Remansit in Ierusalem, dicens: Hodie restituet mihi domus Israel regnum patris mei.
Sai sarki ya ce, “Ina jikar maigidanka?” Ziba ya ce, “Yana zaune a Urushalima gama yana tsammani cewa, ‘Yau gidan Isra’ila za su mayar mini da sarautar kakana.’”
4 Et ait rex Sibae: Tua sint omnia quae fuerunt Miphiboseth. Dixitque Siba: Oro ut inveniam gratiam coram te, domine mi rex.
Sai sarki ya ce wa Ziba, “Duk abin da yake na Mefiboshet, ya zama naka.” Ziba ya rusuna ya ce, “Bari in dinga samun tagomashi a gabanka ranka yă daɗe.”
5 Venit ergo rex David usque Bahurim: et ecce egrediebatur inde vir de cognatione domus Saul, nomine Semei, filius Gera, procedebatque egrediens, et maledicebat,
Yayinda Sarki Dawuda ya kusato Bahurim, sai ga wani mutumin dangin Shawulu ya fito daga can, sunansa Shimeyi ɗan Gera. Ya fito yana ta la’anta yayinda yake fitowa.
6 mittebatque lapides contra David, et contra universos servos regis David: omnis autem populus, et universi bellatores a dextro, et a sinistro latere regis incedebant.
Ya jajjefi Dawuda da dukan fadawan sarki da duwatsu, ko da yake sojoji da masu gadin sarki na musamman suna kewaye da sarki dama da hagu.
7 Ita autem loquebatur Semei cum malediceret regi: Egredere, egredere vir sanguinum, et vir Belial.
Yayinda yake la’antar, Shimeyi ya ce, “Tafi daga nan, tafi daga nan, mai kisankai, mutumin banza kawai!
8 Reddidit tibi Dominus universum sanguinem domus Saul: quoniam invasisti regnum pro eo, et dedit Dominus regnum in manu Absalom filii tui, et ecce premunt te mala tua, quoniam vir sanguinum es.
Ubangiji ya kama ka saboda alhakin jinin gidan Shawulu, wanda kake sarauta a maimakonsa. Ubangiji ya ba da masarautar ga ɗanka Absalom. Hallaka ta zo maka domin kai mai kisankai ne!”
9 Dixit autem Abisai filius Sarviae, regi: Quare maledicit canis hic moriturus domino meo regi? vadam, et amputabo caput eius.
Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce wa sarki, “Ranka yă daɗe, don me wannan mataccen kare yake la’antarka? Bari in je in datse kansa.”
10 Et ait rex: Quid mihi et vobis est filii Sarviae? dimittite eum, ut maledicat: Dominus enim praecepit ei ut malediceret David: et quis est qui audeat dicere, quare sic fecerit?
Amma sarki ya ce, “Ba ruwana da ku, ku’ya’yan Zeruhiya. Idan yana la’ana ne domin Ubangiji ya ce masa, ‘La’anci Dawuda,’ wa zai ce, ‘Don me kake haka?’”
11 Et ait rex Abisai, et universis servis suis: Ecce filius meus, qui egressus est de utero meo, quaerit animam meam: quanto magis hic filius Iemini? dimittite eum ut maledicat iuxta praeceptum Domini:
Sa’an nan Dawuda ya ce wa Abishai da dukan fadawansa, “Ɗana, na cikina, yana ƙoƙari yă kashe ni. Balle wannan mutumin Benyamin! Ku ƙyale shi, yă yi ta zargi, Ubangiji ne ya ce masa yă yi haka.
12 si forte respiciat Dominus afflictionem meam, et reddat mihi Dominus bonum pro maledictione hac hodierna.
Mai yiwuwa Ubangiji yă ga azabata, yă sāka mini da alheri saboda la’anar da nake sha a yau.”
13 Ambulabat itaque David et socii eius per viam cum eo. Semei autem per iugum montis ex latere, contra illum gradiebatur, maledicens, et mittens lapides adversum eum, terramque spargens.
Saboda haka Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu yayinda Shimeyi yana tafiya ɗaura da shi a gefen tudu, yana zagi, yana jifansa da duwatsu, yana tayar masa da ƙura.
14 Venit itaque rex, et universus populus cum eo lassus, et refocillati sunt ibi.
Sarki da dukan mutanen da suke tare da shi suka isa masauƙinsu a gajiye. A can fa ya huta.
15 Absalom autem et omnis populus eius ingressi sunt Ierusalem, sed et Achitophel cum eo.
Ana cikin haka, Absalom da dukan Isra’ila suka iso Urushalima, Ahitofel kuwa yana tare da shi.
16 Cum autem venisset Chusai Arachites amicus David ad Absalom, locutus est ad eum: Salve rex, salve rex.
Sai Hushai mutumin Arkitawa, abokin Dawuda ya je wurin Absalom ya ce masa, “Ran sarki yă daɗe! Ran sarki yă daɗe!”
17 Ad quem Absalom, Haec est, inquit, gratia tua ad amicum tuum? quare non ivisti cum amico tuo?
Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake nuna wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?”
18 Responditque Chusai ad Absalom: Nequaquam: quia illius ero, quem elegit Dominus, et omnis hic populus, et universus Israel, et cum eo manebo.
Hushai ya ce wa Absalom, “A’a, ai, wanda Ubangiji ya zaɓa ta wurin waɗannan mutane, da kuma ta wurin dukan mutane Isra’ila, shi zan zama nasa, zan kuma kasance tare da shi.
19 Sed ut et hoc inferam, cui ego serviturus sum? nonne filio regis? sicut parui patri tuo, ita parebo et tibi.
Ban da haka ma, wane ne zan bauta wa? Ashe, ba ɗan ne zan bauta wa ba? Kamar dai yadda na bauta wa mahaifinka, haka zan bauta maka.”
20 Dixit autem Absalom ad Achitophel: Inite consilium quid agere debeamus.
Absalom ya ce wa Ahitofel, “Ba mu shawararka. Me za mu yi?”
21 Et ait Achitophel ad Absalom: Ingredere ad concubinas patris tui, quas dimisit ad custodiendam domum: ut cum audierit omnis Israel quod foedaveris patrem tuum, roborentur tecum manus eorum.
Ahitofel ya ce wa Absalom, “Je ka kwana da ƙwarƙwaran mahaifinka waɗanda ya bari su lura da fada. Ta haka dukan Isra’ila za su ji cewa ka mai da kanka abin wari a hancin mahaifinka, dukan hannuwan waɗanda suke tare da kai kuwa za su sami ƙarfi.”
22 Tetenderunt ergo Absalom tabernaculum in solario, ingressusque est ad concubinas patris sui coram universo Israel.
Saboda haka suka kafa wa Absalom tenti a bisa rufin ɗaki, a can ya kwana da ƙwarƙwaran mahaifinsa a gaban dukan Isra’ila.
23 Consilium autem Achitophel, quod dabat in diebus illis, quasi siquis consuleret Deum: sic erat omne consilium Achitophel, et cum esset cum David, et cum esset cum Absalom.
To, a kwanakin nan shawarar da Ahitofel yakan bayar takan zama kamar wadda aka nemi daga Allah ne. Haka Dawuda da Absalom duk suke ɗaukan dukan shawarar Ahitofel.

< Ii Samuelis 16 >