< 시편 49 >
1 (고라 자손의 시. 영장으로 한 노래) 만민들아 이를 들어라 세상의 거민들아 귀를 기울이라
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku ji wannan, dukanku mutane; ku saurara, dukanku waɗanda suke zama a wannan duniya,
babba da yaro mai arziki da talaka.
3 내 입은 지혜를 말하겠고 내 마음은 명철을 묵상하리로다
Bakina zai yi maganar hikima; magana daga zuciyata za tă ba da ganewa.
4 내가 비유에 내 귀를 기울이고 수금으로 나의 오묘한 말을 풀리로다
Zan juye kunnena ga karin magana; da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina.
5 죄악이 나를 따라 에우는 환난의 날에 내가 어찌 두려워하랴
Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo, sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni,
6 자기의 재물을 의지하고 풍부함으로 자긍하는 자는
waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu?
7 아무도 결코 그 형제를 구속하지 못하며 저를 위하여 하나님께 속전을 바치지도 못할 것은
Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi,
8 저희 생명의 구속이 너무 귀하며 영영히 못할 것임이라
kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa,
da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.
10 저가 보리로다 지혜있는 자도 죽고 우준하고 무지한 자도 같이 망하고 저희 재물을 타인에게 끼치는도다
Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu.
11 저희의 속 생각에 그 집이 영영히 있고 그 거처가 대대에 미치리라 하여 그 전지를 자기 이름으로 칭하도다
Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.
12 사람은 존귀하나 장구치 못함이여 멸망하는 짐승같도다
Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
13 저희의 이 행위는 저희의 우매함이나 후세 사람은 오히려 저희 말을 칭찬하리로다 (셀라)
Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu. (Sela)
14 양 같이 저희를 음부에 두기로 작정되었으니 사망이 저희 목자일 것이라 정직한 자가 아침에 저희를 다스리리니 저희 아름다움이 음부에서 소멸하여 그 거처조차 없어지려니와 (Sheol )
Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada. (Sheol )
15 하나님은 나를 영접하시리니 이러므로 내 영혼을 음부의 권세에서 구속하시리로다 (셀라) (Sheol )
Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. (Sela) (Sheol )
16 사람이 치부하여 그 집 영광이 더할 때에 너는 두려워 말지어다
Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru;
17 저가 죽으매 가져가는 것이 없고 그 영광이 저를 따라 내려가지 못함이로다
gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba.
18 저가 비록 생시에 자기를 축하하며 스스로 좋게 함으로 사람들에게 칭찬을 받을지라도
Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara,
19 그 역대의 열조에게로 돌아가리니 영영히 빛을 보지 못하리로다
zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.
20 존귀에 처하나 깨닫지 못하는 사람은 멸망하는 짐승같도다
Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.