< 누가복음 22 >

1 유월절이라 하는 무교절이 가까우매
Anan nan idin gurasa mara yisti ya yi kusa, wanda a ke kira Idin ketarewa.
2 대제사장들과 서기관들이 예수를 무슨 방책으로 죽일꼬 연구하니 이는 저희가 백성을 두려워함이더라
Manyan firistoci da marubuta suka yi shawara yadda za su kashe Yesu, gama suna jin tsoron mutane.
3 열둘 중에 하나인 가룟인이라 부르는 유다에게 사단이 들어가니
Shaidan ya shiga Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin goma sha biyun.
4 이에 유다가 대제사장들과 군관들에게 가서 예수를 넘겨 줄 방책을 의논하매
Yahuza ya je ya yi shawara da manyan firistoci da Jarumawa yadda zai ba da Yesu a garesu.
5 저희가 기뻐하여 돈을 주기로 언약하는지라
Suka yi farin ciki, suka yarda su ba shi kudi.
6 유다가 허락하고 예수를 무리가 없을 때에 넘겨 줄 기회를 찾더라
Sai ya yarda, sai ya nimi dama yadda zai ba da shi garesu a lokacin da babu taro.
7 유월절 양을 잡을 무교절일이 이른지라
Ranar idin gurasa mara yisti ya yi, da dole za a yi hadayan rago na Idin ketarewa.
8 예수께서 베드로와 요한을 보내시며 가라사대 가서 우리를 위하여 유월절을 예비하여 우리로 먹게 하라
Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce masu, “Ku je ku shirya mana abincin Idin ketarewa, domin mu ci.”
9 여짜오되 어디서 예비하기를 원하시나이까
Suka tambaye shi, “A ina ka ke so mu shirya?”
10 이르시되 보라 너희가 성내로 들어가면 물 한 동이를 가지고 가는 사람을 만나리니 그의 들어가는 집으로 따라 들어가서
Ya amsa masu, “Ku ji, sa'adda ku ka shiga birnin, wani mutum mai dauke da tulun ruwa zai same ku. Ku bishi zuwa cikin gidan da za ya shiga.
11 그 집 주인에게 이르되 선생님이 네게 하는 말씀이 내가 내 제자들과 함께 유월절을 먹을 객실이 어디 있느뇨 하시더라 하라
Sai ku gaya wa mai gidan, 'Malam ya ce, “Ina dakin baki, inda zan ci abincin Idin ketarewa da almajirai na?'”
12 그리하면 저가 자리를 베푼 큰 다락방을 보이리니 거기서 예비하라 하신대
Zai nuna maku babban bene wanda yake a shirye. Ku shirya a can.”
13 저희가 나가 그 하시던 말씀대로 만나 유월절을 예비하니라
Sai suka tafi, suka sami komai kamar yadda ya gaya masu. Sai suka shirya abincin Idin ketarewan.
14 때가 이르매 예수께서 사도들과 함께 앉으사
Sa'adda lokacin ya yi, ya zauna da almajiran.
15 이르시되 내가 고난을 받기 전에 너희와 함께 이 유월절 먹기를 원하고 원하였노라
Sai ya ce masu, “Ina da marmari matuka in ci wannan abincin Idin ketarewa da ku kamin in sha wahala.
16 내가 너희에게 이르노니 이 유월절이 하나님의 나라에서 이루기까지 다시 먹지 아니하리라 하시고
Gama na ce maku, ba zan ci shi kuma ba, sai dai an cika shi a mulkin Allah.”
17 이에 잔을 받으사 사례하시고 가라사대 이것을 갖다가 너희끼리 나누라
Sai Yesu ya dauki koko, sa'adda ya yi godiya, sai yace, “Karba wannan, ku rarraba a tsakaninku.
18 내가 너희에게 이르노니 내가 이제부터 하나님의 나라가 임할 때까지 포도나무에서 난 것을 다시 마시지 아니하리라 하시고
Gama ina ce maku, ba zan sha wannan ruwan inabi kuma ba, sai dai mulkin Allah ya zo.”
19 또 떡을 가져 사례하시고 떼어 저희에게 주시며 가라사대 이것은 너희를 위하여 주는 내 몸이라 너희가 이를 행하여 나를 기념하라 하시고
Sai ya dauki gurasa, sa'adda ya yi godiya, ya kakkarya shi, sai ya ba su, cewa, “Wannan jikina ne wanda aka bayar dominku. Ku yi wannan domin tunawa da ni.”
20 저녁 먹은 후에 잔도 이와 같이 하여 가라사대 이 잔은 내 피로 세우는 새 언약이니 곧 너희를 위하여 붓는 것이라
Sai ya dauki kokon kuma bayan jibi, cewa, “Wannan koko sabon alkawari ne cikin jinina, wanda aka zubar dominku.
21 그러나 보라 나를 파는 자의 손이 나와 함께 상 위에 있도다
Amma ku yi lura. Wanda zai bashe ni yana tare da ni a teburi.
22 인자는 이미 작정된 대로 가거니와 그를 파는 그 사람에게는 화가 있으리로다 하시니
Gama Dan Mutum zai tafi lallai kamar yadda aka kaddara. Amma kaiton wannan mutum da shine za ya bashe shi!”
23 저희가 서로 묻되 우리 중에서 이 일을 행할 자가 누구일까 하더라
Sai suka fara tambaya a tsakaninsu, wanene a cikinmu da zai yi wannan abu.
24 또 저희 사이에 그 중 누가 크냐 하는 다툼이 난지라
Sai gardama ta tashi a tsakaninsu game da wanene mafi girma.
25 예수께서 이르시되 이방인의 임금들은 저희를 주관하며 그 집권자들은 은인이라 칭함을 받으나
Ya ce masu, “Sarakunan al'ummai suna nuna iko akansu, kuma wadanda suke da iko a kansu ana ce da su masu mulki da daraja.
26 너희는 그렇지 않을지니 너희 중에 큰 자는 젊은 자와 같고 두목은 섬기는 자와 같을지니라
Amma kada ya zama haka da ku. A maimakon haka, bari wanda ya ke mafi girma a cikinku ya zama mafi kankanta. Bari wanda yafi muhimmanci kuma ya zama kamar mai hidima.
27 앉아서 먹는 자가 크냐 섬기는 자가 크냐 앉아 먹는 자가 아니냐 그러나 나는 섬기는 자로 너희 중에 있노라
Gama wanene yafi girma, wanda ya zauna a teburi, ko kuwa wanda yake yin hidima? Ba wanda ya zauna a teburi ba? Duk da haka ina kamar mai hidima a tsakaninku.
28 너희는 나의 모든 시험 중에 항상 나와 함께 한 자들인즉
Amma ku ne wadanda ku ke tare da ni a cikin jarabobina.
29 내 아버지께서 나라를 내게 맡기신 것 같이 나도 너희에게 맡겨
Na baku mulki, kamar yadda Ubana ya ba ni mulki,
30 너희로 내 나라에 있어 내 상에서 먹고 마시며 또는 보좌에 앉아 이스라엘 열두 지파를 다스리게 하려 하노라
domin ku ci ku kuma sha a teburi na mulkina. Za ku zauna a kan kursiyai kuna shari'anta kabilun nan goma sha biyu na Israila.
31 시몬아, 시몬아, 보라 사단이 밀 까부르듯 하려고 너희를 청구하였으나
Siman, Siman, ka yi hankali, shaidan ya nemi izini a bada kai domin ya tankade ka kamar alkama.
32 그러나 내가 너를 위하여 네 믿음이 떨어지지 않기를 기도하였노니 너는 돌이킨 후에 네 형제를 굳게 하라
Amma na yi maka addu'a, saboda kada bangaskiyarka ta fadi. Bayan da ka juyo kuma, ka karfafa 'yan'uwanka.”
33 저가 말하되 주여 내가 주와 함께 옥에도, 죽는 데도 가기를 준비하였나이다
Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ina shirye in tafi tare da kai zuwa cikin kurkuku da zuwa mutuwa.”
34 가라사대 베드로야 내가 네게 말하노니 오늘 닭 울기 전에 네가 세 번 나를 모른다고 부인하리라 하시니라
Yesu ya amsa masa, “Ina gaya maka, Bitrus, kamin caran zakara a yau, za ka yi musu na sau uku cewa ba ka sanni ba.”
35 저희에게 이르시되 내가 너희를 전대와 주머니와 신도 없이 보내었을 때에 부족한 것이 있더냐 가로되 없었나이다
Sa'annan Yesu ya ce masu, “Lokacin da na aike ku babu jaka, ko burgami ko takalma, ko kun rasa wani abu? Sai suka amsa, “Babu.”
36 이르시되 이제는 전대 있는 자는 가질 것이요 주머니도 그리하고 검 없는 자는 겉옷을 팔아 살지어다
Ya kuma ce masu, “Amma yanzu, wanda ya ke da jaka, bari ya dauka, da kuma burgami. Wanda ba shi da takobi sai ya sayar da taguwarsa ya sayi guda.
37 내가 너희에게 말하노니 기록된 바 저는 불법자의 동류로 여김을 받았다 한 말이 내게 이루어져야 하리니 내게 관한 일이 이루어 감이니라
Gama ina ce maku, abin da aka rubuta game da ni dole sai ya cika, 'An lisafta shi kamar daya daga cikin masu karya doka.' Gama abinda aka fada akaina ya cika.”
38 저희가 여짜오되 주여 보소서 여기 검 둘이 있나이다 대답하시되 족하다 하시니라
Sai suka ce, “Ubangiji, duba! Ga takuba biyu.” Sai ya ce masu, “Ya isa.”
39 예수께서 나가사 습관을 좇아 감람 산에 가시매 제자들도 좇았더니
Bayan cin abincin yamma, Yesu ya tafi, kamar yadda ya saba yi, zuwa dutsen Zaitun, sai almajiran suka bi shi.
40 그곳에 이르러 저희에게 이르시되 시험에 들지 않기를 기도하라 하시고
Sa'adda suka iso, ya ce masu, “Ku yi addu'a domin kada ku shiga cikin jaraba.”
41 저희를 떠나 돌 던질 만큼 가서 무릎을 꿇고 기도하여
Ya rabu da su misalin nisan jifa, sai ya durkusa kasa ya yi addu'a,
42 가라사대 아버지여 만일 아버지의 뜻이어든 이 잔을 내게서 옮기시옵소서 그러나 내 원대로 마옵시고 아버지의 원대로 되기를 원하나이다 하시니
yana cewa “Uba, in ka yarda, ka dauke wannan kokon daga gareni. Ko da yake ba nufina ba, amma bari naka nufin ya kasance.”
43 사자가 하늘로부터 예수께 나타나 힘을 돕더라
Sai mala'ika daga sama ya bayyana a wurinsa, yana karfafa shi.
44 예수께서 힘쓰고 애써 더욱 간절히 기도하시니 땀이 땅에 떨어지는 핏방울 같이 되더라
Yana cikin wahala sosai, sai ya dukufa cikin addu'a, har zufarsa kuma tana diga a kasa kamar gudajen jini.
45 기도 후에 일어나 제자들에게 가서 슬픔을 인하여 잠든 것을 보시고
Sa'adda ya tashi daga addu'arsa, sai ya zo wurin almajiran, ya same su suna barci domin bakin cikinsu,
46 이르시되 어찌하여 자느냐 시험에 들지 않게 일어나 기도하라 하시니라
sai ya tambaye su, “Don me kuke barci? Tashi ku yi addu'a, saboda kada ku shiga cikin jaraba.”
47 말씀하실 때에 한 무리가 오는데 열둘 중에 하나인 유다라 하는 자가 그들의 앞에 서서 와서
Sa'adda yana cikin magana, sai, ga taron jama'a suka bayana, tare da Yahuza, daya daga cikin sha biyun, ya na jagabansu. Sai ya zo kusa da Yesu domin ya yi masa sumba,
48 예수께 입을 맞추려고 가까이 하는지라 예수께서 이르시되 유다야 네가 입맞춤으로 인자를 파느냐 하시니
amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, za ka ba da Dan Mutum da sumba?”
49 좌우가 그 될 일을 보고 여짜오되 주여 우리가 검으로 치리이까 하고
Sa'adda wadanda suke kewaye da Yesu suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, “Ubangiji, mu yi sara da takobi ne?”
50 그 중에 한 사람이 대제사장의 종을 쳐 그 오른편 귀를 떨어뜨린지라
Sai daya daga cikinsu ya kai wa bawan babban firist sara a kunne, sai ya yanke masa kunnensa na dama.
51 예수께서 일러 가라사대 이것까지 참으라 하시고 그 귀를 만져 낫게 하시더라
Yesu ya ce, “Ya isa haka.” Sai ya taba kunnensa, sai ya warkar da shi.
52 예수께서 그 잡으러 온 대제사장들과 성전의 군관들과 장로들에게 이르시되 너희가 강도를 잡는 것 같이 검과 몽치를 가지고 나왔느냐
Yesu yace wa manyan firistoci, da masu tsaron haikali, da dattawa wadanda suke gaba da shi, “Kun fito kamar za ku kama dan fashi, da takuba da sanduna?
53 내가 날마다 너희와 함께 성전에 있을 때에 내게 손을 대지 아니하였도다 그러나 이제는 너희 때요 어두움의 권세로다 하시더라
Sa'adda nake tare da ku kowace rana a haikali, ba ku kama ni ba. Amma wannan shine lokacinku, da kuma ikon duhu.”
54 예수를 잡아 끌고 대제사장의 집으로 들어갈새 베드로가 멀찍이 따라가니라
Suka kama shi, sai suka tafi da shi, suka kawo shi cikin gidan babban firist. Amma Bitrus yana binsa daga nesa.
55 사람들이 뜰 가운데 불을 피우고 함께 앉았는지라 베드로도 그 가운데 앉았더니
Bayan da suka hura wuta a tsakiyar gidan da suka zazzauna tare, Bitrus ya zaune a tsakaninsu.
56 한 비자가 베드로의 불빛을 향하여 앉은 것을 보고 주목하여 가로되 이 사람도 그와 함께 있었느니라 하니
Sai wata baranya ta ganshi ya zauna a hasken wuta, sai ta zura masa ido ta ce, “Wannan mutum ma yana tare da shi.”
57 베드로가 부인하여 가로되 이 여자여 내가 저를 알지 못하노라 하더라
Amma Bitrus ya yi musu, yana cewa, “Mace, ban san shi ba.”
58 조금 후에 다른 사람이 보고 가로되 너도 그 당이라 하거늘 베드로가 가로되 이 사람아 나는 아니로라 하더라
Bayan dan karamin lokaci sai wani mutum ya gan shi, sai ya ce, “Kaima kana daya daga cikinsu.” Amma Bitrus ya ce, “Mutumin, ba ni ba ne.”
59 한 시쯤 있다가 또 한 사람이 장담하여 가로되 이는 갈릴리 사람이니 참으로 그와 함께 있었느니라
Bayan sa'a daya sai wani mutum ya nace da cewa, “Gaskiya wannan mutum yana tare da shi, gama shi dan Galili ne.”
60 베드로가 가로되 이 사람아 나는 너 하는 말을 알지 못하노라고 방금 말할 때에 닭이 곧 울더라
Amma Bitrus ya ce, “Mutumin, ban san abin da kake fada ba.” Sai nan da nan, da yana cikin magana, sai zakara ta yi cara.
61 주께서 돌이켜 베드로를 보시니 베드로가 주의 말씀 곧 오늘 닭 울기 전에 네가 세 번 나를 부인하리라 하심이 생각나서
Yana juyawa, sai Ubangiji ya dubi Bitrus. Sai Bitrus ya tuna kalmar Ubangiji, sa'adda ya ce masa, “Kafin zakara ya yi cara yau za ka musunce ni sau uku.”
62 밖에 나가서 심히 통곡하니라
Da fitowarsa waje, Bitrus ya yi kuka mai zafi.
63 지키는 사람들이 예수를 희롱하고 때리며
Sai mutanen da ke tsare da Yesu suka yi masa ba'a da bulala kuma.
64 그의 눈을 가리우고 물어 가로되 선지자 노릇 하라 너를 친 자가 누구냐 하고
Bayan da suka rufe masa idanu, suka tambaye shi, cewa, “Ka yi annabci! Wa ya buge ka?”
65 이 외에도 많은 말로 욕하더라
Suka yi wadansu miyagun maganganu na sabo game da Yesu.
66 날이 새매 백성의 장로들 곧 대제사장들과 서기관들이 모이어 예수를 그 공회로 끌어들여
Da gari ya waye, sai dattawa suka hadu tare, da manyan firistoci da marubuta. Sai suka kai shi cikin majalisa
67 가로되 네가 그리스도여든 우리에게 말하라 대답하시되 내가 말할지라도 너희가 믿지 아니할 것이요
suka ce, “Gaya mana, in kai ne Almasihu.” Amma yace masu, “Idan na gaya maku, ba za ku gaskanta ba,
68 내가 물어도 너희가 대답지 아니할 것이니라
idan na yi maku tambaya, ba za ku amsa ba.
69 그러나 이제 후로는 인자가 하나님의 권능의 우편에 앉아 있으리라 하시니
Amma nan gaba, Dan Mutum zai zauna a hannun dama na ikon Allah.”
70 다 가로되 그러면 네가 하나님의 아들이냐 대답하시되 너희 말과 같이 내가 그니라
Suka ce masa, “Ashe kai Dan Allah ne?” Sai Yesu ya ce masu, “Haka kuka ce, nine.”
71 저희가 가로되 어찌 더 증거를 요구하리요 우리가 친히 그 입에서 들었노라 하더라
Suka ce, “Don me muke neman shaida? Gama mu da kanmu munji daga bakinsa.”

< 누가복음 22 >