< Lucam 18 >
1 Dicebat autem et parabolam ad illos, quoniam oportet semper orare et non deficere,
Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a kada kuma su karaya,
2 dicens: Judex quidam erat in quadam civitate, qui Deum non timebat, et hominem non reverebatur.
yace, “A wani gari an yi wani alkali mara tsoron Allah, kuma baya ganin darajan mutane.
3 Vidua autem quædam erat in civitate illa, et veniebat ad eum, dicens: Vindica me de adversario meo.
Akwai wata mace gwauruwa a wannan garin, wadda ta rika zuwa wurinsa, tana ce masa, 'Ka taimake ni yanda zan sami adalci a kan abokin gaba na.'
4 Et nolebat per multum tempus. Post hæc autem dixit intra se: Etsi Deum non timeo, nec hominem revereor:
An dade bai so ya taimaka mata, amma daga baya sai ya ce a ransa, 'ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma darajanta mutane,
5 tamen quia molesta est mihi hæc vidua, vindicabo illam, ne in novissimo veniens sugillet me.
duk da haka saboda gwauruwar nan ta dame ni, zan taimake ta domin ta sami adalci, yadda ba za ta gajiyar da ni da zuwanta wurina ba.'”
6 Ait autem Dominus: Audite quid judex iniquitatis dicit:
Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alkalin nan marar gaskiya ya fada.
7 Deus autem non faciet vindictam electorum suorum clamantium ad se die ac nocte, et patientiam habebit in illis?
A yanzu Allah ba zai biya wa zababbunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?
8 Dico vobis quia cito faciet vindictam illorum. Verumtamen Filius hominis veniens, putas, inveniet fidem in terra?
Ina gaya maku, zai biya masu hakkin su da wuri. Amma sa'adda Dan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya?”
9 Dixit autem et ad quosdam qui in se confidebant tamquam justi, et aspernabantur ceteros, parabolam istam:
Ya sake ba da misalin nan ga wadansu masu amincewa da kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane,
10 Duo homines ascenderunt in templum ut orarent: unus pharisæus et alter publicanus.
“Wadansu mutane biyu suka shiga haikali domin yin addu'a - daya Bafarise, dayan kuma mai karbar haraji ne.
11 Pharisæus stans, hæc apud se orabat: Deus, gratias ago tibi, quia non sum sicut ceteri hominum: raptores, injusti, adulteri, velut etiam hic publicanus:
Sai Bafarisen ya mike, ya yi addu'a a kan wadannan abubuwa game da kansa, 'Allah, na gode maka, da cewa ni ba kamar sauran mutane dake mazambata ba, ko marasa adalci, ko mazinata, ko kamar wannan mai karbar harajin.
12 jejuno bis in sabbato, decimas do omnium quæ possideo.
Duk mako ina azumi sau biyu. Nakan bayar da zakkar dukan abin da na samu.'
13 Et publicanus a longe stans, nolebat nec oculos ad cælum levare: sed percutiebat pectus suum, dicens: Deus propitius esto mihi peccatori.
Amma mai karbar harajin kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya daga kai sama ba, sai dai yana bugun kirjin sa, yana cewa, 'Allah, ka yi mini jinkai, ni mai zunubi.'
14 Dico vobis, descendit hic justificatus in domum suam ab illo: quia omnis qui se exaltat, humiliabitur, et qui se humiliat, exaltabitur.
Ina gaya maku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar dayan ba, domin dukan wanda ya daukaka kansa, za a kaskantar da shi, amma duk wanda kaskantar da kansa kuwa daukaka shi za a yi.”
15 Afferebant autem ad illum et infantes, ut eos tangeret. Quod cum viderent discipuli, increpabant illos.
Sai mutanen suka kawo masa jariransu, domin ya taba su, da almajiransa suka ga haka, sai suka kwabe su.
16 Jesus autem convocans illos, dixit: Sinite pueros venire ad me, et nolite vetare eos: talium est enim regnum Dei.
Amma Yesu ya kira su wurinsa, ya ce, “Ku bar yara kanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai mulkin Allah na irin su ne.
17 Amen dico vobis, quicumque non acceperit regnum Dei sicut puer, non intrabit in illud.
Gaskiya ina gaya maku, duk wanda bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, lallai ba zai shige shi ba.”
18 Et interrogavit eum quidam princeps, dicens: Magister bone, quid faciens vitam æternam possidebo? (aiōnios )
Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce “Malam managarci, me zan yi in gaji rai Madawwami?” (aiōnios )
19 Dixit autem ei Jesus: Quid me dicis bonum? nemo bonus nisi solus Deus.
Yesu ya ce masa, “Don me ka kira ni managarci? Babu wani managarci sai Allah kadai.
20 Mandata nosti: non occides; non mœchaberis; non furtum facies; non falsum testimonium dices; honora patrem tuum et matrem.
Ka dai san dokokin - kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar karya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.”
21 Qui ait: Hæc omnia custodivi a juventute mea.
Sai shugaban ya ce, “Dukan wadannan abubuwa na kiyaye su tun a kuruciya ta.”
22 Quo audito, Jesus ait ei: Adhuc unum tibi deest: omnia quæcumque habes vende, et da pauperibus, et habebis thesaurum in cælo: et veni, sequere me.
Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Abu daya ne kadai ya rage maka. Dole ne ka sayar da dukan mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka kuma sami wadata a sama - sa'annan ka zo ka biyoni.”
23 His ille auditis, contristatus est: quia dives erat valde.
Amma da mai arzikin ya ji wadannan abubuwa, sai yayi bakin ciki kwarai, don shi mai arziki ne sosai.
24 Videns autem Jesus illum tristem factum, dixit: Quam difficile, qui pecunias habent, in regnum Dei intrabunt!
Yesu kuwa, da ya ga ransa ya baci, sai ya ce, “Yana da wuya masu dukiya su shiga mulkin Allah!
25 facilius est enim camelum per foramen acus transire quam divitem intrare in regnum Dei.
Zai zama da sauki rakumi ya shiga kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”
26 Et dixerunt qui audiebant: Et quis potest salvus fieri?
Wadanda suka ji wannan magana suka ce, “Idan hakane wa zai sami ceto kenan?”
27 Ait illis: Quæ impossibilia sunt apud homines, possibilia sunt apud Deum.
Yesu ya amsa, “Abin da ya fi karfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah.”
28 Ait autem Petrus: Ecce nos dimisimus omnia et secuti sumus te.
Sai Bitrus ya ce, “To, ga shi mun bar mallakarmu, mun bi ka.”
29 Qui dixit eis: Amen dico vobis, nemo est qui reliquit domum, aut parentes, aut fratres, aut uxorem, aut filios propter regnum Dei,
Yesu ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko 'yan'uwansa, ko iyayensa, ko kuma 'ya'yansa, saboda mulkin Allah,
30 et non recipiat multo plura in hoc tempore, et in sæculo venturo vitam æternam. (aiōn , aiōnios )
sa'annan ya kasa samun ninkin ba ninkin a duniyan nan, da rai na har abada a duniya mai zuwa.” (aiōn , aiōnios )
31 Assumpsit autem Jesus duodecim, et ait illis: Ecce ascendimus Jerosolymam, et consummabuntur omnia quæ scripta sunt per prophetas de Filio hominis:
Bayan da ya tara su goma sha biyun nan, ya ce masu, “Ga shi, muna tafiya zuwa Urushalima, duk abubuwan da aka rubuta game da Dan Mutum ta hannun annabawa zasu tabbata.
32 tradetur enim gentibus, et illudetur, et flagellabitur, et conspuetur:
Gama za a bashe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa miyau.
33 et postquam flagellaverint, occident eum, et tertia die resurget.
Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma zai tashi.”
34 Et ipsi nihil horum intellexerunt, et erat verbum istud absconditum ab eis, et non intelligebant quæ dicebantur.
Amma ba su fahimci ko daya daga cikin wadannan abubuwa ba, domin zancen nan a boye yake daga garesu, ba su ma gane abin da aka fada ba.
35 Factum est autem, cum appropinquaret Jericho, cæcus quidam sedebat secus viam, mendicans.
Da ya kusato Yariko, ga wani makaho zaune a gefen hanya, yana bara,
36 Et cum audiret turbam prætereuntem, interrogabat quid hoc esset.
da ya ji taro na wucewa, sai ya tambaya ko menene.
37 Dixerunt autem ei quod Jesus Nazarenus transiret.
Suka ce masa Yesu Banazarat ne yake wucewa.
38 Et clamavit, dicens: Jesu, fili David, miserere mei.
Sai makahon ya ta da murya mai karfi, ya ce, “Yesu, Dan Dauda, ka yi mani jinkai.”
39 Et qui præibant, increpabant eum ut taceret. Ipse vero multo magis clamabat: Fili David, miserere mei.
Sai wadanda suke gaba suka kwabe shi, suna gaya masa ya yi shiru. Amma ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, “Dan Dauda, ka yi mani jinkai.”
40 Stans autem Jesus jussit illum adduci ad se. Et cum appropinquasset, interrogavit illum,
Sai Yesu ya tsaya, ya umarta a kawo shi wurinsa. Da makahon ya zo kusa, sai Yesu ya tambaye shi,
41 dicens: Quid tibi vis faciam? At ille dixit: Domine, ut videam.
“Me kake so in yi maka?” Ya ce, “Ubangiji, ina so in samu gani.”
42 Et Jesus dixit illi: Respice, fides tua te salvum fecit.
Yesu ya ce masa, “Karbi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai.”
43 Et confestim vidit, et sequebatur illum magnificans Deum. Et omnis plebs ut vidit, dedit laudem Deo.
Nan take ya samu gani, ya bi Yesu, yana daukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.