< Ii Paralipomenon 31 >
1 Cumque hæc fuissent rite celebrata, egressus est omnis Israel, qui inventus fuerat in urbibus Iuda, et fregerunt simulacra, succideruntque lucos, demoliti sunt excelsa, et altaria destruxerunt, non solum de universo Iuda et Beniamin, sed et de Ephraim quoque et Manasse, donec penitus everterent: reversique sunt omnes filii Israel in possessiones et civitates suas.
Sa’ad da aka gama dukan wannan, sai Isra’ilawan da suke can suka fita zuwa garuruwan Yahuda, suka rurrushe keɓaɓɓun duwatsu suka kuma farfashe ginshiƙan Ashera. Suka rurrushe masujadan kan tudu da bagadai, ko’ina a Yahuda da Benyamin da kuma cikin Efraim da Manasse. Bayan sun rurrushe dukansu, sai Isra’ilawa suka koma garuruwansu, kowanne zuwa mahallinsa.
2 Ezechias autem constituit turmas Sacerdotales, et Leviticas per divisiones suas, unumquemque in officio proprio, tam Sacerdotum videlicet quam Levitarum ad holocausta, et pacifica ut ministrarent et confiterentur, canerentque in portis castrorum Domini.
Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi-kashi, kowanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima, su yi godiya, su kuma rera yabai a ƙofofin mazaunin Ubangiji.
3 Pars autem regis erat, ut de propria eius substantia offerretur holocaustum, mane semper et vespere. Sabbatis quoque, et Calendis, et sollemnitatibus ceteris, sicut scriptum est in lege Moysi.
Sarki ya ba da taimako daga mallakarsa domin hadayun ƙonawa, safe da yamma da kuma don hadayun ƙonawa a Asabbatai, Sabon Wata da kuma ƙayyadaddun bukukkuwa kamar yadda yake a rubuce a cikin Dokar Ubangiji.
4 Præcepit etiam populo habitantium Ierusalem ut darent partes Sacerdotibus, et Levitis, ut possent vacare legi Domini.
Ya umarci mutanen da suke zama a Urushalima su ba da rabon da yake na firistoci da Lawiyawa, don su ƙwallafa ransu ga Dokar Ubangiji.
5 Quod cum percrebruisset in auribus multitudinis, plurimas obtulere primitias filii Israel frumenti, vini, et olei, mellis quoque: et omnium, quæ gignit humus, decimas obtulerunt.
Nan da nan aka baza umarnin, sai Isra’ilawa suka bayar’ya’yan farin hatsinsu, sabon ruwan inabi, mai da kuma zuma da dukan abin da gona ta bayar, hannu sake. Suka kawo zakan kowane abu da yawa.
6 Sed et filii Israel et Iuda, qui habitabant in urbibus Iuda, obtulerunt decimas boum et ovium, decimasque sanctorum, quæ voverant Domino Deo suo: atque universa portantes, fecerunt acervos plurimos.
Mutanen Isra’ila da Yahuda waɗanda suke zama a garuruwan Yahuda, su ma suka kawo zakan shanu da na tumaki da kuma zakan abubuwa masu tsarki da aka keɓe ga Ubangiji Allahnsu, suka jibge su tsibi-tsibi.
7 Mense tertio cœperunt acervorum iacere fundamenta, et mense septimo compleverunt eos.
Sun fara yin haka a wata na uku, suka kuma gama a wata na bakwai.
8 Cumque ingressi fuissent Ezechias, et principes eius, viderunt acervos, et benedixerunt Domino ac populo Israel.
Sa’ad da Hezekiya da fadawansa suka zo suka ga tsibin, sai suka yabi Ubangiji, suka kuma albarkace mutanensa Isra’ila.
9 Interrogavitque Ezechias Sacerdotes, et Levitas cur ita iacerent acervi.
Hezekiya ya tambayi firistoci da Lawiyawa game da tsibin;
10 Respondit illi Azarias Sacerdos primus de stirpe Sadoc, dicens: Ex quo cœperunt offerri primitiæ in domo Domini, comedimus, et saturati sumus, et remanserunt plurima, eo quod benedixerit Dominus populo suo: reliquarum autem copia est ista, quam cernis.
sai Azariya babban firist, daga iyalin Zadok ya amsa, “Tun daga lokacin da mutane suka fara kawo taimakonsu ga haikalin Ubangiji, muna da isashe don abinci da kuma da yawa da za mu rage, domin Ubangiji ya albarkaci mutanensa, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.”
11 Præcepit igitur Ezechias ut præpararent horrea in domo Domini. Quod cum fecissent,
Hezekiya ya ba da umarni a shirya ɗakunan ajiya a haikalin Ubangiji, aka kuwa yi haka.
12 intulerunt tam primitias, quam decimas, et quæcumque voverant, fideliter. Fuit autem præfectus eorum Chonenias Levita, et Semei frater eius, secundus,
Sa’an nan cikin aminci suka kawo taimako, zakka da keɓaɓɓun kyautai. Konaniya, wani Balawe, shi ne ke lura da waɗannan abubuwa, kuma ɗan’uwansa Shimeyi shi ne na biye da shi.
13 post quem Iahiel, et Azarias, et Nahath, et Asael, et Ierimoth, Iozabad quoque, et Eliel, et Iesmachias, et Mahath, et Banaias, præpositi sub manibus Choneniæ, et Semei fratris eius, ex imperio Ezechiæ regis et Azariæ pontificis domus Dei, ad quos omnia pertinebant.
Yehiyel, Azaziya, Nahat, Asahel, Yerimot, Yozabad, Eliyel, Ismakiya, Mahat da Benahiya su ne shugabanni, mataimakan Konaniya da Shimeyi ɗan’uwansa, waɗanda sarki Hezekiya da Azariya babban shugaban haikalin Allah suka naɗa.
14 Core vero filius Iemna Levites et ianitor Orientalis portæ, præpositus erat iis, quæ sponte offerebantur Domino, primitiisque et consecratis in Sancta sanctorum.
Kore ɗan Imna Balawe, mai tsaron Ƙofar Gabas, shi ne yake lura da baikon yardan ran da aka yi wa Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki.
15 Et sub cura eius Eden, et Beniamin, Iesue, et Semeias, Amarias quoque, et Sechenias in civitatibus Sacerdotum ut fideliter distribuerent fratribus suis partes, minoribus atque maioribus:
Eden, Miniyamin, Yeshuwa, Shemahiya, Amariya da Shekaniya sun taimake shi da aminci a cikin garuruwan firistoci, suna ba da rabo wa’yan’uwansu firistoci bisa ga sassansu, tsofaffi da yara.
16 exceptis maribus ab annis tribus et supra, cunctis qui ingrediebantur templum Domini, et quidquid per singulos dies conducebat in ministerio, atque observationibus iuxta divisiones suas,
Bugu da ƙari, suka ba da rabo ga maza’yan shekaru uku ko fiye waɗanda sunayensu suna a tarihin zuriya, dukan waɗanda ba za su iya shiga haikalin Ubangiji su yi ayyukansu na kullum ba, bisa ga nawayarsu da kuma sassansu.
17 Sacerdotibus per familias, et Levitis a vigesimo anno et supra, per ordines et turmas suas,
Suka kuma ba da rabo ga firistocin da aka rubuta ta iyalansu cikin tarihin zuriya, haka kuma ga Lawiyawa masu shekara ashirin ko fiye, bisa ga nawayarsu da kuma sassansu.
18 universæque multitudini tam uxoribus, quam liberis eorum utriusque sexus, fideliter cibi de his, quæ sanctificata fuerant, præbebantur.
Suka haɗa da dukan ƙanana’ya’yansu, mata, da kuma’ya’ya maza da’ya’ya mata, al’umma gaba ɗaya da aka jera a waɗannan tarihin zuriya. Gama sun yi aminci cikin tsarkake kansu.
19 Sed et filiorum Aaron per agros, et suburbana urbium singularum dispositi erant viri, qui partes distribuerent universo sexui masculino de Sacerdotibus, et Levitis.
Akwai mutane a garuruwa da yawa waɗanda aka sa don su rarraba wa’ya’yan Haruna, firist, maza, waɗanda suke zaune a gonaki na ƙasar garuruwansu su ba kowane namijin da aka rubuta na Lawiyawa, rabonsa.
20 Fecit ergo Ezechias universa quæ diximus in omni Iuda: operatusque est bonum et rectum, et verum coram Domino Deo suo
Abin da Hezekiya ya yi ke nan ko’ina a Yahuda, yana yin abin da yake da kyau, daidai da kuma mai aminci a gaban Ubangiji Allahnsa.
21 in universa cultura ministerii domus Domini, iuxta legem et ceremonias, volens requirere Deum suum in toto corde suo: fecitque et prosperatus est.
Cikin kome da ya yi cikin hidimar haikalin Allah, cikin biyayya kuma ga doka da umarnai, ya nemi Allahnsa, ya kuma yi aiki gabagadi. Ta haka kuwa ya yi nasara.