< 레위기 21 >

1 여호와께서 모세에게 이르시되 아론의 자손 제사장들에게 고하여 이르라 백성 중의 죽은 자로 인하여 스스로 더럽히지 말려니와
Ubangiji ya ce wa Musa, “Yi magana da firistoci,’ya’yan Haruna maza, ka ce musu, ‘Kada firist yă ƙazantar da kansa saboda wani cikin mutanensa da suka mutu,
2 골육지친인 부모나 자녀나 형제나
sai dai na danginsa na kusa, kamar mahaifiyarsa ko mahaifinsa, ɗansa ko’yarsa, ɗan’uwansa,
3 출가하지 아니한 처녀인 친 자매로 인하여는 몸을 더럽힐 수 있느니라
ko’yar’uwarsa da ba tă riga ta yi aure ba, wadda take dogara gare shi, da yake ba ta da miji, saboda ita zai iya ƙazantar da kansa.
4 제사장은 백성의 어른인즉 스스로 더럽혀 욕되게 하지 말지니라
Kada yă ƙazantar da kansa saboda mutanen da suke da dangantakar da shi ta wurin aure, ta yin haka zai ƙazantar da kansa.
5 제사장은 머리털을 깎아 대머리 같게 하지 말며 그 수염 양편을 깎지 말며 살을 베지 말고
“‘Kada firistoci su aske kansu ƙwal ko su kwakkwafe gemunsu, ko su tsattsage jikunansu.
6 그 하나님께 대하여 거룩하고 그 하나님의 이름을 욕되게 하지 말 것이며 그들은 여호와의 화제 곧 그 하나님의 식물을 드리는 자인즉 거룩할 것이라
Dole su kasance masu tsarki ga Allahnsu, kada kuma su ɓata sunan Allahnsu. Domin sukan miƙa hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta, abincin Allahnsu, saboda haka sai su kasance da tsarki.
7 그들은 기생이나 부정한 여인을 취하지 말 것이며 이혼 당한 여인을 취하지 말지니 이는 그가 여호와께 거룩함이니라
“‘Ba za su auri matan da karuwanci ya ɓata su, ko waɗanda mazansu suka sake su ba, gama firistoci masu tsarki ne ga Allahnsu.
8 너는 그를 거룩하게 하라! 그는 네 하나님의 식물을 드림이니라 너는 그를 거룩히 여기라! 나 여호와 너희를 거룩하게 하는 자는 거룩함이니라
An ɗauke su da tsarki, domin suna miƙa abincin Allahnku. An ɗauka su masu tsarki gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, Ni wanda ya mai da ku masu tsarki.
9 아무 제사장의 딸이든지 행음하여 스스로 더럽히면 그 아비를 욕되게 함이니 그를 불사를지니라
“‘In’yar firist ta ɓata kanta ta wurin zama karuwa, ta kunyatar da mahaifinta ke nan; dole a ƙone ta da wuta.
10 자기 형제 중 관유로 부음을 받고 위임되어 예복을 입은 대제사장은 그 머리를 풀지 말며 그 옷을 찢지 말며
“‘Babban firist, wanda yake ɗaya cikin’yan’uwansa wanda aka shafe da mai a kansa, wanda kuma aka naɗa don yă sa rigunan firistoci, kada yă bar gashin kansa buzu-buzu, ko ya kyakketa rigunansa.
11 어떤 시체에든지 가까이 말지니 부모로 인하여도 더러워지게 말며
Ba zai shiga inda akwai gawa ba. Kada yă ƙazantar da kansa, ko ma ta mahaifinsa ce ko ta mahaifiyarsa.
12 성소에서 나오지 말며 그 하나님의 성소를 더럽히지 말라! 이는 하나님의 위임한 관유가 그 위에 있음이니라 나는 여호와니라!
An keɓe shi domina, kada yă ƙazantar da kansa, kada kuwa yă ɓata Tentin Sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce. Ni ne Ubangiji.
13 그는 처녀를 취하여 아내를 삼을지니
“‘Dole macen da zai aura ta kasance budurwa.
14 과부나 이혼된 여인이나 더러운 여인이나 기생을 취하지 말고 자기 백성 중 처녀를 취하여 아내를 삼아
Ba zai auri matan da mijinta ya mutu, ko macen da mijinta ya rabu da ita, ko macen da ta ɓata kanta ta wurin karuwanci ba, sai dai yă auri budurwa daga cikin mutanensa,
15 그 자손으로 백성 중에서 더럽히지 말지니 나는 그를 거룩하게 하는 여호와임이니라
don kada yă ƙazantar da’ya’yansa a cikin mutanensa. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da shi mai tsarki.’”
16 여호와께서 모세에게 일러 가라사대
Ubangiji ya ce wa Musa,
17 아론에게 고하여 이르라 무릇 너의 대대 자손 중 육체에 흠이 있는 자는 그 하나님의 식물을 드리려고 가까이 오지 못할 것이라
“Faɗa wa Haruna cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, kada ko ɗaya daga cikin zuriyarka, da yake da lahani yă zo kusa domin yă miƙa hadaya ta ci gare ni.
18 무릇 흠이 있는 자는 가까이 못할지니 곧 소경이나, 절뚝발이나, 코가 불완전한 자나, 지체가 더한 자나,
Duk mai lahani, ko makaho, ko gurgu, ko mai naƙasa, ko mai wani lahani a jiki;
19 발 부러진 자나, 손 부러진 자나,
ko mai karyayyen ƙafa, ko mai karyayyen hannu,
20 곱사등이나, 난장이나, 눈에 백막이 있는 자나, 괴혈병이나, 버짐이 있는 자나, 불알 상한 자나,
ko mai ƙusumbi, ko wada, ko wanda yake da lahani a ido, ko mai cuta mai sa ƙaiƙayi, ko mai kirci, ko wanda aka daƙe, ba zai yi kusa domin yă miƙa hadaya ba.
21 제사장 아론의 자손 중에 흠이 있는 자는 나아와 여호와의 화제를 드리지 못할지니 그는 흠이 있은즉 나아와 하나님의 식물을 드리지 못하느니라
Ba zuriyar Haruna firist, mai lahanin da zai zo kusa don yă miƙa hadayun da aka yi ga Ubangiji da wuta. Da yake yana da lahani, ba zai zo kusa don yă miƙa abincin Allahnsa ba.
22 그는 하나님의 식물의 지성물이든지 성물이든지 먹을 것이나
Zai iya cin abinci mafi tsarki na Allahnsa, haka ma abinci mai tsarki;
23 장 안에 들어가지 못할 것이요 단에 가까이 못할지니 이는 그가 흠이 있음이라 이와 같이 그가 나의 성소를 더럽히지 못할 것은 나는 그들을 거룩하게 하는 여호와임이니라!
duk da haka saboda lahaninsa, ba zai yi kusa da labule, ko yă yi kusa da bagade don kada yă ƙazantar da wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji wanda yake mai da su masu tsarki.’”
24 모세가 이대로 아론과 그 아들들과 온 이스라엘 자손에게 고하였더라
Sai Musa ya faɗa wannan wa Haruna da’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa.

< 레위기 21 >