< Jeremiæ 10 >
1 Audite verbum quod locutus est Dominus super vos, domus Israël.
Ku ji abin da Ubangiji yana ce muku, ya gidan Isra’ila.
2 Hæc dicit Dominus: Juxta vias gentium nolite discere, et a signis cæli nolite metuere, quæ timent gentes,
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada ku koyi hanyoyin al’ummai ko ku razana game da alamun sararin sama, ko da yake al’ummai sun razana saboda su.
3 quia leges populorum vanæ sunt. Quia lignum de saltu præcidit opus manus artificis in ascia:
Gama al’adun mutane banza ne; sukan yanke itace daga kurmi, sai mai sassaƙa yă sassaƙa shi da gizago.
4 argento et auro decoravit illud: clavis et malleis compegit, ut non dissolvatur:
Sukan yi masa ado da azurfa da kuma zinariya; sukan ɗauki guduma su kafa shi da ƙusoshi, don kada yă fāɗi.
5 in similitudinem palmæ fabricata sunt, et non loquentur: portata tollentur, quia incedere non valent. Nolite ergo timere ea, quia nec male possunt facere, nec bene.
Kamar dodon gona cikin gonar kabewa, haka gumakansu ba sa iya magana; dole a yi ta ɗaukansu domin ba za su iya tafiya ba. Kada ku ji tsoronsu; ba za su iya yi wa wani lahani ba ba sa iya yin wani abin kirki.”
6 Non est similis tui, Domine: magnus es tu, et magnum nomen tuum in fortitudine.
Babu wani kamar ka, ya Ubangiji; kai mai girma ne, kuma sunanka yana da girma da kuma iko.
7 Quis non timebit te, o Rex gentium? tuum est enim decus: inter cunctos sapientes gentium, et in universis regnis eorum, nullus est similis tui.
Wane ne ba zai girmama ka ba, Ya Sarkin al’ummai? Tsoronka wajibi ne. A cikin dukan masu hikima na al’ummai kuma cikin dukan mulkokinsu, babu kamar ka.
8 Pariter insipientes et fatui probabuntur: doctrina vanitatis eorum lignum est.
Dukansu marasa azanci ne wawaye; gumakan itacen banza ne suke koya musu.
9 Argentum involutum de Tharsis affertur, et aurum de Ophaz: opus artificis et manus ærarii. Hyacinthus et purpura indumentum eorum: opus artificum universa hæc.
An kawo ƙeraren azurfa daga Tarshish zinariya kuma daga Ufaz. Abin da gwani da maƙerin zinariya suka yi sa’an nan aka yi masa ado da mulufi da shunayya dukan aikin gwanaye.
10 Dominus autem Deus verus est, ipse Deus vivens, et rex sempiternus. Ab indignatione ejus commovebitur terra, et non sustinebunt gentes comminationem ejus.
Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya; shi ne Allah mai rai, madawwamin sarki. Sa’ad da ya yi fushi, ƙasa takan girgiza; al’ummai ba sa iya jure da hasalarsa.
11 Sic ergo dicetis eis: Dii qui cælos et terram non fecerunt, pereant de terra et de his quæ sub cælo sunt!
“Ka faɗa musu wannan, ‘Waɗannan alloli, waɗanda ba su yi sammai da ƙasa ba, za su hallaka daga duniya da kuma daga ƙarƙashin sammai.’”
12 Qui facit terram in fortitudine sua, præparat orbem in sapientia sua, et prudentia sua extendit cælos:
Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.
13 ad vocem suam dat multitudinem aquarum in cælo, et elevat nebulas ab extremitatibus terræ: fulgura in pluviam facit, et educit ventum de thesauris suis.
Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi; yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya. Yakan aiki walƙiya da ruwan sama ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa.
14 Stultus factus est omnis homo a scientia: confusus est artifex omnis in sculptili, quoniam falsum est quod conflavit, et non est spiritus in eis.
Kowa marar azanci ne, marar ilimi; kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa. Siffofinsa ƙarya ne; ba su da numfashi a cikinsu.
15 Vana sunt, et opus risu dignum: in tempore visitationis suæ peribunt.
Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne; Sa’ad da hukuncinsu ya yi za su lalace.
16 Non est his similis pars Jacob: qui enim formavit omnia, ipse est, et Israël virga hæreditatis ejus: Dominus exercituum nomen illi.
Shi da yake Rabon Yaƙub ba kamar waɗannan yake ba, gama shi ne Mahaliccin abubuwa duka, har da Isra’ila, kabilar gādonsa Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
17 Congrega de terra confusionem tuam, quæ habitas in obsidione:
Ku tattara kayayyakinku don ku bar ƙasar, ku da kuke zaune a wurin da aka kewaye da yaƙi.
18 quia hæc dicit Dominus: Ecce ego longe projiciam habitatores terræ in hac vice, et tribulabo eos ita ut inveniantur.
Gama haka Ubangiji ya faɗa, “A wannan lokaci zan jefar da waɗanda suke zaune a ƙasar; zan kawo damuwa a kansu domin a kama su.”
19 Væ mihi super contritione mea: pessima plaga mea. Ego autem dixi: Plane hæc infirmitas mea est, et portabo illam.
Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka yi mini! Raunina ba mai warkewa ba ne! Duk da haka na ce wa kaina, “Wannan ciwona ne, dole kuma in jure da shi.”
20 Tabernaculum meum vastatum est; omnes funiculi mei dirupti sunt: filii mei exierunt a me, et non subsistunt. Non est qui extendat ultra tentorium meum, et erigat pelles meas.
An lalatar da tentina; dukan igiyoyinsa sun tsintsinke.’Ya’yana maza sun bar ni ba sa nan; ba wanda aka bari da zai kafa tentina ko ya kafa mini mafaka.
21 Quia stulte egerunt pastores, et Dominum non quæsierunt: propterea non intellexerunt, et omnis grex eorum dispersus est.
Makiyaya marasa azanci ne kuma ba sa neman nufin Ubangiji; saboda haka ba sa nasara dukan garkensu kuwa ya watse.
22 Vox auditionis ecce venit, et commotio magna de terra aquilonis: ut ponat civitates Juda solitudinem, et habitaculum draconum.
Ku saurara! Rahoto yana zuwa babban hargitsi daga ƙasar arewa! Zai mai da garuruwan Yahuda kufai, mazaunin diloli.
23 Scio, Domine, quia non est hominis via ejus, nec viri est ut ambulet, et dirigat gressus suos.
Na sani, ya Ubangiji, cewa ran mutum ba nasa ba ne; ba mutum ne yake kiyaye takawarsa ba.
24 Corripe me, Domine, verumtamen in judicio, et non in furore tuo, ne forte ad nihilum redigas me.
Ka yi mini gyara, Ubangiji, amma fa da adalci kaɗai ba cikin fushinka ba, don kada ka wofinta ni.
25 Effunde indignationem tuam super gentes quæ non cognoverunt te, et super provincias quæ nomen tuum non invocaverunt: quia comederunt Jacob, et devoraverunt eum, et consumpserunt illum, et decus ejus dissipaverunt.
Ka zuba hasalarka a kan al’umman da ba su san ka ba, a kan mutanen da ba sa kira bisa sunanka. Gama sun cinye Yaƙub; sun cinye shi gaba ɗaya suka kuma lalace wurin zamansa.