< I Samuelis 18 >

1 Et factum est cum complesset loqui ad Saul: anima Ionathae conglutinata est animae David, et dilexit eum Ionathas quasi animam suam.
Bayan da Dawuda ya gama magana da Shawulu, sai Yonatan ɗan Shawulu ya ji zuciyarsa tana son Dawuda sosai. Yonatan kuwa yana ƙaunar Dawuda kamar ransa.
2 Tulitque eum Saul in die illa, et non concessit ei ut reverteretur in domum patris sui.
Tun daga wannan rana Shawulu ya zaunar da Dawuda tare da shi, bai bar shi ya koma gidan mahaifinsa ba.
3 Inierunt autem David et Ionathas foedus: diligebat enim eum quasi animam suam.
Yonatan kuma ya yi yarjejjeniya da Dawuda saboda yana ƙaunarsa kamar ransa.
4 Nam expoliavit se Ionathas tunica, qua erat indutus, et dedit eam David, et reliqua vestimenta sua usque ad gladium et arcum suum, et usque ad balteum.
Yonatan ya tuɓe doguwar taguwarsa da ya sa, ya ba wa Dawuda, tare da sulkensa, har ma da māshi da kibiyarsa, da kuma bel nasa.
5 Egrediebatur quoque David ad omnia quaecumque misisset eum Saul, et prudenter se agebat: posuitque eum Saul super viros belli, et acceptus erat in oculis universi populi, maximeque in conspectu famulorum Saul.
Duk abin da Shawulu ya aiki Dawuda yă yi yakan yi shi cikin aminci, har Shawulu ya ba shi babban makami a rundunarsa. Wannan ya faranta wa dukan mutane zuciya har ma da ma’aikatan Shawulu.
6 Porro cum reverteretur percusso Philisthaeo David, et ferret caput eius in Ierusalem egressae sunt mulieres de universis urbibus Israel, cantantes, chorosque ducentes in occursum Saul regis, in tympanis laetitiae, et in sistris.
Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa.
7 Et praecinebant mulieres ludentes, atque dicentes: Percussit Saul mille, et David decem millia.
Suna rawa suna cewa, “Shawulu ya kashe dubbansa, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”
8 Iratus est autem Saul nimis, et displicuit in oculis eius sermo iste: dixitque: Dederunt David decem millia, et mihi mille dederunt: quid ei superest, nisi solum regnum?
Shawulu kuwa ya ji fushi, wannan magana ba tă yi masa daɗi ba, ya yi tunani ya ce, “Suna yabon Dawuda cewa ya kashe dubun dubbai amma ni dubbai kawai. Me ya rage masa yanzu, in ba mulki ba?”
9 Non rectis ergo oculis Saul aspiciebat David a die illa, et deinceps.
Tun daga wannan lokaci zuwa gaba, Shawulu ya dinga kishin Dawuda.
10 Post diem autem alteram, invasit spiritus Dei malus Saul, et prophetabat in medio domus suae: David autem psallebat manu sua, sicut per singulos dies. tenebatque Saul lanceam,
Kashegari, mugun ruhu daga Allah ya fāɗo wa Shawulu da tsanani. Yana annabci a gidansa, Dawuda kuwa yana bugan molo kamar yadda ya saba. Shawulu yana riƙe da māshi a hannunsa.
11 et misit eam, putans quod configere posset David cum pariete: et declinavit David a facie eius secundo.
Da ƙarfi yana magana da kansa yana cewa, “Zan kafe Dawuda da bango.” Amma Dawuda ya bauɗe masa sau biyu.
12 Et timuit Saul David, eo quod Dominus esset cum eo, et a se recessisset.
Shawulu ya ji tsoron Dawuda don Ubangiji yana tare da shi, amma Ubangiji ya riga ya bar Shawulu.
13 Amovit ergo eum Saul a se, et fecit eum tribunum super mille viros: et egrediebatur, et intrabat in conspectu populi.
Saboda haka Shawulu bai yarda Dawuda yă zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban sojoji dubu. Dawuda kuwa ya riƙa bi da su yana kaiwa yana kuma da tare da su.
14 In omnibus quoque viis suis David prudenter agebat, et Dominus erat cum eo.
A kome da Dawuda ya yi yakan yi nasara gama Ubangiji yana tare da shi.
15 Vidit itaque Saul quod prudens esset nimis, et coepit cavere eum.
Da Shawulu ya ga yadda yake cin nasara, sai ya ji tsoronsa.
16 Omnis autem Israel et Iuda diligebat David: ipse enim ingrediebatur et egrediebatur ante eos.
Amma dukan Isra’ila da Yahuda suka ƙaunaci Dawuda gama yana bin da su a yaƙe-yaƙensu.
17 Dixitque Saul ad David: Ecce filia mea maior Merob, ipsam dabo tibi uxorem: tantummodo esto vir fortis, et praeliare bella Domini. Saul autem reputabat, dicens: Non sit manus mea in eo, sed sit super eum manus Philisthinorum.
Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.”
18 Ait autem David ad Saul: Quis ego sum, aut quae est vita mea, aut cognatio patris mei in Israel, ut fiam gener regis?
Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Wane ni, wa ya san iyayena ko kabilar iyayena a Isra’ila da zan zama surukin sarki?”
19 Factum est autem tempus cum deberet dari Merob filia Saul David, data est Hadrieli Molathitae uxor.
Da lokaci ya kai da Merab’yar Shawulu za tă yi aure da Dawuda, sai aka aurar da ita wa Adriyel na Mehola.
20 Dilexit autem David Michol filiam Saul alteram. Et nunciatum est Saul, et placuit ei.
Mikal’yar Shawulu kuwa tana ƙaunar Dawuda sosai. Da aka gaya wa Shawulu labarin, sai ya yi farin ciki, ya yi tunani ya ce,
21 Dixitque Saul: Dabo eam illi, ut fiat ei in scandalum, et sit super eum manus Philisthinorum. Dixitque Saul ad David: In duabus rebus gener meus eris hodie.
“Zan ba shi ita tă zama masa tarko, da haka Filistiyawa za su same shi.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Yanzu kana da dama sau na biyu ka zama surukina.”
22 Et mandavit Saul servis suis: Loquimini ad David clam me, dicentes: Ecce places regi, et omnes servi eius diligunt te. Nunc ergo esto gener regis.
Sai Shawulu ya umarci ma’aikatansa cewa, “Ku yi magana da Dawuda asirce ku ce, ‘Duba, sarki yana farin ciki da kai, dukan ma’aikatansa kuma suna sonka, ka yarda ka zama surukinsa.’”
23 Et locuti sunt servi Saul in auribus David omnia verba haec. Et ait David: Num parum videtur vobis, generum esse regis? Ego autem sum vir pauper et tenuis.
Suka sāke yi wa Dawuda wannan magana amma Dawuda ya ce, “Kuna tsammani abu mai sauƙi ne mutum yă zama surukin sarki? Ni talaka ne, kuma ba sananne ba.”
24 Et renunciaverunt servi Saul, dicentes: Huiuscemodi verba locutus est David.
Da ma’aikatan Shawulu suka gaya masa abin da Dawuda ya faɗa.
25 Dixit autem Saul: Sic loquimini ad David: Non habet rex sponsalia necesse, nisi tantum centum praeputia Philisthinorum, ut fiat ultio de inimicis regis. Porro Saul cogitabat tradere David in manus Philisthinorum.
Sai Shawulu ya ce, “Ku gaya wa Dawuda, ‘Sarki ba ya bukatan kuɗin auren’yarsa, sai dai loɓar Filistiyawa domin ramako a kan abokan gābansa.’” Shawulu yana shiri ne domin Dawuda yă fāɗa a hannun Filistiyawa.
26 Cumque renunciassent servi eius David verba, quae dixerat Saul, placuit sermo in oculis David, ut fieret gener regis.
Da ma’aikatan suka gaya wa Dawuda waɗannan abubuwa, sai ya yi murna don zai zama surukin sarki. Amma kafin lokacin yă cika,
27 Et post paucos dies surgens David, abiit cum viris, qui sub eo erant. Et percussit ex Philisthiim ducentos viros, et attulit eorum praeputia, et annumeravit ea regi, ut esset gener eius. Dedit itaque Saul ei Michol filiam suam uxorem.
Dawuda da mutanensa suka fita suka kashe Filistiyawa ɗari biyu, suka kawo loɓar suka miƙa wa sarki, domin yă zama surukin sarki. Sai Shawulu ya ba da’yarsa Mikal aure ga Dawuda.
28 Et vidit Saul, et intellexit quod Dominus esset cum David. Michol autem filia Saul diligebat eum.
Da Shawulu ya gane Ubangiji yana tare da Dawuda,’yarsa Mikal kuma tana ƙaunarsa,
29 Et Saul magis coepit timere David: factusque est Saul inimicus David cunctis diebus.
sai Shawulu ya ƙara jin tsoron Dawuda har ya zama maƙiyinsa a dukan sauran rayuwarsa.
30 Et egressi sunt principes Philisthinorum. a principio autem egressionis eorum, prudentius se gerebat David quam omnes servi Saul, et celebre factum est nomen eius nimis.
Manyan sojojin Filistiyawa suka yi ta fita suna yaƙi da Isra’ilawa, amma kullum Dawuda yakan sami nasara fiye da sauran manyan sojojin Shawulu. Ta haka ya yi suna ƙwarai.

< I Samuelis 18 >