< Apocalypsis 13 >
1 Et stetit supra arenam maris. Et vidi de mari bestiam ascendentem, habentem capita septem, et cornua decem, et super cornua eius decem diademata, et super capita eius nomina blasphemiæ.
Sai diragon ya tsaya a kan yashi, a gaban teku. Sai na ga wani dabba yana fitowa daga teku. Yana da kahonni goma da kawuna bakwai. A kan kahonninsa akwai kambi goma, a kan kowanne kansa akwai suna na sabo.
2 Et bestia, quam vidi, similis erat pardo, et pedes eius sicut pedes ursi, et os eius sicut os leonis. Et dedit illi draco virtutem suam, et potestatem magnam.
Wannan dabban da na gani yana kama da damisa, kafafunsa kuma kamar na beyar, bakinsa kuma kamar na zaki. Wannan diragon ya ba shi karfinsa, da kursiyinsa da ikonsa mai girma na sarauta.
3 Et vidi unum de capitibus suis quasi occisum in mortem: et plaga mortis eius curata est. Et admirata est universa terra post bestiam.
Daya daga cikin kawunan dabban ya yi kamar an kashe shi, amma rauninsa mai tsanani ya warke. Sai dukan duniya ta yi mamaki a yayin da suke bin dabban.
4 Et adoraverunt draconem, qui dedit potestatem bestiæ: et adoraverunt bestiam, dicentes: Quis similis bestiæ? et quis poterit pugnare cum ea?
Su ma suka yi wa diragon sujada, domin ya ba dabban ikonsa. Suka yi wa dabban sujada suna ta cewa, “Wanene kamar dabban? Wa kuma zai iya yin fada da shi?”
5 Et datum est ei os loquens magna, et blasphemias: et data est ei potestas facere menses quadraginta duos.
Aka ba dabban baki da zai iya fadin kalmomin fahariya da sabo. Ya sami izini na zartar da iko har wata arba'in da biyu.
6 Et aperuit os suum in blasphemias ad Deum, blasphemare nomen eius, et tabernaculum eius, et eos, qui in cælo habitant.
Sai dabban ya bude bakinsa yana maganganun sabo ga Allah: yana sabon sunansa, da mazauninsa, da kuma wadanda ke zaune a sama.
7 Et est datum illi bellum facere cum sanctis, et vincere eos. Et data est illi potestas in omnem tribum, et populum, et linguam, et gentem,
Aka yarje wa dabbar ya yi yaki da masu bi ya kuma yi nasara da su. An kuma ba shi iko bisa kowacce kabila, da jama'a, da harshe, da al'umma.
8 et adoraverunt eam omnes, qui inhabitant terram: quorum non sunt scripta nomina in Libro vitæ Agni, qui occisus est ab origine mundi.
Dukan wadanda ke zaune a duniya za su yi masa sujada, dukan wadanda tun hallitar duniya ba a rubuta sunayensu a littafin rai na Dan Rago ba, wanda aka yanka.
9 Si quis habet aurem, audiat.
Idan wani yana da kunne, bari ya ji. Duk wanda za a dauke shi zuwa bauta, ga bauta zai tafi.
10 Qui in captivitatem duxerit, in captivitatem vadet: qui in gladio occiderit, oportet eum gladio occidi. Hic est patientia, et fides Sanctorum.
Duk wanda za a kashe da takobi, da takobi za a kashe shi. Wannan kira ne na dauriya, hakuri da bangaskiya ga wadanda suke da tsarki.
11 Et vidi aliam bestiam ascendentem de terra, et habebat cornua duo similia Agni, et loquebatur sicut draco.
Sai na ga wani dabban na fitowa daga cikin kasa. Yana da kahonni biyu kamar na dan rago, ya kuma yi magana kamar maciji.
12 Et potestatem prioris bestiæ omnem faciebat in conspectu eius: et fecit terram, et habitantes in ea, adorare bestiam primam, cuius curata est plaga mortis.
Ya zartar da dukan ikon dabban na farko a gabansa, ya kuma sa duniya da duk mazaunanta su yi wa dabban nan na farko sujada, wanda aka warkar masa da rauni mai kamar na ajali.
13 Et fecit signa magna, ut etiam ignem faceret de cælo descendere in terram in conspectu hominum.
Ya yi manyan al'ajibai. Har ya sa wuta ta sauko kasa daga sama a gaban mutane.
14 Et seduxit habitantes in terra propter signa, quæ data sunt illi facere in conspectu bestiæ, dicens habitantibus in terra, ut faciant imaginem bestiæ, quæ habet plagam gladii, et vixit.
Ta wurin alamu da aka yarje masa ya yi, ya yaudari mazaunan duniya. Ya ce masu su yi wata siffa don girmama dabban da yake da raunin takobi, amma duk da haka ya rayu.
15 Et datum est illi ut daret spiritum imagini bestiæ, et ut loquatur imago bestiæ: et faciat ut quicumque non adoraverint imaginem bestiæ, occidantur.
Aka yarje masa ya ba da numfashi ga siffar dabban domin siffar ta yi magana, ta kuma sa a kashe duk wadanda suka ki yin sujada ga dabban.
16 Et faciet omnes pusillos, et magnos, et divites, et pauperes, et liberos, et servos habere characterem in dextera manu sua, aut in frontibus suis.
Ya kuma tilasta kowa, kanana da manya, mawadata da matalauta, masu yanci da bayi, su karbi alama a hannun dama ko kuma a goshi.
17 et nequis possit emere, aut vendere, nisi qui habet characterem, aut nomen bestiæ, aut numerum nominis eius.
Ba shi yiwuwa wani ya saya ko ya sayar sai dai yana da alamar dabban, wato lambar nan da ke wakiltar sunansa.
18 Hic sapientia est. Qui habet intellectum, computet numerum bestiæ. Numerus enim hominis est: et numerus eius sexcenti sexaginta sex.
Wannan na bukatar hikima. Idan wani yana da hikima, sai ya kididdige lambar dabban nan. Gama lambar ta mutum ce. Lambarta itace 666.