< Hebræos 8 >
1 Capitulum autem super ea quæ dicuntur: Talem habemus pontificem, qui consedit in dextera sedis magnitudinis in cælis,
Yanzu abin da muke kokarin cewa shine: Muna da babban firist wanda ke zaune a hannun dama na kursiyi mai martaba dake sammai.
2 sanctorum minister, et tabernaculi veri, quod fixit Dominus, et non homo.
Shi kuwa bawa ne a wannan wuri mai tsarki, haikali na gaskiya wanda Allah ya shirya ba wani bil'adama ba.
3 Omnis enim pontifex ad offerendum munera, et hostias constituitur: unde necesse est et hunc habere aliquid, quod offerat.
Kowanne babban firist kuwa yana mika bayebaye da hadayu. Don haka ya kamata a sami abin hadaya.
4 Si ergo esset super terram, nec esset sacerdos: cum essent qui offerent secundum legem munera,
Da a ce Almasihu yana duniya ba zai zama firist ba ko kadan.
5 qui exemplari, et umbræ deserviunt cælestium. Sicut responsum est Moysi, cum consummaret tabernaculum: Vide (inquit) omnia facito secundum exemplar, quod tibi ostensum est in monte.
Domin a kwai masu mika hadaya bisa ga shari'a. Suna hidimar misalin abubuwan da suke inuwar sama. Kamar yadda Allah ya yi wa Musa gargadi yayin da ya ke shirin gina Alfarwa: ''Duba'' Allah ya ce, ''kayi komai bisa ga salon da aka koya maka a bisa dutse.”
6 Nunc autem melius sortitus est ministerium, quanto et melioris testamenti mediator est, quod in melioribus repromissionibus sancitum est.
Amma yanzu hidimar da Almasihu ya karba ta dara tasu dukka, domin kuwa shine matsakancin muhimmin alkawari, wanda aka kammala a kan muhimman alkawura.
7 Nam si illud prius culpa vacasset, non utique secundi locus inquireretur.
Domin kuwa idan alkawarin fari ba shi da laifi babu anfanin neman alkawari na biyu.
8 Vituperans enim eos dicit: Ecce dies venient, dicit Dominus: et consummabo super domum Israël, et super domum Juda, testamentum novum,
Da Allah ya sami laifi akan mutane, sai ya ce ''Zan sake sabon alkawari da gidan Isra'ila da kuma gidan Yahuza.
9 non secundum testamentum quod feci patribus eorum in die qua apprehendi manum eorum ut educerem illos de terra Ægypti: quoniam ipsi non permanserunt in testamento meo: et ego neglexi eos, dicit Dominus.
kuma ba zai zama kamar yadda nayi da kakanninku ba, kamar yadda na rike su a hannu har Na fidda su daga kasar Masar. Basu kuma ci gaba da Alkawarina ba, ni kuwa na yi watsi da su,'' inji Ubangiji.
10 Quia hoc est testamentum quod disponam domui Israël post dies illos, dicit Dominus: dando leges meas in mentem eorum, et in corde eorum superscribam eas: et ero eis in Deum, et ipsi erunt mihi in populum:
Gama wanna shine alkawarin da zan yi da gidan Isra'ila bayan wadannan kwanaki, Inji Ubangiji. Zan sa shari'a ta a bakinsu in kuma rubuta ta a zuciyarsu, Zan kuma zama Allah a garesu, su kuma su zama jama'ata.
11 et non docebit unusquisque proximum suum, et unusquisque fratrem suum, dicens: Cognosce Dominum: quoniam omnes scient me a minore usque ad majorem eorum:
Ba za su kuma koyar da makwabta ko yan'uwansu cewa, ''ku san Ubangiji'' gama dukkanin su za su san ni, daga karami har zuwa babba.
12 quia propitius ero iniquitatibus eorum, et peccatorum eorum jam non memorabor.
Zan kuma nuna tausayi ga ayyukan su na rashin adalci, ba kuma zan kara tunawa da zunubansu ba.
13 Dicendo autem novum: veteravit prius. Quod autem antiquatur, et senescit, prope interitum est.
A kan fadin ''sabo'' ya mayar da alkawarin fari tsoho. Wannan kuma da aka ambata tsoho na shirin bacewa.