< 마가복음 1 >

1 하나님의 아들 예수 그리스도 복음의 시작이라
Wannan itace farkon bisharar Yesu Almasihu, Dan Allah.
2 선지자 이사야의 글에 보라 내가 내 사자를 네 앞에 보내노니 저가 네 길을 예비하리라
kamar yadda aka rubuta cikin littafin annabi Ishaya. Duba, ina aika manzona, a gabanka, wanda zai shirya maka hanya.
3 광야에 외치는 자의 소리가 있어 가로되 너희는 주의 길을 예비하라 그의 첩경을 평탄케 하라 기록된 것과 같이
Akwai murya mai kira a jeji, tana cewa ka shirya hanyar Ubangiji. ka daidaita ta.
4 세례요한이 이르러 광야에서 죄 사함을 받게하는 회개의 세례를 전파하니
Yahaya ya zo, yana baptisma acikin jeji yana wa'azin tuba, domin gafarar zunubai.
5 온 유대 지방과 예루살렘 사람이 다 나아가 자기 죄를 자복하고 요단강에서 그에게 세례를 받더라
Dukan kasar Yahudiya da mutanen Urshalima suka zo wurin sa, a ka kuma yi masu baptisma a kogin urdun. suna furta zunubansu.
6 요한은 약대털을 입고 허리에 가죽띠를 띠고 메뚜기와 석청을 먹더라
Yahaya yana saye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma da damara ta fata a kugunsa, abincinsa fara ce da zuma.
7 그가 전파하여 가로되 `나보다 능력 많으신 이가 내 뒤에 오시나니 나는 그의 신들메를 풀기도 감당치 못하겠노라
Yana wa'azi, ya ce “akwai mai zuwa a bayana wanda ya ke da iko fiye da ni. wanda ko maballin takalminsa ban isa in kwance ba.
8 나는 너희에게 물로 세례 주었거니와 그는 성령으로 너희에게 세례를 주시리라'
Ni ina yi maku baptisma da ruwa, amma mai zuwa a bayana zai yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki''.
9 그 때에 예수께서 갈릴리 나사렛으로부터 와서 요단강에서 요한에게 세례를 받으시고
Sai ya kasance a kwanakin nan Yesu ya zo daga Nazarat ta Galili, sai Yahaya ya yi masa baptisma a kogin urdun.
10 곧 물에서 올라 오실새 하늘이 갈라짐과 성령이 비둘기같이 자기에게 내려 오심을 보시더니
Sa'adda Yesu ya fito daga ruwan, sai sama ta bude, sai Ruhu ya sauko a bisansa da kamanin kurciya.
11 하늘로서 소리가 나기를 `너는 내 사랑하는 아들이라 내가 너를 기뻐 하노라' 하시니라
Sai wata murya ta zo daga sama, tana cewa, “Kai kaunataccen Dana ne. zuciyata ta na murna da kai kwarai''.
12 성령이 곧 예수를 광야로 몰아 내신지라
Sai Ruhu ya iza shi zuwa jeji.
13 광야에서 사십일을 계셔서 사단에게 시험을 받으시며 들짐승과 함께 계시니 천사들이 수종들더라
Yana a jeji kwana arba'in, Shaidan yana jarabtar sa. Yana cikin jeji da dabobi, sai malaiku su ka yi masa hidima.
14 요한이 잡힌 후 예수께서 갈릴리에 오셔서 하나님의 복음을 전파하여
Bayan da aka kama Yahaya, Yesu ya shiga kasar Galili yana wa'azin bisharar Allah.
15 가라사대 `때가 찼고 하나님 나라가 가까왔으니 회개하고 복음을 믿으라!' 하시더라
Yana cewa, “Lokaci ya yi, gama mulkin Allah ya kusato. Ku tuba ku bada gaskiya ga bishara”.
16 갈릴리 해변으로 지나가시다가 시몬과 그 형제 안드레가 바다에 그물 던지는 것을 보고 저희는 어부라
Sa'adda ya ke wucewa a gefen takun Galili, sai ya ga Saminu da Andarawus, dan'uwansa suna jefa taru a teku, domin su masunta ne.
17 예수께서 가라사대 `나를 따라 오너라 내가 너희로 사람을 낚는 어부가 되게 하리라' 하시니
Yesu ya ce masu ku zo, ku biyo ni, ni kuwa sai in maisheku masuntan mutane”.
18 곧 그물을 버려 두고 좇으니라
Nan da nan suka bar tarun su, suka bi shi.
19 조금 더 가시다가 세베대의 아들 야고보와 그 형제 요한을 보시니 저희도 배에 있어 그물을 깁는데
Sa'adda Yesu ya yi tafiya kadan, sai ya ga Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan'uwansa; suna gyaran tarunsu a jirgin ruwa.
20 곧 부르시니 그 아비 세베대를 삯군들과 함께 배에 버려두고 예수를 따라 가니라
Sai ya kira su, su kuwa suka bar mahaifinsu Zabadi a jirgin ruwan da ma'aikatansu, sai su ka bi shi.
21 저희가 가버나움에 들어가니라 예수께서 곧 안식일에 회당에 들어가 가르치시매
Da su ka shigo cikin kafanahum, a ranar asabar, Yesu ya shiga majami'a ya koya masu.
22 뭇사람이 그의 교훈에 놀라니 이는 그 가르치시는 것이 권세 있는 자와 같고 서기관들과 같지 아니함일러라
Su ka yi mamakin koyarwarsa, domin ya na koya masu da iko ba kamar marubuta ba.
23 마침 저희 회당에 더러운 귀신들린 사람이 있어 소리질러 가로되
A nan cikin majami'a akwai wani mutum mai kazamin ruhu, sai ya yi ihu da karfi.
24 `나사렛 예수여 우리가 당신과 무슨 상관이 있나이까? 우리를 멸하러 왔나이까? 나는 당신이 누구인줄 아노니 하나님의 거룩한 자니이다'
Yana cewa Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo ne domin ka halakar da mu? Na san wanene kai. Kai ne Mai Tsarki na Allah”.
25 예수께서 꾸짖어 가라사대 `잠잠하고 그사람에게서 나오라!' 하시니
Sai Yesu ya tsauta wa kazamin ruhun ya ce, “Ka yi shiru ka fita daga cikinsa”.
26 더러운 귀신이 그사람으로 경련을 일으키게 하고 큰소리를 지르며 나오는지라
Bayan da kazamin ruhun ya buga shi kasa, sai kazamin ruhun ya yi ihu sa'annan ya fita daga jikinsa.
27 다 놀라 서로 물어 가로되 `이는 어찜이뇨 권세있는 새 교훈이로다 더러운 귀신들을 명한즉 순종하는도다' 하더라
Sai dukan mutanen su ka yi mamaki kwarai, suna tambayar junansu menene wannan? wace sabuwar koyarwa ce da iko haka? har yana umartar kazaman ruhohi suna kuwa yi masa biyayya!”
28 예수의 소문이 곧 온 갈릴리 사방에 퍼지더라
Nan da nan labarinsa ya bazu ko'ina a dukkan kewayen kasar Galili.
29 회당에서 나와 곧 야고보와 요한과 함께 시몬과 안드레의 집에 들어 가시니
Bayan da suka bar majami'a, sai su ka shiga gidan Saminu da Andarawus, suna kuma tare da Yakubu da Yahaya.
30 시몬의 장모가 열병으로 누웠는지라 사람들이 곧 그의 일로 예수께 여짜온대
Surikar Saminu tana kwance ba lafiya tana fama da zazzabi. Sai suka gaya wa Yesu game da ita.
31 나아가사 그 손을 잡아 일으키시니 열병이 떠나고 여자가 저희에게 수종드니라
Sai ya zo, ya kama hannunta, ya daga ta, sai zazzabin ya sake ta, ta fara yi masu hidima.
32 저물어 해 질때에 모든 병자와 귀신들린 자를 예수께 데려오니
Da yamman nan, bayan da rana ta fadi, sai su ka kawo masa dukan marasa lafiya da masu fama da aljanu.
33 온 동네가 문 앞에 모였더라
Dukan mutanen garin su ka taru a bakin kofa.
34 예수께서 각색 병든 많은 사람을 고치시며 많은 귀신을 내어 쫓으시되 귀신이 자기를 알므로 그 말하는 것을 허락지 아니하시니
ya warkar da masu ciwo da yawa da masu chututtuka iri-iri, ya kuma fitar da bakaken aljanu, amma bai yarda aljanun su yi magana ba domin sun san shi.
35 새벽 오히려 미명에 예수께서 일어나 나가 한적한 곳으로 가사 거기서 기도하시더니
Ya tashi da sassafe, tun da sauran dare, ya tafi wurin da ba kowa, a can ya yi add'ua.
36 시몬과 및 그와 함께 있는 자들이 예수의 뒤를 따라가
Saminu da wandanda suke tare da shi suka neme shi.
37 만나서 가로되 `모든 사람이 주를 찾나이다'
Suka sa me shi, sai su ka ce masa, “kowa yana nemanka”.
38 이르시되 `우리가 다른 가까운 마을들로 가자 거기서도 전도하리니 내가 이를 위하여 왔노라' 하시고
Ya ce, bari mu tafi wani wuri, zuwa wadansu garuruwan da ke kewaye, Saboda in yi wa'azi a can kuma. Wannan shi yasa na zo nan''.
39 이에 온 갈릴리에 다니시며 저희 여러 회당에서 전도하시고 또 귀신들을 내어 쫓으시더라
Ya tafi dukan kasar Galili, yana wa'azi a majimi'un su yana kuma fitar da aljanu.
40 한 문둥병자가 예수께 와서 꿇어 엎드리어 간구하여 가로되 `원하시면 저를 깨끗케 하실수 있나이다'
Wani kuturu ya zo wurinsa. Yana rokonsa, ya durkusa. Ya ce masa, “in ka yarda kana iya warkar da ni.
41 예수께서 민망히 여기사 손을 내밀어 저에게 대시며 가라사대 `내가 원하노니 깨끗함을 받으라!' 하신대
Sai ya yi juyayi, Yesu ya mi ka hannun sa ya ta ba shi ya na ce masa “Na yarda. Ka sarkaka”.
42 곧 문둥병이 그 사람에게서 떠나가고 깨끗하여진지라
Nan da nan kuturtar ta barshi, ya kuma sa mu tsarkakewa.
43 엄히 경계하사 곧 보내시며
Yesu ya yi masa gargadi sosai, ya salame shi.
44 가라사대 `삼가 아무에게 아무 말도 하지 말고 가서 네 몸을 제사장에게 보이고 네 깨끗케 됨을 인하여 모세의 명한 것을 드려 저희에게 증거하라' 하셨더니
Ya ce masa “ka tabbata fa kada ka gayawa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, sai ka je ka yi hadaya domin tsarkakewa kamar yadda Musa ya umurta, domin shaida.
45 그러나 그 사람이 나가서 이 일을 많이 전파하여 널리 퍼지게 하니 그러므로 예수께서 다시는 드러나게 동네에 들어가지 못하시고 오직 바깥 한적한 곳에 계셨으나 사방에서 그에게로 나아오더라
Amma da ya fita sai ya fara gaya wa kowa, ya baza maganar a ko'ina, har Yesu bai iya tafiya a sake a garin ba. Ya tafi ya tsaya a wuraren da ba kowa, mutane kuwa su ka zo wurinsa daga ko'ina.

< 마가복음 1 >