< 이사야 14 >
1 여호와께서 야곱을 긍휼히 여기시며 이스라엘을 다시 택하여 자기 고토에 두시리니 나그네 된 자가 야곱 족속에게 가입되어 그들과 연합할 것이며
Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai; zai sāke zaɓi Isra’ila yă kuma zaunar da su a ƙasarsu. Baƙi ma za su zo su zauna tare da su su haɗa kai da gidan Yaƙub.
2 민족들이 그들을 데리고 그들의 본토에 돌아오리니 이스라엘 족속이 어호와의 땅에서 그들을 얻어 노비를 삼겠고 전에 자기를 사로잡던 자를 사로잡고 자기를 압제하던 자를 주관하리라
Al’ummai za su ɗauke su su kuma kawo wurin da yake nasu. Gidan Isra’ila kuwa za tă mallaki al’ummai a matsayin bayi maza da mata a ƙasar Ubangiji. Za su mai da waɗanda suka kama su su zama kamammu su kuma yi mulki a kan waɗanda suka taɓa danne su.
3 여호와께서 너를 슬픔과 곤고와 및 너의 수고하는 고역에서 놓으시고 안식을 주시는 날에
A ranar da Ubangiji ya hutashe ku daga wahala da azaba da muguwar bauta,
4 너는 바벨론 왕에 대하여 이 노래를 지어 이르기를 학대하던 자가 어찌 그리 그쳤으며 강포한 성이 어찌 그리 폐하였는고
za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a. Mai danniya ya zo ga ƙarshe! Dubi yadda fushinsa ya ƙare!
5 여호와께서 악인의 몽둥이와 패권자의 홀을 꺾으셨도다
Ubangiji ya karye sandar mugaye, sandan mulkin masu mulki,
6 그들이 분내어 여러 민족을 치되 치기를 마지 아니하였고 노하여 열방을 억압하여도 그 억압을 막을 자 없었더니
wanda cikin fushi ya kashe mutane da bugu marar ƙarewa, kuma cikin fushi ya mamaye al’ummai da fushi ba ƙaƙƙautawa.
7 이제는 온 땅이 평안하고 정온하니 무리가 소리질러 노래하는도다
Dukan ƙasashe suna hutawa suna kuma cikin salama; sun ɓarke da waƙa.
8 향나무와 레바논 백향목도 너로 인하여 기뻐하여 이르기를 네가 넘어뜨리웠은즉 올라와서 우리를 작벌할 자 없다 하는도다
Har itatuwan fir ma da kuma al’ul na Lebanon suna murna a kanka suna cewa, “Yanzu da aka ƙasƙantar da kai, babu wani mai yankan katakon da ya zo yă yanka mu.”
9 아래의 음부가 너로 인하여 소동하여 너의 옴을 영접하되 그것이 세상에서의 모든 영웅을 너로 인하여 동하게 하며 열방의 모든 왕으로 그 보좌에서 일어서게 하므로 (Sheol )
Kabari a ƙarƙashi duk ya shirya don yă sadu da kai a zuwanka; yana tā da ruhohin da suka rasu don su gaishe ka, dukan waɗanda sun taɓa zama shugabanni a duniya; ya sa suka tashi daga kujerun sarauta, dukan waɗanda suke sarakuna a kan al’ummai. (Sheol )
10 그들은 다 네게 말하여 이르기를 너도 우리 같이 연약하게 되었느냐 너도 우리 같이 되었느냐 하리로다
Duk za su amsa, za su ce maka, “Ashe kai ma raunana ne, kamar mu; ka zama kamar mu.”
11 네 영화가 음부에 떨어졌음이여 너의 비파 소리까지로다 구더기가 네 아래 깔림이여 지렁이가 너를 덮었도다 (Sheol )
An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari, tare da surutan garayunka; tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka tsutsotsi kuma suka rufe ka. (Sheol )
12 너 아침의 아들 계명성이여 어찌 그리 하늘에서 떨어졌으며 너 열국을 엎은 자여 어찌 그리 땅에 찍혔는고
Yaya aka yi ka fāɗo daga sama Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba! An fyaɗa ka da ƙasa, kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!
13 네가 네 마음에 이르기를 내가 하늘에 올라 하나님의 뭇별 위에 나의 보좌를 높이리라 내가 북극 집회의 산 위에 좌정하리라
Ka yi tunani a ranka ka ce, “Zan hau zuwa sama; zan ɗaga kursiyina sama da taurarin Allah; zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro, a can ƙurewar saman dutse mai tsarki.
14 가장 높은 구름에 올라 지극히 높은 자와 비기리라 하도다
Zan haura can bisa gizagizai; zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.”
15 그러나 이제 네가 음부 곧 구덩이의 맨 밑에 빠치우리로다 (Sheol )
Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari, zuwa zurfafan rami. (Sheol )
16 너를 보는 자가 주목하여 너를 자세히 살펴 보며 말하기를 이 사람이 땅을 진동시키며 열국을 경동시키며
Waɗanda suka gan ka sun zura maka ido, suna tunani abin da zai same ka. “Wannan mutumin ne ya girgiza duniya ya kuma sa mulkoki suka razana,
17 세계를 황무케 하며 성읍을 파괴하며 사로잡힌 자를 그 집으로 놓아 보내지 않던 자가 아니뇨 하리로다
mutumin da ya mai da duniya ta zama hamada, wanda ya tumɓuke biranenta bai kuma bar kamammunsa suka tafi ba?”
18 열방의 왕들은 모두 각각 자기 집에서 영광 중에 자건마는
Dukan sarakunan duniya suna kwance a mace, kowa a kabarinsa.
19 오직 너는 자기 무덤에서 내어쫓겼으니 가증한 나무가지 같고 칼에 찔려 돌구덩이에 빠진 주검에 둘러싸였으니 밟힌 시체와 같도다
Amma an jefar da kabarinka kamar reshen da aka ƙi; an rufe ka da waɗanda aka kashe, tare da waɗanda aka soke da takobi, waɗanda suka gangara zuwa duwatsun rami. Kamar gawar da aka tattake da ƙafa,
20 네가 자기 땅을 망케 하였고 자기 백성을 죽였으므로 그들과 일반으로 안장함을 얻지 못하나니 악을 행하는 자의 후손은 영영히 이름이 나지 못하리로다
ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba, gama ka hallaka ƙasarka ka kuma kashe mutanenka. Ba za a ƙara ambaci zuriyarka masu aikata mugunta ba.
21 너희는 그들의 열조의 죄악을 인하여 그 자손 도륙하기를 예비하여 그들로 일어나 땅을 취하여 세상에 성읍을 충만케 하지 못하게 하라
A shirya wuri don a yayyanka’ya’yansa maza saboda zunuban kakanninsu; kada a reno su su gāji ƙasar su cika duniya da biranensu.
22 만군의 여호와께서 말씀하시되 내가 일어나 그들을 쳐서 그 이름과 남은 자와 아들과 후손을 바벨론에서 끊으리라 나 여호와의 말이니라
“Zan yi gāba da su,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kau da sunan Babilon da waɗanda suka rage da rai a cikinta,’ya’yanta da zuriyarta,” in ji Ubangiji.
23 내가 또 그것으로 고슴도치의 굴혈과 물웅덩이가 되게 하고 또 멸망의 비로 소제하리라 나 만군의 여호와의 말이니라
“Zan mai da ita wuri domin mujiyoyi da kuma fadama; zan share ta da tsintsiyar hallaka,” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.
24 만군의 여호와께서 맹세하여 가라사대 나의 생각한 것이 반드시 되며 나의 경영한 것이 반드시 이루리라
Ubangiji Maɗaukaki ya rantse, “Tabbatacce, kamar yadda na riga na shirya, haka zai kasance, kuma kamar yadda na nufa, haka zai zama.
25 내가 앗수르 사람을 나의 땅에서 파하며 나의 산에서 발아래 밟으리니 그 때에 그의 멍에가 이스라엘에게서 떠나고 그의 짐이 그들의 어깨에서 벗어질 것이라
Zan ragargazar da Assuriya a cikin ƙasata; a kan duwatsuna zan tattake shi. Za a ɗauke nauyin da ya sa wa mutanena, a kuma ɗauke nauyinsa daga kafaɗunsu.”
26 이것이 온 세계를 향하여 정한 경영이며 이것이 열방을 향하여 편 손이라 하셨나니
Wannan shi ne shirin da na yi domin dukan duniya; wannan shi ne hannun da aka miƙa a bisa dukan al’ummai ke nan.
27 만군의 여호와께서 경영하셨은즉 누가 능히 그것을 폐하며 그 손을 펴셨은즉 누가 능히 그것을 돌이키랴
Gama Ubangiji Maɗaukaki ya ƙudura ya yi wannan, wa kuwa zai hana shi? Ya riga ya miƙa hannunsa, wa zai komar da shi?
Wannan abin da Allah ya yi magana ya zo ne a shekarar da Sarki Ahaz ya mutu.
29 블레셋 온 땅이여 너를 치던 막대기가 부러졌다고 기뻐하지 말라 뱀의 뿌리에서는 독사가 나겠고 그 열매는 나는 불뱀이 되리라
Kada ku yi farin ciki, dukanku Filistiyawa, cewa sandar da ta buge ku ta karye; daga saiwar wannan maciji wani mugun maciji mai dafi zai taso,’ya’yansa za su zama wani maciji masu dafi mai tashi sama.
30 가난한 자의 장자는 먹겠고 빈핍한 자는 평안히 누우려니와 내가 너의 뿌리를 기근으로 죽일 것이요 너의 남은 자는 살륙을 당하리라
Mafi talauci na matalauta zai sami wurin kiwo, mabukata kuma za su kwana lafiya. Amma zan hallakar da saiwarka da matsananciyar yunwa; za tă kashe naka da suka rage da rai.
31 성문이여 슬피 울지어다 성읍이여 부르짖을지어다 너 블레셋이여 다 소멸되게 되었도다 대저 연기가 북방에서 오는데 그 항오를 떨어져 행하는 자 없느니라
Ki yi ihu, ya ke ƙofa! Yi kururuwa, ya ke birni! Ku razana, dukanku Filistiyawa! Ƙunshin hayaƙi yana tasowa daga arewa, kuma babu matsorata a cikin sojojinsa.
32 그 나라 사신들에게 어떻게 대답하겠느냐 여호와께서 시온을 세우셨으니 그의 백성의 곤고한 자들이 그 안에서 피난하리라 할 것이니라
Wace amsa ce za a bayar wa jakadun wannan al’umma? “Ubangiji ya kafa Sihiyona, kuma a cikinta mutanensa masu shan azaba za su sami mafaka.”