< 느헤미야 10 >
1 그 인친 자는 하가랴의 아들 방백 느헤미야와, 시드기야
Waɗanda suka buga hatimin su ne, Nehemiya ɗan Hakaliya, wanda yake gwamna. Zedekiya
da Serahiya, da Azariya, da Irmiya,
da Fashhur, da Amariya, da Malkiya,
da Hattush, da Shebaniya, da Malluk,
da Harim, da Meremot, da Obadiya,
da Daniyel, da Ginneton, da Baruk,
da Meshullam, da Abiya, da Miyamin,
8 마아시야, 빌개, 스마야니 이는 다 제사장이요
da Ma’aziya, da Bilgai, da kuma Shemahiya. Waɗannan su ne Firistocin.
9 또 레위 사람 곧 아사냐의 아들 예수아 헤나닷의 자손 중 빈누이 갓미엘과
Lawiyawan kuwa su ne, Yeshuwa ɗan Azaniya, da Binnuyi ɗan Henadad, da Kadmiyel,
10 그 형제 스바냐, 호디야, 그리다, 블라야, 하난
’yan’uwansu kuwa su ne, Shebaniya, da Hodiya, da Kelita, da Felahiya, da Hanan,
da Mika, da Rehob, da Hashabiya,
da Zakkur, da Sherebiya, da Shebaniya,
da Hodiya, da Bani da kuma Beninu.
14 또 백성의 두목들 곧 바로스, 바핫모압, 엘람, 삿두, 바니,
Shugabannin mutane su ne, Farosh, da Fahat-Mowab, da Elam, da Zattu, da Bani,
da Bunni, da Azgad, da Bebai,
da Adoniya, da Bigwai, da Adin,
da Ater, da Hezekiya, da Azzur,
da Hodiya, da Hashum, da Bezai,
da Harif, da Anatot, da Nebai,
da Magfiyash, da Meshullam, da Hezir,
da Meshezabel, da Zadok, da Yadduwa
da Felatiya, da Hanan, da Anahiya,
da Hosheya, da Hananiya, da Hasshub,
da Hallohesh, da Filha, da Shobek,
da Rehum, da Hashabna, da Ma’asehiya
da Ahiya, da Hanan, da Anan,
da Malluk, da Harim da kuma Ba’ana.
28 그 남은 백성과 제사장들과, 레위 사람들과, 문지기들과, 노래하는 자들과, 느디님 사람들과, 및 이방 사람과 절교하고 하나님의 율법을 준행하는 모든 자와 그 아내와 그 자녀들 무릇 지식과 총명이 있는 자가
“Sauran mutane, wato, firistoci, Lawiyawa, matsaran ƙofofi, mawaƙa, ma’aikatan haikali da dukan waɗanda suka ware kansu daga maƙwabta saboda Dokar Allah, tare da matansu da dukan’ya’yansu maza da mata waɗanda za su iya fahimta,
29 다 그 형제 귀인들을 좇아 저주로 맹세하기를 우리가 하나님의 종 모세로 주신 하나님의 율법을 좇아 우리 주 여호와의 모든 계명과 규례와 율례를 지켜
dukan waɗannan yanzu suka sadu da manyan gari’yan’uwansu, suka rantse, cewa la’ana ta same su idan ba su kiyaye Dokar Allah da aka bayar ta wurin Musa bawan Allah su kuma mai da hankali ga yin biyayya da dukan umarnai, ƙa’idodi da farillan Ubangiji shugabanmu ba.
30 우리 딸은 이 땅 백성에게 주지 아니하고 우리 아들을 위하여 저희 딸을 데려오지 아니하며
“Mun yi alkawari ba za mu ba da’ya’yanmu mata aure ga mutanen da suke kewaye da mu ba, ba kuwa za mu auri’ya’yansu mata wa’ya’yanmu maza ba.
31 혹시 이 땅 백성이 안식일에 물화나 식물을 가져다가 팔려 할지라도 우리가 안식일이나 성일에는 사지 않겠고 제 칠년마다 땅을 쉬게 하고 모든 빚을 탕감하리라 하였고
“Sa’ad da maƙwabta suka kawo kayayyaki ko hatsi don su sayar a ranar Asabbaci, ba za mu saya daga gare su a ranar Asabbaci ko a rana mai tsarki ba. Kowace shekarar Asabbaci ba za mu nome ƙasa ba kuma za mu yafe kowane irin bashi.
32 우리가 또 스스로 규례를 정하기를 해마다 각기 세겔의 삼분 일을 수납하여 하나님의 전을 위하여 쓰게 하되
“Mun ɗauka hakkin bin umarnai na ba da kashi ɗaya bisa uku na shekel kowace shekara don hidimar gidan Allahnmu.
33 곧 진설병과 항상 드리는 소제와 항상 드리는 번제와 안식일과 초하루와 정한 절기에 쓸 것과 성물과 이스라엘을 위하는 속죄제와 우리 하나님의 전의 모든 일을 위하여 쓰게 하였고
Za mu tanada burodin da ake ajiye a kan tebur; za mu ba da hadayun hatsi da hadayun ƙonawa na kullum; za mu ba da hadayun Asabbatai, da na bukukkuwan Sabon Wata da na bukukkuwan da aka ƙayyade; za mu ba da hadayu masu tsarki; za mu ba da hadayun zunubi don a yi kafara domin Isra’ila; mu kuma ba da abubuwan da ake bukata dukan domin ayyukan gidan Allahnmu.
34 또 우리 제사장들과 레위 사람들과 백성들이 제비 뽑아 각기 종족 대로 해마다 정한 기한에 나무를 우리 하나님의 전에 드려서 율법에 기록한대로 우리 하나님 여호와의 단에 사르게 하였고
“Mu, firistoci, da Lawiyawa da kuma mutane, mun jefa ƙuri’a don a san lokacin da kowane iyalinmu zai kawo sadakar itace don ƙonewa a gidan Allahnmu a ƙayyadaddun lokuta a bagaden Ubangiji Allahnmu, kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka.
35 해마다 우리 토지 소산의 맏물과 각종 과목의 첫 열매를 여호와의 전에 드리기로 하였고
“Mun kuma ɗauka hakkin kawo nunan fari na hatsinmu da kuma na kowane itace mai ba da’ya’ya a gidan Ubangiji kowace shekara.
36 또 우리의 맏아들들과 생축의 처음 난 것과 우양의 처음 난 것을 율법에 기록된대로 우리 하나님의 전으로 가져다가 우리 하나님의 전에서 섬기는 제사장들에게 주고
“Kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka, za mu kawo ɗan fari na’ya’yanmu maza da na garken shanunmu, da na tumakinmu, da kuma na awakinmu a gidan Allahnmu, don firistocin da suke aikin a can.
37 또 처음 익은 밀의 가루와 거제물과 각종 과목의 열매와 새 포도주와 기름을 제사장들에게로 가져다가 우리하나님의 전 골방에 두고 또 우리 물산의 십일조를 레위 사람들에게 주리라 하였나니 이 레위 사람들은 우리의 모든 성읍에서 물산의 십일조를 받는 자임이며
“Ban da haka ma, za mu kawo wa ɗakunan ajiyar gidan Allahnmu, abincinmu na farko daga ƙasa, na hadayun hatsinmu, na’ya’yan dukan itatuwanmu da kuma na sabon ruwan inabinmu da mai namu wa firistoci. Za mu kuma kawo zakkar hatsinmu wa Lawiyawa, gama Lawiyawa ne ke karɓan Zakka cikin dukan garuruwan da muke noma.
38 레위 사람들이 십일조를 받을 때에는 아론의 자손 제사장 하나가 함께 있을 것이요 레위 사람들은 그 십일조의 십분 일을 가져다가 우리 하나님의 전 골방 곧 곳간에 두되
Firist wanda yake daga zuriyar Haruna zai raka Lawiyawa sa’ad da suke karɓan zakka, Lawiyawan kuma za su kawo kashi ɗaya bisa goma na zakka zuwa gidan Allahnmu, su kawo a ɗakunan ajiya na baitulmali.
39 곧 이스라엘 자손과 레위 자손이 거제로 드린바 곡식과 새 포도주와 기름을 가져다가 성소의 기명을 두는 골방 곧 섬기는 제사장들과 및 문지기들과 노래하는 자들이 있는 골방에 둘 것이라 그리하여 우리가 우리 하나님의 전을 버리지 아니하리라
Mutanen Isra’ila haɗe da Lawiyawa, za su kawo sadakokinsu na hatsi, sabon ruwan inabi da mai a ɗakunan ajiya inda ake ajiyar kayayyakin wuri mai tsarki da kuma inda firistoci, matsaran ƙofofi da kuma mawaƙa suke zama. “Ba za mu ƙyale gidan Allahnmu ba.”