< Mattheum 19 >

1 Et factum est, cum consummasset Jesus sermones istos, migravit a Galilæa, et venit in fines Judææ trans Jordanem,
Sai ya zama sa'adda Yesu ya gama wadannan maganganu, sai ya bar Galili ya zo kan iyakokin Yahudiya, ketaren kogin Urdun.
2 et secutæ sunt eum turbæ multæ, et curavit eos ibi.
Taro mai yawa suka bi shi, ya kuma warkar da su a wurin.
3 Et accesserunt ad eum pharisæi tentantes eum, et dicentes: Si licet homini dimittere uxorem suam, quacumque ex causa?
Farisawa suka zo wurinsa, suna gwada shi, suka ce masa, ''Ya hallata bisa ga doka mutum ya saki matarsa don kowanne dalili?''
4 Qui respondens, ait eis: Non legistis, quia qui fecit hominem ab initio, masculum et feminam fecit eos? Et dixit:
Yesu ya amsa ya ce, ''Baku karanta ba, cewa shi wanda ya yi su tun farko ya yi su miji da mace?
5 Propter hoc dimittet homo patrem, et matrem, et adhærebit uxori suæ, et erunt duo in carne una.
Shi wanda ya yi su kuma ya ce, “Saboda wannan dalilin, mutum zai rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya hade da matarsa, su biyun su zama jiki daya?”
6 Itaque jam non sunt duo, sed una caro. Quod ergo Deus conjunxit, homo non separet.
Su ba biyu ba ne kuma, amma jiki daya. Don haka, duk abin da Allah ya hada, kada wani ya raba.''
7 Dicunt illi: Quid ergo Moyses mandavit dare libellum repudii, et dimittere?
Sai suka ce masa, ''To me yasa Musa ya umarcemu mu bada takardar saki, mu kuma kore ta?''
8 Ait illis: Quoniam Moyses ad duritiam cordis vestri permisit vobis dimittere uxores vestras: ab initio autem non fuit sic.
Sai ya ce masu, ''Saboda taurin zuciyarku, shi yasa Musa ya yarda maku ku saki matanku, amma da farko ba haka yake ba.
9 Dico autem vobis, quia quicumque dimiserit uxorem suam, nisi ob fornicationem, et aliam duxerit, mœchatur: et qui dimissam duxerit, mœchatur.
Ina gaya maku, duk wanda ya saki matarsa in ba saboda zina ba, ya kuma auri wata, yana zina kenan. Wanda kuma ya auri macen da aka saka, yana aikata zina.''
10 Dicunt ei discipuli ejus: Si ita est causa hominis cum uxore, non expedit nubere.
Almajiran suka ce wa Yesu, ''Idan haka yake game da mutum da matarsa, ba kyau ayi aure ba.''
11 Qui dixit illis: Non omnes capiunt verbum istud, sed quibus datum est.
Amma Yesu yace masu, ''Ba kowa ne zai karbi wannan koyarwa ba, amma sai wadanda an yardar masu su karbe ta.
12 Sunt enim eunuchi, qui de matris utero sic nati sunt: et sunt eunuchi, qui facti sunt ab hominibus: et sunt eunuchi, qui seipsos castraverunt propter regnum cælorum. Qui potest capere capiat.
Akwai wadanda aka haife su babanni. Akwai wadanda mutane ne suka maida su babanni. Sa'annan akwai wadanda sun mayar da kansu babanni saboda mulkin sama. Duk wanda zai iya karbar wannan koyarwa, ya karba.''
13 Tunc oblati sunt ei parvuli, ut manus eis imponeret, et oraret. Discipuli autem increpabant eos.
Sai aka kawo masa yara kanana don ya dibiya hannuwansa akansu, yayi masu addu'a, amma almajiran suka kwabe su.
14 Jesus vero ait eis: Sinite parvulos, et nolite eos prohibere ad me venire: talium est enim regnum cælorum.
Amma Yesu ya ce masu, ''Ku bar yara kanana, kada ku hana su zuwa wuri na, domin mulkin sama na irinsu ne.''
15 Et cum imposuisset eis manus, abiit inde.
Ya sa hannuwa akan su, sa'annan ya bar wurin.
16 Et ecce unus accedens, ait illi: Magister bone, quid boni faciam ut habeam vitam æternam? (aiōnios g166)
Sai wani mutum ya zo wurin Yesu, ya ce, ''Malam, wanne ayyuka nagari ne zan yi domin in sami rai madawwami?'' (aiōnios g166)
17 Qui dixit ei: Quid me interrogas de bono? Unus est bonus, Deus. Si autem vis ad vitam ingredi, serva mandata.
Yesu ya ce masa, ''Me yasa kake tambaya ta game da abin da ke nagari? Daya ne kawai ke nagari, amma idan kana so ka shiga cikin rai, ka kiyaye dokokin.''
18 Dicit illi: Quæ? Jesus autem dixit: Non homicidium facies; non adulterabis; non facies furtum; non falsum testimonium dices;
Mutumin ya ce masa, ''Wadanne dokokin?'' Yesu ya ce masa, ''Kada kayi kisa, kada kayi zina, kada kayi sata, kada kayi shaidar zur,
19 honora patrem tuum, et matrem tuam, et diliges proximum tuum sicut teipsum.
ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.''
20 Dicit illi adolescens: Omnia hæc custodivi a juventute mea: quid adhuc mihi deest?
Saurayin nan ya ce masa, ''Ai na kiyaye duk wadannan. Me nake bukata kuma?''
21 Ait illi Jesus: Si vis perfectus esse, vade, vende quæ habes, et da pauperibus, et habebis thesaurum in cælo: et veni, sequere me.
Yesu ya ce masa, ''Idan kana so ka zama cikakke, ka tafi ka sayar da mallakarka, ka kuma ba matalauta, zaka sami dukiya a sama. Sa'annan ka zo ka biyo ni.''
22 Cum audisset autem adolescens verbum, abiit tristis: erat enim habens multas possessiones.
Amma da saurayin nan ya ji abin da Yesu ya fada, ya koma da bakin ciki, domin shi mai arziki ne kwarai.
23 Jesus autem dixit discipulis suis: Amen dico vobis, quia dives difficile intrabit in regnum cælorum.
Yesu ya ce wa almajiransa, ''Hakika ina gaya maku, zai zama da wuya mai arziki ya shiga mulkin sama.
24 Et iterum dico vobis: Facilius est camelum per foramen acus transire, quam divitem intrare in regnum cælorum.
Ina sake gaya maku, zai fi wa rakumi sauki ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.''
25 Auditis autem his, discipuli mirabantur valde, dicentes: Quis ergo poterit salvus esse?
Da almajiran sun ji haka, suka yi mamaki kwarai da gaske, suka ce, ''Wanene zai sami ceto?''
26 Aspiciens autem Jesus, dixit illis: Apud homines hoc impossibile est: apud Deum autem omnia possibilia sunt.
Yesu ya dube su, ya ce, ''A wurin mutane wannan ba zai yiwu ba, amma a wurin Allah, kome mai yiwuwa ne.''
27 Tunc respondens Petrus, dixit ei: Ecce nos reliquimus omnia, et secuti sumus te: quid ergo erit nobis?
Sai Bitrus ya amsa ya ce masa, ''Duba, mun bar kome da kome mun bi ka. To me za mu samu?''
28 Jesus autem dixit illis: Amen dico vobis, quod vos, qui secuti estis me, in regeneratione cum sederit Filius hominis in sede majestatis suæ, sedebitis et vos super sedes duodecim, judicantes duodecim tribus Israël.
Yesu ya ce masu, ''Hakika ina gaya maku, ku da kuka bi ni, a sabuwar haihuwa, lokacin da Dan Mutum ya zauna a kursiyin daukakarsa, ku ma zaku zauna a kursiyoyi goma sha biyu, kuna shari'anta kabilu goma sha biyu na Isra'ila.
29 Et omnis qui reliquerit domum, vel fratres, aut sorores, aut patrem, aut matrem, aut uxorem, aut filios, aut agros propter nomen meum, centuplum accipiet, et vitam æternam possidebit. (aiōnios g166)
Duk wanda ya bar gidaje, 'yan'uwa maza, 'yan'uwa mata, mahaifi, mahaifiya, 'ya'ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkin su dari, ya kuma gaji rai madawwami. (aiōnios g166)
30 Multi autem erunt primi novissimi, et novissimi primi.
Amma dayawa dake farko yanzu, za su zama na karshe, dayawa dake karshe kuma, su zama na farko.

< Mattheum 19 >