< Iohannem 21 >

1 Postea manifestavit se iterum Jesus discipulis ad mare Tiberiadis. Manifestavit autem sic:
Bayan wadannan abubuwa, Yesu ya sake bayyana kansa ga almajiran a bakin tekun Tibariya. Ga yadda ya bayyana kansa:
2 erant simul Simon Petrus, et Thomas, qui dicitur Didymus, et Nathanaël, qui erat a Cana Galilææ, et filii Zebedæi, et alii ex discipulis ejus duo.
Saminu Bitrus na tare da Toma wanda ake kira Dan Tagwai, da Natana'ilu daga Kana ta kasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma wadansu almajiran Yesu biyu.
3 Dicit eis Simon Petrus: Vado piscari. Dicunt ei: Venimus et nos tecum. Et exierunt, et ascenderunt in navim: et illa nocte nihil prendiderunt.
Saminu Bitrus yace masu, “Zani su.” sukace masa “Mu ma za mu je tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgi, amma a daren nan basu kama komai ba.
4 Mane autem facto stetit Jesus in littore: non tamen cognoverunt discipuli quia Jesus est.
To, gari na wayewa, sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran basu gane cewa Yesu bane.
5 Dixit ergo eis Jesus: Pueri, numquid pulmentarium habetis? Responderunt ei: Non.
Sai Yesu yace masu, “Samari, kuna da wani abinda za a ci?” Suka amsa masa sukace “A'a”.
6 Dicit eis: Mittite in dexteram navigii rete, et invenietis. Miserunt ergo: et jam non valebant illud trahere præ multitudine piscium.
Yace masu, “Ku jefa taru dama da jirgin zaku samu wasu.” Suka jefa tarunsu har suka kasa jawo shi don yawan kifin.
7 Dixit ergo discipulus ille, quem diligebat Jesus, Petro: Dominus est. Simon Petrus cum audisset quia Dominus est, tunica succinxit se (erat enim nudus) et misit se in mare.
Sai almajirin nan da Yesu yake kauna yace wa Bitrus, “Ubangiji ne fa!” Da Saminu Bitrus yaji, Ashe, Ubangiji ne, yayi damara da taguwarsa, (don a tube yake), ya fada a tekun.
8 Alii autem discipuli navigio venerunt (non enim longe erant a terra, sed quasi cubitis ducentis), trahentes rete piscium.
Sauran almajiran kuwa suka zo a cikin karamin jirgi, (domin basu da nisa da kasa, kamar kamu dari biyu zuwa sama), janye da tarun cike da kifi.
9 Ut ergo descenderunt in terram, viderunt prunas positas, et piscem superpositum, et panem.
Da isowarsu gaci, sai suka ga garwashin wuta a wurin da kifi akai, da kuma gurasa.
10 Dicit eis Jesus: Afferte de piscibus, quos prendidistis nunc.
Yesu ya ce masu “Ku kawo wandansu daga cikin kifin da kuka kama yanzu”.
11 Ascendit Simon Petrus et traxit rete in terram, plenum magnis piscibus centum quinquaginta tribus. Et cum tanti essent, non est scissum rete.
Sai Saminu Bitrus ya hau, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku. Amma duk da yawansu, tarun bai tsage ba.
12 Dicit eis Jesus: Venite, prandete. Et nemo audebat discumbentium interrogare eum: Tu quis es? scientes, quia Dominus est.
Yesu yace masu, “Ku zo ku karya kumallo”. Daga cikin almajiran kuwa babu wanda yayi karfin halin tambayarsa “Ko shi wanene?” Domin sunsani Ubangiji ne.
13 Et venit Jesus, et accipit panem, et dat eis, et piscem similiter.
Yesu zo ya dauki gurasar ya ba su, haka kuma kifin.
14 Hoc jam tertio manifestatus est Jesus discipulis suis cum resurrexisset a mortuis.
Wannan shine karo na uku da Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan tashinsa daga matattu.
15 Cum ergo prandissent, dicit Simoni Petro Jesus: Simon Joannis, diligis me plus his? Dicit ei: Etiam Domine, tu scis quia amo te. Dicit ei: Pasce agnos meos.
Da suka karya kumallon, Yesu yace wa Saminu Bitrus, “Bitrus dan Yahaya, kana kaunata fiye da wadannan?” Bitrus yace masa “I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka” Yesu yace masa “Ka ciyar da 'ya'yan tumakina”.
16 Dicit ei iterum: Simon Joannis, diligis me? Ait illi: Etiam Domine, tu scis quia amo te. Dicit ei: Pasce agnos meos.
Ya sake fada masa karo na biyu, “Saminu Dan Yahaya, kana kaunata?” Bitrus Yace masa “I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka”. Yesu yace masa, “Ka lura da Tumakina”.
17 Dicit ei tertio: Simon Joannis, amas me? Contristatus est Petrus, quia dixit ei tertio: Amas me? et dixit ei: Domine, tu omnia nosti, tu scis quia amo te. Dixit ei: Pasce oves meas.
Ya sake fada masa, karo na uku, “Bitrus Dan Yahaya, kana kaunata? Sai Bitrus bai ji dadi ba domin Yesu ya fada masa karo na uku, “Kana kaunata” Yace masa, “Ubangiji ka san komai duka, ka sani ina kaunarka.” Yesu yace masa “Ka ciyar da tumaki na.
18 Amen, amen dico tibi: cum esses junior, cingebas te, et ambulabas ubi volebas: cum autem senueris, extendes manus tuas, et alius te cinget, et ducet quo tu non vis.
Hakika, hakika, Ina gaya maka, lokacin da kake kuruciyarka, kakan yi wa kanka damara, ka tafi inda ka ga dama. amma in ka tsufa, zaka mike hannuwanka wani yayi maka damara, ya kai ka inda baka nufa ba.”
19 Hoc autem dixit significans qua morte clarificaturus esset Deum. Et cum hoc dixisset, dicit ei: Sequere me.
To Yesu ya fadi haka ne domin ya nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi ga daukakar Allah. Bayan ya fadi haka, sai yace wa Bitrus, ka biyo ni.
20 Conversus Petrus vidit illum discipulum, quem diligebat Jesus, sequentem, qui et recubuit in cœna super pectus ejus, et dixit: Domine, quis est qui tradet te?
Bitrus ya juya sai ya ga almajirin da Yesu yake kauna yana biye dasu; wanda ya jingina a kirgin Yesu lokacin cin jibin nan da yace “Ya Ubangiji, wanene zai bashe ka?”
21 Hunc ergo cum vidisset Petrus, dixit Jesu: Domine, hic autem quid?
Da Bitrus ya gan shi, yace wa Yesu “Ya Ubangiji, Me mutumin nan zai yi?”
22 Dicit ei Jesus: Sic eum volo manere donec veniam, quid ad te? tu me sequere.
Yesu yace masa, “Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka? Ka biyo ni.”
23 Exiit ergo sermo iste inter fratres quia discipulus ille non moritur. Et non dixit ei Jesus: Non moritur, sed: Sic eum volo manere donec veniam, quid ad te?
Wannan zance ya yadu cikin 'yan'uwa cewa, wannan almajirin ba zai mutu ba. Alhali Yesu bai cewa Bitrus, wannan almajirin ba zai mutu ba, Amma “Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka?”
24 Hic est discipulus ille qui testimonium perhibet de his, et scripsit hæc: et scimus quia verum est testimonium ejus.
Wannan shine almajirin da yake shaida wadannan abubuwa, wanda ya rubuta su, kuma mun tabbata shaidarsa gaskiya ne.
25 Sunt autem et alia multa quæ fecit Jesus: quæ si scribantur per singula, nec ipsum arbitror mundum capere posse eos, qui scribendi sunt, libros.
Akwai kuma sauran abubuwa da yawa wanda Yesu yayi. Idan da an rubuta kowannensu daya bayan daya, ina gaya maku, ko duniya bazata iya daukar litattafan da za a rubuta ba.

< Iohannem 21 >