< Isaiæ 17 >

1 Onus Damasci. Ecce Damascus desinet esse civitas, et erit sicut acervus lapidum in ruina.
Abin da Allah ya faɗa game da Damaskus. “Duba, Damaskus ba za tă ƙara zama birni ba amma za tă zama tsibin juji.
2 Derelictæ civitates Aroër gregibus erunt, et requiescent ibi, et non erit qui exterreat.
Za a watse a bar biranen Arower a bar wa tumaki da shanu, waɗanda za su kwanta, ba tare da wani wanda zai tsorata su ba.
3 Et cessabit adjutorium ab Ephraim, et regnum a Damasco; et reliquiæ Syriæ sicut gloria filiorum Israël erunt, dicit Dominus exercituum.
Birni mai katanga za tă ɓace daga Efraim, ikon sarauta kuma daga Damaskus; raguwar Aram za tă zama kamar darajar Isra’ila,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
4 Et erit in die illa: attenuabitur gloria Jacob, et pinguedo carnis ejus marcescet.
“A wannan rana ɗaukakar Yaƙub za tă ƙare; kitsen jikinsa zai lalace.
5 Et erit sicut congregans in messe quod restiterit, et brachium ejus spicas leget; et erit sicut quærens spicas in valle Raphaim.
Zai zama kamar sa’ad da mai girbi ya tara hatsin da yake tsaye ya kuma girbe hatsin da hannunsa kamar sa’ad da mutum ya yi kala kawunan hatsi a Kwarin Refayim.
6 Et relinquetur in eo sicut racemus et sicut excussio oleæ duarum vel trium olivarum in summitate rami, sive quatuor aut quinque in cacuminibus ejus fructus ejus, dicit Dominus Deus Israël.
Duk da haka waɗansu kala za su ragu, sai ka ce sa’ad da an karkaɗe itace zaitun, aka bar’ya’yan zaitun biyu ko uku a can ƙwanƙolin rassan, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassa na gefe na itace mai’ya’ya,” in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila.
7 In die illa inclinabitur homo ad factorem suum, et oculi ejus ad Sanctum Israël respicient;
A wannan rana mutane za su nemi Mahaliccinsu su kuma juye idanunsu ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
8 et non inclinabitur ad altaria quæ fecerunt manus ejus; et quæ operati sunt digiti ejus non respiciet lucos et delubra.
Ba za su dubi bagade ba, waɗanda suke aikin hannuwansu, ba za su kuma kula da ginshiƙan Ashera ba da kuma bagadan turaren da yatsotsinsu suka yi.
9 In die illa erunt civitates fortitudinis ejus derelictæ sicut aratra, et segetes quæ derelictæ sunt a facie filiorum Israël; et eris deserta.
A wannan rana biranensu masu ƙarfi, waɗanda suka bari saboda Isra’ilawa, za su zama kamar wuraren da aka ƙyale suka zama kufai a jeji. Za su kuma zama kango.
10 Quia oblitus es Dei salvatoris tui, et fortis adjutoris tui non es recordata: propterea plantabis plantationem fidelem, et germen alienum seminabis;
Kun manta da Allah Mai Cetonku; ba ku tuna da Dutse, kagararku ba. Saboda haka, ko da yake kun fita ku shuka tsire-tsire mafi kyau kuka kuma shuka inabin da aka sayo daga waje,
11 in die plantationis tuæ labrusca, et mane semen tuum florebit; ablata est messis in die hæreditatis, et dolebit graviter.
ko da yake a ranar kun shuka su, kuka sa su yi girma, da safe kuma sa’ad da kuka shuka su, kuka sa suka yi toho suka yi fure, duk da haka girbin ba zai zama kome ba a ranar cuta da zafin da ba ta da magani.
12 Væ multitudini populorum multorum, ut multitudo maris sonantis; et tumultus turbarum, sicut sonitus aquarum multarum.
Kash, ga hayaniyar al’ummai masu yawa suna hayaniya kamar rurin teku! Kash, ga fushin mutane suna ruri kamar rugugi kamar manyan ruwaye!
13 Sonabunt populi sicut sonitus aquarum inundantium, et increpabit eum, et fugiet procul; et rapietur sicut pulvis montium a facie venti, et sicut turbo coram tempestate.
Ko da yake mutane suna ruri kamar sukuwar raƙuman ruwa, sa’ad da ya tsawata musu za su gudu can da nisa, aka kore su kamar yayinda iska ya hura a kan tuddai, kamar tattake kuma a cikin guguwa.
14 In tempore vespere, et ecce turbatio; in matutino, et non subsistet. Hæc est pars eorum qui vastaverunt nos, et sors diripientium nos.
Da yamma, sai razana ba tsammani! Kafin safiya, duk sun ɓace! Wannan ne rabon waɗanda suka washe mu, rabon waɗanda suka yi mana ƙwace.

< Isaiæ 17 >