< 요한복음 17 >

1 예수께서 이 말씀을 하시고 눈을 들어 하늘을 우러러 가라사대 아버지여 때가 이르렀사오니 아들을 영화롭게 하사 아들로 아버지를 영화롭게 하게 하옵소서
Da Yesu ya fadi wandannan abubuwa, sai ya tada idanunsa sama ya ce, ya Uba, sa'a ta zo; ka daukaka Danka, domin Dan shi ya daukaka ka,
2 아버지께서 아들에게 주신 모든 자에게 영생을 주게 하시려고 만민을 다스리는 권세를 아들에게 주셨음이로소이다 (aiōnios g166)
kamar yadda ka ba shi iko akan dukkan 'yan adam, ya ba da rai madawwami ga duk wanda ka ba shi. (aiōnios g166)
3 영생은 곧 유일하신 참 하나님과 그의 보내신 자 예수 그리스도를 아는 것이니이다 (aiōnios g166)
Wannan ne rai madawwami: wato su san ka, Allah makadaici na gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Almasihu. (aiōnios g166)
4 아버지께서 내게 하라고 주신 일을 내가 이루어 아버지를 이 세상에서 영화롭게 하였사오니
Na daukaka ka a duniya, na gama aikin da ka ba ni in yi.
5 아버지여 창세 전에 내가 아버지와 함께 가졌던 영화로써 지금도 아버지와 함께 나를 영화롭게 하옵소서
Yanzu, ya Uba, ka daukaka ni tare da kai da daukaka wadda ni ke da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasanci.
6 세상 중에서 내게 주신 사람들에게 내가 아버지의 이름을 나타내었나이다 저희는 아버지의 것이었는데 내게 주셨으며 저희는 아버지의 말씀을 지키었나이다
Na bayyana sunanka ga mutunen da ka ba ni acikin duniya. Na ka suke, ka ba ni su, sun kuwa kiyaye maganarka.
7 지금 저희는 아버지께서 내게 주신 것이 다 아버지께로서 온 것인 줄 알았나이다
Yanzu kuwa sun san duk iyakar abinda ka ba ni daga gare ka yake,
8 나는 아버지께서 내게 주신 말씀들을 저희에게 주었사오며 저희는 이것을 받고 내가 아버지께로부터 나온 줄을 참으로 아오며 아버지께서 나를 보내신 줄도 믿었사옵나이다
don kuwa maganganun da ka fada mani. Na fada masu, sun kuma karba, sun sani kuwa hakika na fito daga gareka ne, kuma sun gaskata kai ne ka aiko ni.
9 내가 저희를 위하여 비옵나니 내가 비옵는 것은 세상을 위함이 아니요 내게 주신 자들을 위함이니이다 저희는 아버지의 것이로소이다
Ina yi masu addu'a. Ba domin duniya ni ke yin addu'a ba, amma domin wadanda ka bani gama na ka ne.
10 내 것은 다 아버지의 것이요 아버지의 것은 내 것이온데 내가 저희로 말미암아 영광을 받았나이다
Gama dukan abinda ke nawa na ka ne, naka kuwa nawa ne, an kuma daukaka ni a cikinsu.
11 나는 세상에 더 있지 아니하오나 저희는 세상에 있사옵고 나는 아버지께로 가옵나니 거룩하신 아버지여 내게 주신 아버지의 이름으로 저희를 보전하사 우리와 같이 저희도 하나가 되게 하옵소서
Ba na cikin duniya kuma, amma wadannan mutane suna cikin duniya, ni kuwa ina zuwa wurin ka. Ya Uba mai Tsarki, ka adanasu cikin sunanka da ka ba ni domin su zama daya, kamar dai yadda muke daya.
12 내가 저희와 함께 있을 때에 내게 주신 아버지의 이름으로 저희를 보전하와 지키었나이다 그 중에 하나도 멸망치 않고 오직 멸망의 자식뿐이오니 이는 성경을 응하게 함이니이다
Lokacin da ina tare da su, na adanasu acikin sunanka da ka ba ni. Na kiyaye su, kuma ko daya kuwa daga cikinsu ba ya bace ba, sai dai dan hallakar nan, domin Nassi ya cika.
13 지금 내가 아버지께로 가오니 내가 세상에서 이 말을 하옵는 것은 저희로 내 기쁨을 저희 안에 충만히 가지게 하려 함이니이다
Amma yanzu ina zuwa wurinka, Ina fadar wadannan abubuwa tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu.
14 내가 아버지의 말씀을 저희에게 주었사오매 세상이 저희를 미워하였사오니 이는 내가 세상에 속하지 아니함같이 저희도 세상에 속하지 아니함을 인함이니이다
Na ba su maganarka, kuma duniya ta tsane su domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.
15 내가 비옵는 것은 저희를 세상에서 데려가시기를 위함이 아니요 오직 악에 빠지지 않게 보전하시기를 위함이니이다
Ba ina roko ka dauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga mugun nan.
16 내가 세상에 속하지 아니함 같이 저희도 세상에 속하지 아니하였삽나이다
Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.
17 저희를 진리로 거룩하게 하옵소서! 아버지의 말씀은 진리니이다!
Ka kebe su domin kanka cikin gaskiya. maganarka gaskiya ce.
18 아버지께서 나를 세상에 보내신 것같이 나도 저희를 세상에 보내었고
Kamar dai yadda ka aiko ni cikin duniya, haka kuma na aike su cikin duniya.
19 또 저희를 위하여 내가 나를 거룩하게 하오니 이는 저희도 진리로 거룩함을 얻게 하려 함이니이다
Na kebe kaina gareka sabili da su, domin su ma kansu a kebe su gareka cikin gaskiya.
20 내가 비옵는 것은 이 사람들만 위함이 아니요 또 저희 말을 인하여 나를 믿는 사람들도 위함이니
Ina addu'a ba domin wadannan kadai ba, amma har da wadanda zasu gaskata da ni ta wurin maganarsu,
21 아버지께서 내 안에 내가 아버지 안에 있는 것같이 저희도 다 하나가 되어 우리 안에 있게 하사 세상으로 아버지께서 나를 보내신 것을 믿게 하옵소서
Domin su zama daya dukansu, kamar yadda kai, ya Uba, ka ke ciki na, ni kuma na ke cikin ka. Ina roko suma su kasance a cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa ka aiko ni
22 내게 주신 영광을 내가 저희에게 주었사오니 이는 우리가 하나가 된 것같이 저희도 하나가 되게 하려 함이니이다
Daukakar da ka bani, ita nake basu, domin su zama daya, kamar yadda mu ke daya;
23 곧 내가 저희 안에 아버지께서 내 안에 계셔 저희로 온전함을 이루어 하나가 되게 하려 함은 아버지께서 나를 보내신 것과 또 나를 사랑하심 같이 저희도 사랑하신 것을 세상으로 알게 하려 함이로소이다
ni a cikinsu, kai kuma a ciki na. Domin su kammalu cikin zama daya, domin duniya ta sani cewa ka aiko ni, kuma ka kaunace su, kamar yadda ka kaunace ni.
24 아버지여 내게 주신 자도 나 있는 곳에 나와 함께 있어 아버지께서 창세 전부터 나를 사랑하시므로 내게 주신 나의 영광을 저희로 보게 하시기를 원하옵니다
Ya Uba, ina so wadanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, domin su dubi daukakata da ka yi mani. Domin ka kaunace ni tun kafin halittar duniya.
25 의로우신 아버지여 세상이 아버지를 알지 못하여도 나는 아버지를 알았삽고 저희도 아버지께서 나를 보내신 줄 알았삽나이다
Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta sanka ba, amma ni na sanka; kuma wadannan sun sani kai ne ka aiko ni.
26 내가 아버지의 이름을 저희에게 알게 하였고 또 알게 하리니 이는 나를 사랑하신 사랑이 저희 안에 있고 나도 저희 안에 있게 하려 함이니이다'
Na sanar masu da sunanka, zan kuma sanar da shi domin kaunar da ka yi mani ta kasance a cikinsu, ni kuma in kasance a cikinsu,

< 요한복음 17 >