< 마가복음 11 >
1 저희가 예루살렘에 가까이 와서 감람산 벳바게와 베다니에 이르렀을 때에 예수께서 제자 중 둘을 보내시며
Sa’ad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa,
2 이르시되 `너희 맞은편 마을로 가라 그리로 들어가면 곧 아직 아무 사람도 타 보지 않은 나귀 새끼의 매여 있는 것을 보리니 풀어 끌고 오너라
ya ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku, da shigarku, za ku tarar da wani ɗan jaki a daure a can, wanda ba wanda ya taɓa hawa. Ku kunce shi ku kawo nan.
3 만일 누가 너희에게 왜 이리 하느냐? 묻거든 주가 쓰시겠다! 하라 그리하면 즉시 이리로 보내리라' 하시니
In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke yin haka?’ Ku gaya masa cewa, ‘Ubangiji yana bukatarsa, zai kuma dawo da shi ba da jimawa ba.’”
4 제자들이 가서 본즉 나귀 새끼가 문 앞 거리에 매여 있는지라 그것을 푸니
Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, daure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan,
5 거기 섰는 사람 중 어떤 이들이 가로되 `나귀새끼를 풀어 무엇하려느냐?' 하매
sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?”
6 제자들이 예수의 이르신대로 말한대 이에 허락하는지라
Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su.
7 나귀 새끼를 예수께로 끌고 와서 자기들의 겉옷을 그 위에 걸쳐 두매 예수께서 타시니
Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa.
8 많은 사람은 자기 겉옷과 다른 이들은 밭에서 벤 나무가지를 길에 펴며
Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki.
9 앞에서 가고 뒤에서 따르는 자들이 소리지르되 `호산나 찬송하리로다 주의 이름으로 오시는 이여!
Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!”
10 찬송하리로다 오는 우리 조상 다윗의 나라여! 가장 높은 곳에서 호산나' 하더라
“Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!” “Hosanna a can cikin samaniya!”
11 예수께서 예루살렘에 이르러 성전에 들어가사 모든 것을 둘러 보시고 때가 이미 저물매 열 두 제자를 데리시고 베다니에 나가시다
Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.
12 이튿날 저희가 베다니에서 나왔을 때에 예수께서 시장하신지라
Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa.
13 멀리서 잎사귀 있는 한 무화과나무를 보시고 혹 그 나무에 무엇이 있을까 하여 가셨더니 가서 보신즉 잎사귀 외에 아무 것도 없더라 이는 무화과의 때가 아님이라
Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin’ya’yan ɓaure ba ne.
14 예수께서 나무에게 일러 가라사대 `이제부터 영원토록 사람이 네게서 열매를 따먹지 못하리라' 하시니 제자들이 이를 듣더라 (aiōn )
Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka. (aiōn )
15 저희가 예루살렘에 들어가니라 예수께서 성전에 들어가사 성전 안에서 매매하는 자들을 내어 쫓으시며 돈 바꾸는 자들의 상과 비둘기 파는 자들의 의자를 둘러 엎으시며
Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru,
16 아무나 기구를 가지고 성전 안으로 지나다님을 허치 아니하시고
ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki.
17 이에 가르쳐 이르시되 `기록된 바 내 집은 만민의 기도하는 집이라 칭함을 받으리라고 하지 아니하였느냐? 너희는 강도의 굴혈을 만들었도다' 하시매
Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’? Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon’yan fashi.’”
18 대제사장들과 서기관들이 듣고 예수를 어떻게 멸할까 하고 꾀하니 이는 무리가 다 그의 교훈을 기이히 여기므로 그를 두려워함 일러라
Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa.
Da yamma ta yi, sai Yesu da almajiransa suka bar garin.
20 저희가 아침에 지나갈 때에 무화과나무가 뿌리로부터 마른 것을 보고
Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa.
21 베드로가 생각이 나서 여짜오되 `랍비여, 보소서 저주하신 무화과 나무가 말랐나이다'
Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!”
22 예수께서 대답하여 저희에게 이르시되 `하나님을 믿으라!
Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah.
23 내가 진실로 너희에게 이르노니 누구든지 이 산더러 들리어 바다에 던지우라 하며 그 말하는 것이 이를 줄 믿고 마음에 의심치 아니하면 그대로 되리라!
Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa.
24 그러므로 내가 너희에게 말하노니 무엇이든지 기도하고 구하는 것은 받은 줄로 믿으라 그리하면 너희에게 그대로 되리라
Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku.
25 서서 기도할 때에 아무에게나 혐의가 있거든 용서하라 그리하여야 하늘에 계신 너희 아버지도 너희 허물을 사하여 주시리라' 하셨더라
A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”
27 저희가 다시 예루살렘에 들어가니라 예수께서 성전에서 걸어다니실 때에 대제사장들과 서기관들과 장로들이 나아와
Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa.
28 가로되 `무슨 권세로 이런 일을 하느뇨? 누가 이런 일 할 이 권세를 주었느뇨?'
Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?”
29 예수께서 가라사대 `나도 한 말을 너희에게 물으리니 대답하라 그리하면 나도 무슨 권세로 이런 일을 하는지 이르리라
Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.
30 요한의 세례가 하늘로서냐? 사람에게로서냐? 내게 대답하라'
Baftismar Yohanna, daga sama ce, ko daga mutane? Ku faɗa mini!”
31 저희가 서로 의논하여 가로되 `만일 하늘로서라 하면 어찌하여 저를 믿지 아니하였느냐? 할 것이니
Sai suka tattauna a junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
32 그러면 사람에게로서라 할까?' 하였으나 모든 사람이 요한을 참 선지자로 여기므로 저희가 백성을 무서워하는지라
In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’; suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.”
33 이에 예수께 대답하여 가로되 `우리가 알지 못하노라? 하니 예수께서 가라사대 `나도 무슨 권세로 이런 일을 하는지 너희에게 이르지 아니하리라' 하시니라
Saboda haka, suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”