< 마태복음 18 >

1 그 때에 제자들이 예수께 나아와 가로되 `천국에서는 누가 크니이까?'
Daidai wannan lokacin, almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ''Wanene mafi girma a mulkin sama?''
2 예수께서 한 어린 아이를 불러 저희 가운데 세우시고
Sai Yesu ya kira karamin yaro gunsa, ya sa shi a tsakaninsu,
3 가라사대 진실로 너희에게 이르노니 너희가 돌이켜 어린 아이들과 같이 되지 아니하면 결단코 천국에 들어가지 못하리라
ya ce, ''Hakika ina gaya maku, idan baku juya kun zama kamar kananan yara ba, babu yadda zaku shiga mulkin sama.
4 그러므로 누구든지 이 어린 아이와 같이 자기를 낮추는 그이가 천국에서 큰 자니라
Saboda haka, duk wanda ya kaskantar da kansa kamar karamin yaron nan, shi ne mafi girma a mulkin sama.
5 또 누구든지 내 이름으로 이런 어린아이 하나를 영접하면 곧 나를 영접함이니
Duk wanda ya karbi karamin yaro a suna na, ya karbe ni.
6 누구든지 나를 믿는 이 소자 중 하나를 실족케 하면 차라리 연자 맷돌을 그목에 달리우고 깊은 바다에 빠뜨리우는 것이 나으리라
Amma duk wanda ya sa daya daga cikin 'yan yaran nan da suka gaskanta da ni zunubi, gwamma a rataya dutsen nika a wuyansa a jefa shi cikin zurfin teku.
7 실족케 하는 일들이 있음을 인하여 세상에 화가 있도다 실족케 하는 일이 없을 수는 없으나 실족케 하는 그 사람에게는 화가 있도다
Kaiton duniya saboda lokacin tuntube! Lallai ne wadannan lokuta su zo, amma kaiton mutumin da ta wurinsa ne wadannan lokutan za su zo!
8 만일 네 손이나 네 발이 너를 범죄케 하거든 찍어 내버리라 불구자나 절뚝발이로 영생에 들어가는 것이 두 손과 두 발을 가지고 영원한 불에 던지우는 것보다 나으니라 (aiōnios g166)
Idan hannunka ko kafarka ce za ta sa ka tuntube, ka yanke ta, ka yar daga gare ka. Zai fi maka kyau ka shiga rai da nakasa ko gurguntaka, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta tare da hannayenka ko kafafunka. (aiōnios g166)
9 만일 네 눈이 너를 범죄케 하거든 빼어 내버리라 한 눈으로 영생에 들어가는 것이 두 눈을 가지고 지옥불에 던지우는 것보다 나으니라 (Geenna g1067)
Idan idonka zai sa ka tuntube, ka kwakule shi, ka yar. Zai fi maka kyau ka shiga rai da ido daya, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta da idanu biyu. (Geenna g1067)
10 삼가 이 소자 중에 하나도 업신 여기지 말라 너희에게 말하노니 저희 천사들이 하늘에서 하늘에 계신 내 아버지의 얼굴을 항상 뵈옵느니라
Ku kula fa kada ku rena kananan nan. Domin koyaushe a sama, mala'ikunsu na duban fuskar Ubana da ke sama.
11 (없 음)
[Dan Mutum ya zo ya ceci abinda ya bata].
12 너희 생각에는 어떻겠느뇨 만일 어떤 사람이 양 일백 마리가 있는데 그 중에 하나가 길을 잃었으면 그 아흔 아홉 마리를 산에 두고 가서 길 잃은 양을 찾지 않겠느냐
Menene tunaninku? Idan mutum na da tumaki dari, sa'annan daya ta bata, ashe ba zai bar tassa'in da tara a gefen tudu ya tafi neman wadda ta bata ba?
13 진실로 너희에게 이르노니 만일 찾으면 길을 잃지 아니한 아흔 아홉 마리보다 이것을 더 기뻐하리라
In ya same ta, hakika ina gaya maku, farin cikinsa na samun dayan nan da ta bace, zai fi na tassa'in da taran nan da basu bata ba.
14 이와 같이 이 소자 중에 하나라도 잃어지는 것은 하늘에 계신 너희 아버지의 뜻이 아니니라
Hakanan fa, ba nufin Ubanku dake sama ba ne da ya daga cikin wadannan kananan ya hallaka.
15 네 형제가 죄를 범하거든 가서 너와 그 사람과만 상대하여 권고하라 만일 들으면 네가 네 형제를 얻은 것이요
Idan dan'uwanka yayi maka laifi, fada masa tsakaninku, kai da shi kadai. Idan ya saurare ka, ka maido da dan'uwanka kenan.
16 만일 듣지 않거든 한 두 사람을 데리고 가서 두 세 증인의 입으로 말마다 증참케 하라
Amma in ya ki ya saurare ka, ka je da 'yan'uwa biyu ko uku su zama shaidu, don ta wurin shaidu biyu ko uku ake tabbatar da kowacce kalma.
17 만일 그들의 말도 듣지 않거든 교회에 말하고 교회의 말도 듣지 않거든 이방인과 세리와 같이 여기라
In kuma ya ki ya saurare su, ka kai lamarin ga ikklisiya. Idan ya ki ya saurari ikklisiya, ka maishe shi ba'al'umme da mai karbar haraji.
18 진실로 너희에게 이르노니 무엇이든지 너희가 땅에서 매면 하늘에서도 매일 것이요 무엇이든지 땅에서 풀면 하늘에서도 풀리리라
Hakika ina gaya maku, duk abin da kuka daure a duniya, a daure yake a sama. Abin da kuka kwance kuma, a kwance yake a sama.
19 진실로 다시 너희에게 이르노니 너희 중에 두 사람이 땅에서 합심하여 무엇이든지 구하면 하늘에 계신 내 아버지께서 저희를 위하여 이루게 하시리라
Kuma ina gaya maku, idan mutum ku biyu zaku yarda akan duk abin da zaku roka, Ubana wanda ke a sama zai yi maku shi.
20 두 세 사람이 내 이름으로 모인 곳에는 나도 그들 중에 있느니라
Wurin da mutum biyu ko uku suka taru a cikin sunana, zan kasance tare da su.''
21 그 때에 베드로가 나아와 가로되 `주여, 형제가 내게 죄를 범하면 몇 번이나 용서하여 주리이까? 일곱 번까지 하오리이까?'
Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, ''Ubangiji, sau nawa ne dan'uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?''
22 예수께서 가라사대 네게 이르노니 일곱번뿐 아니라 일흔 번씩 일곱번이라도 할지니라
Yesu ya amsa ya ce masa, ''Ban gaya maka sau bakwai ba, amma bakwai din ma har sau saba'in.
23 이러므로 천국은 그 종들과 회계하려 하던 어떤 임금과 같으니
Saboda haka, za a kwatanta mulkin sama da wani sarki da yake so ya lisafta dukiyarsa dake a hannun barorinsa.
24 회계할 때에 일만 달란트 빚진 자 하나를 데려오매
Da ya fara yin haka, sai aka kawo masa daya daga cikin barorinsa da yake binsa talanti dubu goma.
25 갚을 것이 없는지라 주인이 명하여 그 몸과 처와 자식들과 모든 소유를 다 팔아 갚게 하라 한대
Amma tunda ba shi da abin biya, ubangidansa ya bada umurni a sayar da shi, tare da matarsa da 'ya'yansa da duk mallakarsa, domin a biya.
26 그 종이 엎드리어 절하며 가로되 내게 참으소서 다 갚으리이다 하거늘
Sai baran ya fadi kasa, ya rusuna a gaban ubangidansa ya ce, “Maigida, kayi mani hakuri, zan biya duk abin da na karba.”
27 그 종의 주인이 불쌍히 여겨 놓아 보내며 그 빚을 탕감하여 주었더니
Don haka ubangidansa yayi juyayi, sai ya ce, ya yafe bashin, a saki baran.
28 그 종이 나가서 제게 백 데나리온 빚진 동관 하나를 만나 붙들어 목을 잡고 가로되 빚을 갚으라 하매
Amma bayan an saki wannan baran, ya je ya sami wani baran kamar sa da yake bi bashin dinari dari. Ya cafke shi, ya shake shi a wuya, ya ce, 'Ka biya bashin da nake bin ka.'
29 그 동관이 엎드리어 간구하여 가로되 나를 참아 주소서 갚으리이다 하되
Amma dan'uwansa bara ya roke shi ya ce, kayi mani hakuri, zan biya ka duk abinda na karba.'
30 허락하지 아니하고 이에 가서 저가 빚을 갚도록 옥에 가두거늘
Amma baran nan na farko ya ki. A maimakon haka, ya sa aka jefa dan'uwansa bara a kurkuku sai ya biya bashin nan.
31 그 동관들이 그것을 보고 심히 민망하여 주인에게 가서 그 일을 다 고하니
Da sauran barori suka ga abin da ya faru, suka damu kwarai. Sai suka je suka fada wa ubangidansu yadda abin ya faru duka.
32 이에 주인이 저를 불러다가 말하되 악한 종아 네가 빌기에 내가 네 빚을 전부 탕감하여 주었거늘
Sai ubangidansa ya kirawo shi, ya ce masa, ''Kai mugun bawa, na gafarta maka bashin nan duka, domin ka roke ni.
33 내가 너를 불쌍히 여김과 같이 너도 네 동관을 불쌍히 여김이 마땅치 아니하냐 하고
Ashe, bai kamata kaima ka nuna jinkai ga dan'uwanka bara kamar yadda na nuna maka jinkai ba?'
34 주인이 노하여 그 빚을 다 갚도록 저를 옥졸들에게 붙이니라
Ubangidansa yayi fushi, ya danka shi ga masu azabtarwa, har sai ya gama biyan dukan bashin da ake binsa.
35 너희가 각각 중심으로 형제를 용서하지 아니하면 내 천부께서도 너희에게 이와 같이 하시리라
Hakanan Ubana dake a sama zai yi maku, idan kowannenku bai gafarta wa dan'uwansa daga zuciya ba.''

< 마태복음 18 >