< 시편 113 >
1 할렐루야! 여호와의 종들아 찬양하라! 여호와의 이름을 찬양하라
Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji.
2 이제부터 영원까지 여호와의 이름을 찬송할지로다
Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma.
3 해 돋는 데서부터 해 지는 데까지 여호와의 이름이 찬양을 받으시리로다
Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji.
4 여호와는 모든 나라 위에 높으시며 그 영광은 하늘 위에 높으시도다
Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammai
5 여호와 우리 하나님과 같은 자 누구리요 높은 위에 앉으셨으나
Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa,
wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya?
7 가난한 자를 진토에서 일으키시며 궁핍한 자를 거름 무더기에서 드셔서
Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka;
8 방백들 곧 그 백성의 방백들과 함께 세우시며
ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu.
9 또 잉태하지 못하던 여자로 집에 거하게 하사 자녀의 즐거운 어미가 되게 하시는도다 할렐루야
Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji.