< 누가복음 23 >

1 무리가 다 일어나 예수를 빌라도에게 끌고 가서
Sai duk taron suka tashi, suka kawo Yesu gaban Bilatus.
2 고소하여 가로되 `우리가 이 사람을 보매 우리 백성을 미혹하고 가이사에게 세 바치는 것을 금하며 자칭 왕 그리스도라 하더이다' 하니
Suka fara saransa, cewa “Mun same wannan mutum yana ruda kasarmu, ya haramta a ba Kaisar haraji, yana kuma cewa shi da kansa ne Almasihu, sarki.”
3 빌라도가 예수께 물어 가로되 `네가 유대인의 왕이냐?' 대답하여 가라사대 `네 말이 옳도다'
Bilatus ya tambaye shi, cewa “Shin kaine Sarkin Yahudawa?” Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Haka ka ce.”
4 빌라도가 대제사장들과 무리에게 이르되 `내가 보니 이 사람에게 죄가 없도다' 하니
Sai Bilatus ya ce wa manyan firistocin da taro mai yawa, “Ban samu ko laifi daya game da wannan mutumin ba.”
5 무리가 더욱 굳세게 말하되 `저가 온 유대에서 가르치고 갈릴리에서부터 시작하여 여기까지 와서 백성을 소동케 하나이다'
Amma suka yi ta cewa, “Yana ta da hankalin mutane da koyarwa a dukan Yahudiya, ya fara daga Galili har zuwa ga wannan wuri.”
6 빌라도가 듣고 묻되 `저가 갈릴리 사람이냐?' 하여
Sa'adda Bilatus ya ji wannan, sai ya tambaya ko mutumin daga Galiline.
7 헤롯의 관할에 속한 줄을 알고 헤롯에게 보내니 때에 헤롯이 예루살렘에 있더라
Sa'adda ya gane cewa yana karkashin mulkin Hirudus, sai ya tura Yesu wurin Hirudus, wanda shi da kansa yana Urushalima a wadannan kwanakin.
8 헤롯이 예수를 보고 심히 기뻐하니 이는 그의 소문을 들었으므로 보고자 한 지 오래였고 또한 무엇이나 이적 행하심을 볼까 바랐던 연고러라
Sa'adda Hirudus ya ga Yesu, sai ya cika da farin ciki sosai, saboda ya so ganinsa tunda dadewa. Tun can ya ji game da shi sai ya yi begen ganin wadansu al'ajibai da zai yi.
9 여러 말로 물으나 아무 말도 대답지 아니하시니
Hirudus ya tambaye Yesu cikin kalmomi masu yawa, amma Yesu bai amsa masa da komai ba.
10 대제사장들과 서기관들이 서서 힘써 고소하더라
Sai manyan firistoci da marubuta suka tsaya, suna ta yi masa zargi mai zafi.
11 헤롯이 그 군병들과 함께 예수를 업신여기며 희롱하고 빛난 옷을 입혀 빌라도에게 도로 보내니
Hirudus da sojojinsa suka zarge shi, suka kuma yi masa ba'a, suka sa masa tufafi masu kyau, sa'annan ya sake aika Yesu zuwa wurin Bilatus.
12 헤롯과 빌라도가 전에는 원수이었으나 당일에 서로 친구가 되니라
Sai Hirudus da Bilatus suka zama abokai a wannan rana (da ma su abokai gaba ne).
13 빌라도가 대제사장들과 관원들과 백성을 불러 모으고
Bilatus ya kira manyan firistoci tare da masu mulki da kuma taron jama'ar,
14 이르되 `너희가 이 사람을 백성을 미혹하는 자라 하여 내게 끌어왔도다 보라 내가 너희 앞에서 사실하였으되 너희의 고소하는 일에 대하여 이 사람에게 죄를 찾지 못하였고
sai ya ce masu, “Kun kawo mani wannan mutum kamar wanda yake jagorar mutane ga munanan ayyuka, ku kuma gani, Ni, na tuhume shi a gabanku, ban sami ko kuskure daya daga mutumin nan game da abinda ku ke zarginsa da shi ba.
15 헤롯이 또한 그렇게 하여 저를 우리에게 도로 보내었도다 보라 저의 행한 것은 죽일 일이 없느니라
Babu, ko Hirudus ma, ya sake komar mana da shi, kun gani, babu wani abu wanda ya yi da ya cancanci mutuwa,
16 그러므로 때려서 놓겠노라'
saboda haka zan yi masa horo sa'annan in sake shi.”
17 (없 음)
[Ya zama dole Bilatus ya sakar wa Yahudawa wani daurarre guda daya lokacin idin.]
18 무리가 일제히 소리질러 가로되 `이 사람을 없이하고 바라바를 우리에게 놓아 주소서'하니
Amma dukansu suka yi ihu tare, cewa, “A tafi da wannan mutumin, sai a sako mana Barabbas!”
19 이 바라바는 성중에서 일어난 민란과 살인을 인하여 옥에 갇힌 자러라
Barabbas mutum ne wanda aka sa a cikin kurkuku saboda wani tada hankali a cikin birni da kuma kisankai.
20 빌라도는 예수를 놓고자 하여 다시 저희에게 말하되
Bilatus ya sake yi masu magana, yana so ya saki Yesu.
21 저희는 소리질러 가로되 `저를 십자가에 못박게 하소서! 십자가에 못박게 하소서!' 하는지라
Amma suka yi ihu, cewa, “A giciye shi, a giciye shi.”
22 빌라도가 세 번째 말하되 `이 사람이 무슨 악한 일을 하였느냐? 나는 그 죽일 죄를 찾지 못하였나니 때려서 놓으리라'한대
Sai ya sake ce masu sau na uku, “Don me, wace magunta wannan mutum ya yi? Ban sami wani abu da ya isa sanadin mutuwa game da shi ba. Saboda haka bayan na hore shi, zan sake shi.”
23 저희가 큰 소리로 재촉하여 십자가에 못 박기를 구하니 저희의 소리가 이긴지라
Amma suka nace da murya mai karfi, suna so a giciye shi, sai muryarsu ta rinjayi Bilatus.
24 이에 빌라도가 저희의 구하는대로 하기를 언도하고
Sai Bilatus ya yarda ya yi masu bisa ga abin da suke so.
25 저희의 구하는 자 곧 민란과 살인을 인하여 옥에 갇힌 자를 놓고 예수를 넘겨 주어 저희 뜻대로 하게 하니라
Ya sako masu wanda suka tambaya ya ba su wanda aka sa a kurkuku domin tada hankali da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu bisa nufinsu.
26 저희가 예수를 끌고 갈 때에 시몬이라는 구레네 사람이 시골로서 오는 것을 잡아 그에게 십자가를 지워 예수를 좇게 하더라
Da suka tafi da shi, sai suka kama wani mai suna siman Bakurane, yana zuwa daga karkara, sai suka daura masa giciyen ya dauka, yana biye da Yesu.
27 또 백성과 및 그를 위하여 가슴을 치며 슬피 우는 여자의 큰 무리가 따라 오는지라
Babban taron jama'a, da na mata da suke makoki da kuka dominsa, suna binsa.
28 예수께서 돌이켜 그들을 향하여 가라사대 `예루살렘의 딸들아! 나를 위하여 울지 말고 너희와 너희 자녀를 위하여 울라
Amma da ya juya wurinsu, Yesu yace, “Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka domina, amma ku yi kuka domin kanku da 'ya'yanku.
29 보라, 날이 이르면 사람이 말하기를 수태 못하는 이와 해산하지 못한 배와 먹이지 못한 젖이 복이 있다 하리라
Gama ku gani, kwanaki suna zuwa da za su ce, 'Albarka ta tabbata ga bakararru da wadanda basu taba haihuwa ba da kuma wadanda ba a taba shan mamansu ba.'
30 그 때에 사람이 산들을 대하여 우리 위에 무너지라 하며 작은 산들을 대하여 우리를 덮으라 하리라
Sa'annan za su fara ce wa duwatsu, 'Ku fado bisanmu,' da tuddai ma, 'Ku rufe mu.'
31 푸른 나무에도 이같이 하거든 마른 나무에는 어떻게 되리요' 하시니라
Gama idan sun yi wadannan abubuwan lokacin da itace yana danye, me zai faru sa'adda ya bushe?”
32 또 다른 두 행악자도 사형을 받게 되어 예수와 함께 끌려 가니라
Aka kai wadansu mutum biyu masu laifi, domin a kashe shi tare da su.
33 해골이라 하는 곳에 이르러 거기서 예수를 십자가에 못 박고 두 행악자도 그렇게 하니 하나는 우편에 하나는 좌편에 있더라
Sa'adda suka zo wurin da a ke kira kwalluwa, nan suka giciye shi da barayin, daya daga hannun damansa dayan kuma daga hannun hagu.
34 이에 예수께서 가라사대 `아버지여 저희를 사하여 주옵소서 자기의 하는 것을 알지 못함이니이다' 하시더라 저희가 그의 옷을 나눠 제비 뽑을쌔
Yesu yace, “Uba, ka yafe masu, gama basu san abin da suke yi ba.” Sai suka jefa kuri'a, suka rarraba tufafinsa.
35 백성은 서서 구경하며 관원들도 비웃어 가로되 `저가 남을 구원하였으니 만일 하나님의 택하신 자 그리스도여든 자기도 구원할지어다'하고
Mutane sun tsaya suna kallo sa'annan masu mulki suna ta yin masa ba'a, cewa, “Ya ceci wadansu. Bari ya ceci kansa, idan shine Almasihu na Allah, zababben nan.”
36 군병들도 희롱하면서 나아와 신포도주를 주며
Sojojin ma suka yi masa dariya, suna zuwa wurinsa, suna mika masa ruwan tsami,
37 가로되 `네가 만일 유대인의 왕이어든 네가 너를 구원하라' 하더라
suna cewa, “Idan kai Sarkin Yahudawa ne, ceci kanka.”
38 그의 위에 이는 유대인의 왕이라 쓴 패가 있더라
Akwai wata alama bisansa, “Wannan shine Sarkin Yahudawa.”
39 달린 행악자 중 하나는 비방하여 가로되 `네가 그리스도가 아니냐? 너와 우리를 구원하라' 하되
Daya daga cikin barayi wanda aka giciye, ya zage shi, cewa, “Ba kai ne Almasihu ba? Ka ceci kanka da mu.”
40 하나는 그 사람을 꾸짖어 가로되 `네가 동일한 정죄를 받고서도 하나님을 두려워 아니하느냐?
Amma dayan ya amsa, ya tsauta masa cewa, “Ba ka tsoron Allah, da yake shari'arka daya ne da nasa?
41 우리는 우리의 행한 일에 상당한 보응을 받는 것이니 이에 당연하거니와 이 사람의 행한 것은 옳지 않은 것이 없느니라' 하고
Mu kam an yi ma na daidai, gama mun samu bisa ga abin da muka yi. Amma wannan mutum bai yi wani abu mara kyau ba.”
42 가로되 `예수여 당신의 나라에 임하실 때에 나를 생각하소서!' 하니
Sai ya kara, “Yesu, ka tuna da ni sa'adda ka shiga mulkinka.”
43 예수께서 이르시되 `내가 진실로 네게 이르노니 오늘 네가 나와 함께 낙원에 있으리라!' 하시니라
Yesu ya ce masa, “Gaskiya ina ce maka, yau za ka kasance tare da ni a firdausi.”
44 때가 제 육시쯤 되어 해가 빛을 잃고 온 땅에 어두움이 임하여 제 구시까지 계속하며
Anan nan a wajen sa'a na shida, sai duhu ya mamaye kasar duka har zuwa sa'a na tara
45 성소의 휘장이 한가운데가 찢어지더라
sa'adda rana ya fadi. Sai labulen haikalin ya rabu a tsakiya zuwa kasa.
46 예수께서 큰 소리로 불러 가라사대 `아버지여! 내 영혼을 아버지 손에 부탁하나이다!' 하고 이 말씀을 하신 후 운명하시다
Da kuka da murya mai karfi, Yesu yace, “Uba, na mika Ruhu na a hannunka.” Bayan da ya fadi wannan, sai ya mutu.
47 이 그 된 일을 보고 하나님께 영광을 돌려 가로되 `이 사람은 정녕 의인이었도다' 하고
Sa'adda jarumin ya ga abin da ya faru, ya daukaka Allah, cewa, “Lallai wannan mutumin mai adalci ne.”
48 이를 구경하러 모인 무리도 그 된 일을 보고 다 가슴을 두드리며 돌아가고
Sa'adda dukan taro mai yawa wadanda suka zo tare domin su shaida da idanunsu suka ga abubuwan da suka faru, suka koma suna bugan kirjinsu.
49 예수의 아는 자들과 및 갈릴리로부터 따라온 여자들도 다 멀리 서서 이 일을 보니라
Amma duk idon sani, da kuma matan da suka bi shi tun daga Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban wadannan abubuwa.
50 공회 의원으로 선하고 의로운 요셉이라 하는 사람이 있으니
Ga shi kuwa, wani mutum mai suna Yusufu, shi dan majalisa ne, nagari ne kuma mutum mai adalci ne
51 (저희의 결의와 행사에 가타 하지 아니한 자라) 그는 유대인의 동네 아리마대 사람이요 하나님의 나라를 기다리는 자러니
(bai yarda da shawarar da kuma abin da suka aikata ba), daga Arimatiya a kasar Yahudiya, wanda yake jiran mulkin Allah.
52 빌라도에게 가서 예수의 시체를 달라 하여
Wannan mutum, ya sami Bilatus, ya tambaya a bashi jikin Yesu.
53 이를 내려 세마포로 싸고 아직 사람을 장사한 일이 없는 바위에 판 무덤에 넣어 두니
Ya saukar da shi kasa, sai ya nade shi cikin likafani na linin mai kyau, ya kwantar da shi cikin kabari da aka sassaka shi daga dutse, inda ba a taba binne wani ba.
54 이 날은 예비일이요 안식일이 거의 되었더라
Ranar kuwa, ranar shiri ce, Asabaci kuma ta kusato.
55 갈릴리에서 예수와 함께 온 여자들이 뒤를 좇아 그 무덤과 그의 시체를 어떻게 둔 것을 보고
Matan da suka taho da shi tun daga Galili, suka biyo baya, su ga kabarin da inda aka ajiye shi.
56 돌아가 향품과 향유를 예비하더라 계명을 좇아 안식일에 쉬더라
Suka koma, sai suka shirya kayan kamshi da mai. Suka kuma huta a ranar Asabaci bisa ga doka.

< 누가복음 23 >