< 고린도전서 7 >
1 너희의 쓴 말에 대하여는 남자가 여자를 가까이 아니함이 좋으나
Game da abubuwan da kuka rubuto: “Yayi kyau ga mutum kada ya taba mace.”
2 음행의 연고로 남자마다 자기 아내를 두고 여자마다 자기 남편을 두라
Amma Saboda jarabobi na ayyukan fasikanci masu yawa, ya kamata kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma ta kasance da mijinta.
3 남편은 그 아내에게 대한 의무를 다하고 아내도 그 남편에게 그렇게 할지라
Kowanne maigidanci ya ba matarsa hakin ta, kuma kowace mace ta ba maigidan ta hakinsa na saduwa da juna.
4 아내가 자기 몸을 주장하지 못하고 오직 그 남편이 하며 남편도 이와 같이 자기 몸을 주장하지 못하고 오직 그 아내가 하나니
Matan ba ta da iko akan jikin ta amma maigidan ne. Haka ma, maigidan bashi da iko akan jikinsa amma matar ce.
5 서로 분방하지 말라 다만 기도할 틈을 얻기 위하여 합의상 얼마 동안은 하되 다시 합하라 이는 너희의 절제 못함을 인하여 사단으로 너희를 시험하지 못하게 하려 함이라
Kada ku hana wa junanku saduwa, sai dai da yardar junanku domin wani dan lokaci. Kuyi haka domin ku bada kanku ga addu'a. Daganan sai ku sake saduwa, domin kada Shaidan ya jarabce ku saboda rashin kamun kanku.
6 그러나 내가 이 말을 함은 권도요 명령은 아니라
Amma ina fada maku wadannan abubuwa ne a matsayin nuni, ba a matsayin umurni ba.
7 나는 모든 사람이 나와 같기를 원하노라 그러나 각각 하나님께 받은 자기의 은사가 있으니 하나는 이러하고 하나는 저러하니라
Na so da kowa da kowa kamar ni yake. Amma kowa na da baiwarsa daga wurin Allah. Wani na da irin wannan baiwar, wani kuma waccan.
8 내가 혼인하지 아니한 자들과 및 과부들에게 이르노니 나와 같이 그냥 지내는 것이 좋으니라
Ga marasa aure da gwamraye, Ina cewa, yana da kyau a garesu su zauna ba aure, kamar yadda nike.
9 만일 절제할 수 없거든 혼인하라 정욕이 불 같이 타는 것보다 혼인하는 것이 나으니라
Amma idan baza su iya kame kansu ba, ya kamata su yi aure. Gama yafi masu kyau su yi aure da su kuna da sha'awa.
10 혼인한 자들에게 내가 명하노니 (명하는 자는 내가 아니요 주시라) 여자는 남편에게서 갈리지 말고
Ga masu aure kwa, ina bada wannan umarni- ba ni ba, amma Ubangiji: “Kada mace ta rabu da mijinta.”
11 (만일 갈릴지라도 그냥 지내든지 다시 그 남편과 화합하든지 하라) 남편도 아내를 버리지 말라
Amma idan har ta rabu da mijinta, sai ta zauna ba aure ko kuma ta shirya da shi. Haka kuma “Kada miji ya saki matarsa.”
12 그 남은 사람들에게 내가 말하노니 (이는 주의 명령이 아니라) 만일 어떤 형제에게 믿지 아니하는 아내가 있어 남편과 함께 살기를 좋아하거든 저를 버리지 말며
Amma ga sauran ina cewa-Ni, ba Ubangiji ba-idan wani dan'uwa yana da mata wadda ba mai bi ba, kuma idan ta yarda ta zauna da shi, to kada ya sake ta.
13 어떤 여자에게 믿지 아니하는 남편이 있어 아내와 함께 살기를 좋아하거든 그 남편을 버리지 말라
Idan kuwa mace tana da miji marar bi, idan ya yarda ya zauna tare da ita, to kada ta kashe aure da shi.
14 믿지 아니하는 남편이 아내로 인하여 거룩하게 되고 믿지 아니하는 아내가 남편으로 인하여 거룩하게 되나니 그렇지 아니하면 너희 자녀도 깨끗지 못하니라 그러나 이제 거룩하니라
Gama miji marar bada gaskiya ya zama kebabbe saboda matarsa, sannan mata marar bada gaskiya ta zama kebbiya saboda mijinta mai bi. In ba haka ba 'ya'yanku za su zama marasa tsarki, amma a zahiri su kebabbu ne.
15 혹 믿지 아니하는 자가 갈리거든 갈리게 하라 형제나 자매나 이런 일에 구속 받을 것이 없느니라 그러나 하나님은 화평 중에서 너희를 부르셨느니라
Amma idan abokin aure marar bi ya fita, a bar shi ya tafi. A irin wannan hali, dan'uwa ko 'yar'uwa ba a daure suke ga alkawarinsu ba. Allah ya kira mu da mu zauna cikin salama.
16 아내 된 자여 네가 남편을 구원할는지 어찌 알 수 있으며 남편된 자여 네가 네 아내를 구원할는지 어찌 알 수 있으리요
Yaya kika sani, ke mace, ko za ki ceci mijinki? ko yaya ka sani, kai miji, ko za ka ceci matarka?
17 오직 주께서 각 사람에게 나눠주신 대로 하나님이 각 사람을 부르신 그대로 행하라 내가 모든 교회에서 이와 같이 명하노라
Bari dai kowa ya yi rayuwar da Ubangiji ya aiyana masa, kamar yadda Allah ya kirawo shi. Wannan ce ka'idata a dukkan ikilisiyu.
18 할례자로 부르심을 받은 자가 있느냐 무할례자가 되지 말며 무할례자로 부르심을 받은 자가 있느냐 할례를 받지 말라
Mutum na da kaciya sa'adda aka kira shi ga bada gaskiya? Kada yayi kokarin bayyana kamar marar kaciya. Mutum ba shi da kaciya sa'adda aka kira ga bangaskiya? To kada ya bidi kaciya.
19 할례 받는 것도 아무 것도 아니요 할례 받지 아니하는 것도 아무 것도 아니로되 오직 하나님의 계명을 지킬 따름이니라
Gama kaciya ko rashin kaciya ba shine mahimmin abu ba. Mahimmin abu shine biyayya da dokokin Allah.
20 각 사람이 부르심을 받은 그 부르심 그대로 지내라
Kowa ya tsaya cikin kiran da yake lokacin da Allah ya kira shi ga bada gaskiya.
21 네가 종으로 있을 때에 부르심을 받았느냐 염려하지 말라 그러나 자유할 수 있거든 차라리 사용하라
Kai bawa ne lokacin da Allah ya kirawo ka? Kada ka damu da haka. Amma idan kana da zarafin samun 'yanci, ka yi haka.
22 주 안에서 부르심을 받은 자는 종이라도 주께 속한 자유자요 또 이와 같이 자유자로 있을 때에 부르심을 받은 자는 그리스도의 종이니라
Domin wanda Ubangiji ya kira shi lokacin da yake bawa, shi 'yantacce ne na Ubangiji. Hakanan kuma, wanda shike 'yantacce lokacin da aka kira shi ga bada gaskiya, Bawan Almasihu ne.
23 너희는 값으로 사신 것이니 사람들의 종이 되지 말라
An saye ku da tsada, donhaka kada ku zama bayin mutane.
24 형제들아 각각 부르심을 받은 그대로 하나님과 함께 거하라
Yan'uwa, a kowace irin rayuwa kowannenmu ke ciki lokacin da aka kira mu ga bada gaskiya, bari mu tsaya a haka.
25 처녀에 대하여는 내가 주께 받은 계명이 없으되 주의 자비하심을 받아서 충성된 자가 되어 의견을 고하노니
Game da wadanda basu taba aure ba, ba ni da wani umarni daga wurin Ubangiji. Amma ina bada ra'ayina kamar mutum wanda, ta wurin jinkan Allah, yake yardajje.
26 내 생각에는 이것이 좋으니 곧 임박한 환난을 인하여 사람이 그냥 지내는 것이 좋으니라
Don haka, Ina ganin saboda yamutsin dake tafe ba da jimawa ba, ya yi kyau mutum ya zauna yadda yake.
27 네가 아내에게 매였느냐 놓이기를 구하지 말며 아내에게서 놓였느냐 아내를 구하지 말라
Kana daure da mace? Kada ka nemi 'yanci daga gare ta. Baka daure da mace? Kada ka nemi auren mace.
28 그러나 장가 가도 죄 짓는 것이 아니요 처녀가 시집 가도 죄 짓는 것이 아니로되 이런 이들은 육신에 고난이 있으리니 나는 너희를 아끼노라
Amma idan ka yi aure, ba ka yi zunubi ba. Kuma idan mace marar aure ta yi aure, bata yi zunubi ba. Saidai su wadanda suka yi aure za sha wahalhalu iri-iri a yayinda suke raye, kuma ina so in raba ku da su.
29 형제들아 내가 이 말을 하노니 때가 단축하여진 고로 이후부터 아내 있는 자들은 없는 자 같이 하며
Amma wannan nike fadi ya'nuwa: lokaci ya kure. Daga yanzu, bari wadanda suke da mata suyi rayuwa kamar basu da su.
30 우는 자들은 울지 않는 자 같이 하며 기쁜 자들은 기쁘지 않은 자 같이 하며 매매하는 자들은 없는 자 같이 하며
Masu kuka su zama kamar marasa kuka, masu farinciki kamar marasa farinciki, masu sayen abubuwa kamar marasa komai.
31 세상 물건을 쓰는 자들은 다 쓰지 못하는 자 같이 하라 이 세상의 형적은 지나감이니라
Wadanda suke harka da duniya kamar ba su harka da ita, domin ka'idar duniyan nan tana kawowa ga karshe.
32 너희가 염려 없기를 원하노라 장가 가지 않은 자는 주의 일을 염려하여 어찌하여야 주를 기쁘시게 할꼬 하되
Ina so ku kubuta daga damuwa mai yawa. Mutum marar aure yana tunani akan al'amuran Ubangiji, yadda zai gamshe shi.
33 장가 간 자는 세상 일을 염려하여 어찌하여야 아내를 기쁘게 할꼬 하여 마음이 나누이며
Amma mai aure yana tunani akan al'amuran duniya, yadda za ya gamshi matarsa,
34 시집 가지 않은 자와 처녀는 주의 일을 염려하여 몸과 영을 다 거룩하게 하려 하되 시집 간 자는 세상 일을 염려하여 어찌하여야 남편을 기쁘게 할꼬 하느니라
hankalinsa ya rabu. Mace marar aure ko budurwa tana tunanin al'amuran Ubangiji, yadda za ta kebe kanta a jiki da ruhu. Amma mace mai aure tana tunanin al'amuran duniya, yadda za ta gamshi mijinta.
35 내가 이것을 말함은 너희의 유익을 위함이요 너희에게 올무를 놓으려 함이 아니니 오직 너희로 하여금 이치에 합하게 하여 분요함이 없이 주를 섬기게 하려 함이라
Ina fadar wannan domin amfaninku ne, ba domin in takura ku ba. Na fadi wannan domin abinda ke daidai, yadda zaku bi Ubangiji ba tare da hankalinku ya rabu ba.
36 누가 자기의 처녀 딸에 대한 일이 이치에 합당치 못한 줄로 생각할 때에 혼기도 지나고 그같이 할 필요가 있거든 마음대로 하라 이것은 죄 짓는 것이 아니니 혼인하게 하라
Amma idan wani yana tunani da cewa baya yin abinda ya dace ga budurwarsa- idan ta wuce shekarun aure, kuma hakan ya zama dole- sai yayi abinda yake so. Ba zunubi yake yi ba. Sai suyi aure.
37 그러나 그 마음을 굳게 하고 또 부득이한 일도 없고 자기 뜻대로 할 권리가 있어서 그 처녀 딸을 머물러 두기로 마음에 작정하여도 잘 하는 것이니라
Amma idan ya tsaya da karfi a zuciyarsa, idan baya shan wani matsi kuma yana iya kame kansa, har ya kudurta a zuciyarsa yayi haka, wato ya kiyaye budurwarsa da yake tashi, to hakan ya yi daidai.
38 그러므로 처녀 딸을 시집 보내는 자도 잘 하거니와 시집 보내지 아니하는 자가 더 잘 하는 것이니라
Don haka, shi wanda ya auri budurwarsa yayi daidai, sannan shi wanda ya zabi yaki yin aure yafi yin daidai.
39 아내가 그 남편이 살 동안에 매여 있다가 남편이 죽으면 자유하여 자기 뜻대로 시집 갈 것이나 주 안에서만 할 것이니라
Mace tana a daure ga mijinta a duk tsawon rayuwarsa. Amma idan mijin ya mutu, tana da 'yanci ta auri duk wanda take so ta aura, amma a cikin Ubangiji.
40 그러나 내 뜻에는 그냥 지내는 것이 더욱 복이 있으리로다 나도 또한 하나님의 영을 받은 줄로 생각하노라
Amma a ganina, za ta fi farinciki idan za ta zauna yadda take. Kuma ina tunanin ni ma ina da Ruhun Allah.