< Marcum 3 >
1 Et introivit iterum in synagogam: et erat ibi homo habens manum aridam.
Sai kuma ya sake tafiya cikin Majami'a sai ga wani Mutum mai shanyayyen hannu.
2 Et observabant eum, si sabbatis curaret, ut accusarent illum.
Wadansu mutane suna kallonsa sosai, su gani ko zai warkar da shi a ranar Asabar. don su zarge shi.
3 Et ait homini habenti manum aridam: Surge in medium.
Yesu ya ce wa mai shanyayyen hanun “Ka tashi ka tsaya a tsakiyar kowa.”
4 Et dicit eis: Licet sabbatis benefacere, an male? animam salvam facere, an perdere? At illi tacebant.
Sai ya ce wa mutane, “Ya dace a yi abu mai kyau aranar Asabar ko a yi mugunta; a ceci rai, ko a yi kisa? “Amma suka yi shiru.
5 Et circumspiciens eos cum ira, contristatus super cæcitate cordis eorum, dicit homini: Extende manum tuam. Et extendit, et restituta est manus illi.
Sai ya dube su cikin fushi, yana bakin ciki da taurin zuciyar su, ya ce wa mutumin ka mikar da hanunka, sai ya mikar da hanunsa Yesu kuwa ya warkar da shi.
6 Exeuntes autem pharisæi, statim cum Herodianis consilium faciebant adversus eum quomodo eum perderent.
Sai Farisiyawa suka fita da sauri zuwa wurin mutanen Hirudus suka shirya yadda za su kashe shi.
7 Jesus autem cum discipulis suis secessit ad mare: et multa turba a Galilæa et Judæa secuta est eum,
Sai Yesu da almajiransa, suka tafi bakin teku. sai mutane dayawa suka bi shi, daga Galili da Yahudiya
8 et ab Jerosolymis, et ab Idumæa, et trans Jordanem: et qui circa Tyrum et Sidonem multitudo magna, audientes quæ faciebat, venerunt ad eum.
Daga Urushalima da Edom gaba da Urdun da kewayan Taya da Sidon, da baban taro, ya ji abinda yake yi. suka zo wurinsa.
9 Et dicit discipulis suis ut navicula sibi deserviret propter turbam, ne comprimerent eum:
Ya tambayi almajiransa su shirya masa karamin jirgin ruwa domin yawan mutane, domin kada su murkushe shi.
10 multos enim sanabat, ita ut irruerent in eum ut illum tangerent, quotquot habebant plagas.
Ya warkar da mutane da yawa, yadda duk wadanda suke da cuttutuka suna kokari su taba shi.
11 Et spiritus immundi, cum illum videbant, procidebant ei: et clamabant, dicentes:
Duk sa'adda kazaman ruhohin suka ganshi, sai su durkusa a gabansa su yi ihu da karfi su ce, kai Dan Allah ne.”
12 Tu es Filius Dei. Et vehementer comminabatur eis ne manifestarent illum.
Ya umarce su da karfi kada su sa a san shi.
13 Et ascendens in montem vocavit ad se quos voluit ipse: et venerunt ad eum.
Ya hau saman dutsen, ya kira wadanda yake bukar su, su zo wurinsa.
14 Et fecit ut essent duodecim cum illo: et ut mitteret eos prædicare.
Ya zabi guda goma sha biyu (ya kira su manzanni). Wadanda zasu kasance tare da shi, ya kuma aike su, su yi wa, azi,
15 Et dedit illis potestatem curandi infirmitates et ejiciendi dæmonia.
Ya kuma basu Ikon fitar da aljanu.
16 Et imposuit Simoni nomen Petrus:
Ya zabi guda goma sha biyu wato Saminu kuma yaba shi suna Bitrus.
17 et Jacobum Zebedæi, et Joannem fratrem Jacobi, et imposuit eis nomina Boanerges, quod est, Filii tonitrui:
Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan-uwan Yakubu wanda ya basu sunan Buwanarjis watau 'ya'yan tsawa,
18 et Andræam, et Philippum, et Bartholomæum, et Matthæum, et Thomam, et Jacobum Alphæi, et Thaddæum, et Simonem Cananæum,
da Andarawus da Filibus da Bartalamawus da Matta da Toma da Yakubu dan Halfa, da Taddawus da Saminu Ba-kananiye,
19 et Judam Iscariotem, qui et tradidit illum.
da Yahuza Iskariyoti wanda zai bashe shi.
20 Et veniunt ad domum: et convenit iterum turba, ita ut non possent neque panem manducare.
Sa'adda ya shiga gida, Taron kuwa ya sake haduwa, har ya hana su cin abinci,
21 Et cum audissent sui, exierunt tenere eum: dicebant enim: Quoniam in furorem versus est.
Da iyalansa suka ji haka, sai suka fito sun kamo shi, saboda sun ce, “Ai, baya cikin hankalinsa “
22 Et scribæ, qui ab Jerosolymis descenderant, dicebant: Quoniam Beelzebub habet, et quia in principe dæmoniorum ejicit dæmonia.
Marubutan da suka zo daga Urushalima suka ce “Ai Ba'alzabuba ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.”
23 Et convocatis eis in parabolis dicebat illis: Quomodo potest Satanas Satanam ejicere?
Yesu ya kirawo su wurinsa ya ce da su cikin misalai, “Yaya shaidan zai iya fitar da shaidan?
24 Et si regnum in se dividatur, non potest regnum illud stare.
idan mulki ya rabu gida biyu ba zai tsayawa ba.
25 Et si domus super semetipsam dispertiatur, non potest domus illa stare.
Haka in gida ya rabu kashi biyu, gaba da kansa bai zai tsaya ba.
26 Et si Satanas consurrexerit in semetipsum, dispertitus est, et non poterit stare, sed finem habet.
Shaidan kuma in ya tayar wa kansa ya rabu, ba zai iya tsayawa ba, gama karshen sa ya zo kenan.
27 Nemo potest vasa fortis ingressus in domum diripere, nisi prius fortem alliget, et tunc domum ejus diripiet.
Amma ba mai iya shiga gidan kakkarfan mutum ya kwace kayansa, ba tare da ya fara daure kakkarfan mutumin ba, sa'an nan kuma ya kwashe kayan gidansa.
28 Amen dico vobis, quoniam omnia dimittentur filiis hominum peccata, et blasphemiæ quibus blasphemaverint:
Hakika, ina gaya maku, dukan zunuban da mutane suka yi za a gafarta masu, da kowane irin sabon da suka furta,
29 qui autem blasphemaverit in Spiritum Sanctum, non habebit remissionem in æternum, sed reus erit æterni delicti. (aiōn , aiōnios )
amma fa duk wanda yayi sabon Ruhun Mai Tsarki baza a gafarta masa ba ko kadan, ya zama mai zunubi har abada.” (aiōn , aiōnios )
30 Quoniam dicebant: Spiritum immundum habet.
“Yesu ya fadi wadannan abubuwa domin suna cewa yana da ba kazamin ruhu,”
31 Et veniunt mater ejus et fratres: et foris stantes miserunt ad eum vocantes eum,
Sa'an nan uwatasa, da “Yan'uwansa suka zo suna tsaye a waje. sai suka aika masa, suna kuma umurtar sa ya zo.
32 et sedebat circa eum turba: et dicunt ei: Ecce mater tua et fratres tui foris quærunt te.
Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka yi magana da shi da cewa, ga uwarka da yan-uwanka suna nan a waje, suna nemanka.”
33 Et respondens eis, ait: Quæ est mater mea et fratres mei?
Ya amsa masu, “Dacewa su wanene uwa-ta da “yan'uwa na? “
34 Et circumspiciens eos, qui in circuitu ejus sedebant, ait: Ecce mater mea et fratres mei.
Sai ya waiwayi wadanda suke zaune kewaye da shi, yace, “Ga uwa-ta da yan-uwana anan!
35 Qui enim fecerit voluntatem Dei, hic frater meus, et soror mea, et mater est.
Gama duk wanda ke yin abin da Allah yake so, shine dan'uwana da yar, uwata, da kuma uwa-ta.”