< Isaiæ 55 >
1 Omnes sitientes venite ad aquas: et qui non habetis argentum, properate, emite, et comedite: venite, emite absque argento, et absque ulla commutatione vinum et lac.
“Ku zo, dukanku masu jin ƙishi, ku zo wurin ruwaye; ku kuma da ba ku da kuɗi, ku zo, ku saya ku kuma ci! Ku zo, ku saya ruwan inabi da madara ba tare da kuɗi ba ba za ku kuma biya kome ba.
2 Quare appenditis argentum non in panibus, et laborem vestrum non in saturitate? Audite audientes me, et comedite bonum, et delectabitur in crassitudine anima vestra.
Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba, ku kuma yi wahala a kan abin da ba za ku ƙoshi ba? Ku saurara, ku saurare ni, ku kuma ci abin da yake da kyau, ranku kuma zai ji daɗin abinci mafi kyau.
3 Inclinate aurem vestram, et venite ad me: audite, et vivet anima vestra, et feriam vobiscum pactum sempiternum, misericordias David fideles.
Ku kasa kunne ku kuma zo gare ni; ku saurare ni, don ranku ya rayu. Zan yi madawwamin alkawari da ku, zan nuna muku ƙaunata marar ƙarewa da na yi wa Dawuda alkawari.
4 Ecce testem populis dedi eum, ducem ac præceptorem Gentibus.
Duba, na mai da shi shaida ga mutane, shugaba da kuma jagorar mutane.
5 Ecce gentem, quam nesciebas, vocabis: et Gentes, quæ te non cognoverunt, ad te current propter Dominum Deum tuum, et sanctum Israel, quia glorificavit te.
Tabbatacce za ku kira al’umman da ba ku sani ba, kuma al’umman da ba ku sani ba za su sheƙo a guje zuwa wurinku, saboda Ubangiji Allahnku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, gama ya darjanta ku.”
6 Quærite Dominum, dum inveniri potest: invocate eum, dum prope est.
Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa; ku yi kira gare shi tun yana kusa.
7 Derelinquat impius viam suam, et vir iniquus cogitationes suas, et revertatur ad Dominum, et miserebitur eius, et ad Deum nostrum: quoniam multus est ad ignoscendum.
Bari mugu ya bar irin halinsa mugu kuma ya sāke irin tunaninsa. Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa, ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.
8 Non enim cogitationes meæ, cogitationes vestræ: neque viæ vestræ, viæ meæ, dicit Dominus.
“Gama tunanina ba tunaninku ba ne, yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,” in ji Ubangiji.
9 Quia sicut exaltantur cæli a terra, sic exaltatæ sunt viæ meæ a viis vestris, et cogitationes meæ a cogitationibus vestris.
“Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa, haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa tunanina kuma dabam da naku.
10 Et quomodo descendit imber, et nix de cælo, et illuc ultra non revertitur, sed inebriat terram, et infundit eam, et germinare eam facit, et dat semen serenti, et panem comedenti:
Kamar yadda ruwan sama da dusar ƙanƙara suke saukowa daga sama, ba sa komowa ba tare da sun jiƙe duniya sun kuma sa su yi’ya’ya su kuma yi toho, don su ba da iri ga mai shuki da kuma abinci ga mai ci,
11 Sic erit verbum meum, quod egredietur de ore meo: non revertetur ad me vacuum, sed faciet quæcumque volui, et prosperabitur in his, ad quæ misi illud.
haka maganata da take fitowa daga bakina. Ba za tă koma gare ni wofi ba, amma za tă cika abin da nake so ta kuma cika abin da na aike ta tă yi.
12 Quia in lætitia egrediemini, et in pace deducemini: montes et colles cantabunt coram vobis laudem, et omnia ligna regionis plaudent manu.
Za ku fita da farin ciki a kuma bi da ku da salama; duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa a gabanku, dukan itatuwan jeji kuma za su tafa hannuwansu.
13 Pro saliunca ascendet abies, et pro urtica crescet myrtus: et erit Dominus nominatus in signum æternum, quod non auferetur.
A maimakon sarƙaƙƙiya, itacen fir ne zai tsiro, a maimakon ƙayayyuwa kuma, itacen ci-zaƙi ne zai tsiro. Wannan zai zama matuni na abin da Ni Ubangiji na yi, madawwamiyar alama ce, wadda ba za a datse ba.”