< Genesis 36 >

1 Hæ sunt autem generationes Esau, ipse est Edom.
Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom).
2 Esau accepit uxores de filiabus Chanaan: Ada filiam Elon Hethæi, et Oolibama filiam Anæ filiæ Sebeon Hevæi:
Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye
3 Basemath quoque filiam Ismaël sororem Nabaioth.
ya kuma auri Basemat’yar Ishmayel wadda take’yar’uwar Nebayiwot.
4 Peperit autem Ada Eliphaz: Basemath genuit Rahuel:
Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel.
5 Oolibama genuit Jehus et Ihelon et Core. Hi filii Esau qui nati sunt ei in terra Chanaan.
Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana.
6 Tulit autem Esau uxores suas et filios et filias, et omnem animam domus suæ, et substantiam, et pecora, et cuncta quæ habere poterat in terra Chanaan: et abiit in alteram regionem, recessitque a fratre suo Jacob.
Isuwa ya ɗauki matansa da’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub.
7 Divites enim erant valde, et simul habitare non poterant: nec sustinebat eos terra peregrinationis eorum præ multitudine gregum.
Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu.
8 Habitavitque Esau in monte Seir, ipse est Edom.
Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.
9 Hæ autem sunt generationes Esau patris Edom in monte Seir,
Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom, a ƙasar tuddai na Seyir.
10 et hæc nomina filiorum ejus: Eliphaz filius Ada uxoris Esau: Rahuel quoque filius Basemath uxoris ejus.
Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Isuwa maza, Elifaz, ɗan Ada matar Isuwa, da Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.
11 Fueruntque Eliphaz filii: Theman, Omar, Sepho, et Gatham, et Cenez.
’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz.
12 Erat autem Thamna concubina Eliphaz filii Esau: quæ peperit ei Amalech. Hi sunt filii Ada uxoris Esau.
Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa.
13 Filii autem Rahuel: Nahath et Zara, Samma et Meza: hi filii Basemath uxoris Esau.
’Ya’yan Reyuwel maza su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
14 Isti quoque erant filii Oolibama filiæ Anæ filiæ Sebeon, uxoris Esau, quos genuit ei, Jehus et Ihelon et Core.
’Ya’yan Oholibama maza’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon, matar Isuwa, waɗanda ta haifa wa Isuwa su ne, Yewush, Yalam da Kora.
15 Hi duces filiorum Esau: filii Eliphaz primogeniti Esau: dux Theman, dux Omra, dux Sepho, dux Cenez,
Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa,’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa, Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz,
16 dux Core, dux Gathan, dux Amalech. Hi filii Eliphaz in terra Edom, et hi filii Ada.
Kora, Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada.
17 Hi quoque filii Rahuel filii Esau: dux Nahath, dux Zara, dux Samma, dux Meza: hi autem duces Rahuel in terra Edom: isti filii Basemath uxoris Esau.
’Ya’yan Reyuwel maza, Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
18 Hi autem filii Oolibama uxoris Esau: dux Jehus, dux Ihelon, dux Core: hi duces Oolibama filiæ Anæ uxoris Esau.
’Ya’yan Oholibama maza matar Isuwa, Shugabannin su ne; Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Oholibama’yar Ana matar Isuwa.
19 Isti sunt filii Esau, et hi duces eorum: ipse est Edom.
Waɗannan su ne’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu.
20 Isti sunt filii Seir Horræi, habitatores terræ: Lotan, et Sobal, et Sebeon, et Ana,
Waɗannan su ne’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,
21 et Dison, et Eser, et Disan: hi duces Horræi, filii Seir in terra Edom.
Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa,’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.
22 Facti sunt autem filii Lotan: Hori et Heman. Erat autem soror Lotan, Thamna.
’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna’yar’uwar Lotan ce.
23 Et isti filii Sobal: Alvan et Manahat et Ebal, et Sepho et Onam.
’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.
24 Et hi filii Sebeon: Aja et Ana. Iste est Ana qui invenit aquas calidas in solitudine, cum pasceret asinos Sebeon patris sui:
’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon.
25 habuitque filium Dison, et filiam Oolibama.
’Ya’yan Ana su ne, Dishon da Oholibama’yar Ana.
26 Et isti filii Dison: Hamdan, et Eseban, et Jethram, et Charan.
’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
27 Hi quoque filii Eser: Balaan, et Zavan, et Acan.
’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Akan.
28 Habuit autem filios Disan: Hus et Aram.
’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.
29 Hi duces Horræorum: dux Lotan, dux Sobal, dux Sebeon, dux Ana,
Waɗannan su ne manyan Horiyawa, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,
30 dux Dison, dux Eser, dux Disan: isti duces Horræorum qui imperaverunt in terra Seir.
Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir.
31 Reges autem qui regnaverunt in terra Edom antequam haberent regem filii Israël, fuerunt hi:
Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki,
32 Bela filius Beor, nomenque urbis ejus Denaba.
Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.
33 Mortuus est autem Bela, et regnavit pro eo Jobab filius Zaræ de Bosra.
Sa’ad da Bela ya rasu, Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi.
34 Cumque mortuus esset Jobab, regnavit pro eo Husam de terra Themanorum.
Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.
35 Hoc quoque mortuo, regnavit pro eo Adad filius Badad, qui percussit Madian in regione Moab: et nomen urbis ejus Avith.
Sa’ad da Husham ya rasu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a ƙasar Mowab, ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Awit.
36 Cumque mortuus esset Adad, regnavit pro eo Semla de Masreca.
Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi.
37 Hoc quoque mortuo regnavit pro eo Saul de fluvio Rohoboth.
Sa’ad da Samla ya rasu, Sha’ul daga Rehobot na ta kogi ya gāje shi.
38 Cumque et hic obiisset, successit in regnum Balanan filius Achobor.
Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi.
39 Isto quoque mortuo regnavit pro eo Adar, nomenque urbis ejus Phau: et appellabatur uxor ejus Meetabel, filia Matred filiæ Mezaab.
Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce’yar Matired, jikanyar Me-Zahab.
40 Hæc ergo nomina ducum Esau in cognationibus, et locis, et vocabulis suis: dux Thamna, dux Alva, dux Jetheth,
Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne, Timna, Alwa, Yetet.
41 dux Oolibama, dux Ela, dux Phinon,
Oholibama, Ela, Finon.
42 dux Cenez, dux Theman, dux Mabsar,
Kenaz, Teman, Mibzar.
43 dux Magdiel, dux Hiram: hi duces Edom habitantes in terra imperii sui, ipse est Esau pater Idumæorum.
Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna. Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom.

< Genesis 36 >