< 이사야 5 >

1 내가 나의 사랑하는 자를 위하여 노래 하되 나의 사랑하는 자의 포도원을 노래하리라 나의 사랑하는 자에게 포도원이 있음이여 심히 기름진 산에로다
Zan rera waƙa wa ƙaunataccena waƙa game da gonar inabinsa. Ƙaunataccena yana da gonar inabi a gefen tudu mai dausayi.
2 땅을 파서 돌을 제하고 극상품 포도나무를 심었도다 그 중에 망대를 세웠고 그 안에 술틀을 팠었도다 좋은 포도 맺기를 바랐더니 들 포도를 맺혔도다
Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun ya shuka mata inabi mafi kyau. Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi. Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin, amma sai ga shi inabin ya ba da munanan’ya’ya.
3 예루살렘 거민과 유다 사람들아 구하노니 이제 나와 내 포도원 사이에 판단하라
“Yanzu fa ku mazauna cikin Urushalima da mutanen Yahuda, ku shari’anta tsakanina da gonar inabina.
4 내가 내 포도원을 위하여 행한 것 외에 무엇을 더할 것이 있었으랴 내가 좋은 포도 맺기를 기다렸거늘 들포도를 맺힘은 어찜인고
Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina fiye da abin da na yi mata? Da na nemi inabi masu kyau, me ya sa ta ba da munana’ya’ya?
5 이제 내가 내 포도원에 어떻게 행할 것을 너희에게 이르리라 내가 그 울타리를 걷어 먹힘을 당케 하며 그 담을 헐어 짓밟히게 할 것이요
Yanzu zan faɗa muku abin da zan yi da gonar inabina. Zan cire katangar da ta kewaye ta, za tă kuwa lalace; zan rushe bangonta, za a kuwa tattake ta.
6 내가 그것으로 황무케 하리니 다시는 가지를 자름이나 북을 돋우지 못하여 질려와 형극이 날 것이며 내가 또 구름을 명하여 그 위에 비를 내리지 말라 하리라 하셨으니
Zan mai da ita kango, ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba, sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can Zan umarci gizagizai kada su yi ruwan sama a kanta.”
7 대저 만군의 여호와의 포도원은 이스라엘 족속이요 그의 기뻐하시는 나무는 유다 사람이라 그들에게 공평을 바라셨더니 도리어 포학이요 그들에게 의로움을 바라셨더니 도리어 부르짖음이었도다
Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki ita ce gidan Isra’ila, mutanen Yahuda kuma su ne lambun farin cikinsa. Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini; yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.
8 가옥에 가옥을 연하며 전토에 전토를 더하여 빈 틈이 없도록 하고 이 땅 가운데서 홀로 거하려 하는 그들은 화 있을진저
Kaitonku ku waɗanda kuke ƙara wa kanku gidaje kuke kuma haɗa gonaki da gonaki har babu sauran filin da ya rage ku kuma zauna ku kaɗai a ƙasar.
9 만군의 여호와께서 내 귀에 말씀하시되 정녕히 허다한 가옥이 황폐하리니 크고 아름다울지라도 거할 자가 없을 것이며
Ubangiji Maɗaukaki ya furta a kunnuwana, “Tabbatacce manyan gidajen za su zama kango, za a bar kyawawan gidajen nan ba kowa.
10 열흘갈이 포도원에 겨우 포도주 한 바트가 나겠고 한 호멜지기에는 간신히 한 에바가 나리라 하시도다
Kadada goma na gonar inabi zai ba da garwan ruwan inabi ɗaya kaɗai, mudu guda na iri kuma zai ba da efa na hatsi guda kurum.”
11 아침에 일찌기 일어나 독주를 따라가며 밤이 깊도록 머물러 포도주에 취하는 그들은 화 있을진저
Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe don su nufi wurin shaye-shaye, waɗanda suke raba dare har sai sun bugu da ruwan inabi.
12 그들이 연회에는 수금과 비파와 소고와 저와 포도주를 갖추었어도 여호와의 행하심을 관심치 아니하며 그의 손으로 하신 일을 생각지 아니하는도다
Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu, ganguna da busa da ruwan inabi, amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba, ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.
13 이러므로 나의 백성이 무지함을 인하여 사로잡힐 것이요 그 귀한자는 주릴 것이요 무리는 목마를 것이며
Saboda haka mutanena za su yi zaman bauta domin rashin fahimi; manyan mutanensu za su mutu da yunwa talakawansu kuma su mutu da ƙishirwa.
14 음부가 그 욕망을 크게 내어 한량 없이 그 입을 벌린즉 그들의 호화로움과 그들의 많은 무리와 그들의 떠드는 것과 그 중에서 연락하는 자가 거기 빠질 것이라 (Sheol h7585)
Saboda haka kabari ya fadada marmarinsa ya kuma buɗe bakinsa babu iyaka; cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangara tare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu. (Sheol h7585)
15 천한 자는 굴복되고 귀한 자는 낮아지고 오만한 자의 눈도 낮아질 것이로되
Ta haka za a ƙasƙantar da mutum kuma za a ƙasƙantar da’yan adam, za a ƙasƙanta da masu girman kai.
16 오직 만군의 여호와는 공평하므로 높임을 받으시며 거룩하신 하나님은 의로우시므로 거룩하다 함을 받으시리니
Amma Ubangiji Maɗaukaki zai sami ɗaukaka ta wurin aikata gaskiya, kuma Allah mai tsarki zai nuna kansa ta wurin adalcinsa.
17 그 때에는 어린 양들이 자기 초장에 있는 것 같이 먹을 것이요 살찐 자의 황무한 밭의 소산은 유리하는 자들이 먹으리라
Sa’an nan tumaki za su yi kiwo kamar yadda suke yi a wurin kiwonsu; raguna za su yi kiwo cikin abubuwa masu kyau da suka lalace.
18 거짓으로 끈을 삼아 죄악을 끌며 수레 줄로 함 같이 죄악을 끄는 자는 화 있을찐저
Kaiton waɗanda suke jan zunubi da igiyar ruɗu, da kuma mugunta da igiyoyin keken yaƙin,
19 그들이 이르기를 그는 그 일을 속속히 이루어 우리로 보게 할 것이며 이스라엘의 거룩한 자는 그 도모를 속히 임하게 하여 우리로 알게 할 것이라 하는도다
waɗanda suke cewa, “Bari Allah yă gaggauta, bari yă hanzarta aikinsa don mu gani. Bari yă iso, bari shirin Mai Tsarkin nan na Isra’ila yă zo, don mu sani.”
20 악을 선하다 하며 선을 악하다 하며 흑암으로 광명을 삼으며 광명으로 흑암을 삼으며 쓴 것으로 단 것을 삼으며 단 것으로 쓴 것을 삼는 그들은 화 있을진저
Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagarta nagarta kuma mugunta, waɗanda suke mai da duhu haske haske kuma duhu, waɗanda suke mai da ɗaci zaƙi zaƙi kuma ɗaci.
21 스스로 지혜롭다 하며 스스로 명철하다 하는 그들은 화 있을진저
Kaiton waɗanda suke tsammani suna da hikima da kuma wayo a idonsu.
22 포도주를 마시기에 용감하며 독주를 빚기에 유력한 그들은 화 있을진저
Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabi da gwanaye a haɗin abubuwan sha,
23 그들은 뇌물로 인하여 악인을 의롭다 하고 의인에게서 그 의를 빼았는도다
waɗanda suke ƙyale masu laifi don sun ba da cin hanci, amma su hana a yi gaskiya wa marasa laifi.
24 이로 인하여 불꽃이 그루터기를 삼킴 같이, 마른 풀이 불 속에 떨어짐 같이 그들의 뿌리가 썩겠고 꽃이 티끌처럼 날리니 그들이 만군의 여호와의 율법을 버리며 이스라엘의 거룩하신 자의 말씀을 멸시하였음이라
Saboda haka kamar yadda harshen wuta yakan lashe kara kuma kamar yadda busasshiyar ciyawa takan ƙone ƙurmus a cikin wuta, haka saiwarsu za su ruɓa iska kuma ta hura furanninsu kamar ƙura; gama sun ƙi dokar Ubangiji Maɗaukaki suka kuma ƙyale maganar Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
25 그러므로 여호와께서 자기 백성에게 노를 발하시고 손을 들어 그들을 치신지라 산들은 진동하며 그들의 시체는 거리 가운데 분토같이 되었으나 그 노가 돌아서지 아니하였고 그 손이 오히려 펴졌느니라
Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan mutanensa; ya ɗaga hannunsa ya kuma buge su. Duwatsu sun jijjigu, gawawwaki kuwa suka zama kamar juji a tituna. Saboda wannan duka, fushinsa bai huce ba, bai kuwa janye hannunsa ba.
26 기를 세우시고 먼 나라들을 불러 땅 끝에서부터 오게 하실 것이라 보라 그들이 빨리 달려 올 것이로되
Ya ɗaga tuta don al’ummai masu nisa, ya yi feɗuwa wa waɗanda suke a iyakar duniya. Ga shi sun iso, da sauri da kuma gaggawa!
27 그 중에 곤핍하여 넘어지는 자도 없을 것이며 조는 자나 자는 자도 없을 것이며 그들의 허리띠는 풀리지 아니하며 그들의 신들메는 끊어지지 아니하며
Babu ko ɗayansu da ya gaji ko ya yi tuntuɓe, babu ko ɗaya da ya yi gyangyaɗi ko barci; babu abin ɗamarar da ya kunce a gindi, ba igiyar takalmin da ta tsinke.
28 그들의 살은 날카롭고 모든 활은 당기어졌으며 그 말굽은 부싯돌같고 차 바퀴는 회리바람 같을 것이며
Kibiyoyinsu masu tsini ne, an ɗaura dukan bakkunansu; kofatan dawakansu sun yi kamar dutsen ƙanƙara, ƙafafun keken yaƙinsu kamar guguwa ne.
29 그 부르짖는 것은 암사자 같을 것이요 그 소리지름은 어린 사자들과 같을 것이라 그들이 부르짖으며 물건을 움키어 염려 없이 가져가도 건질 자가 없으리로다
Rurinsu ya yi kamar na zaki, suna ruri kamar’yan zakoki; suna yin gurnani yayinda suke kamun abin da suke farauta su ɗauke shi ba mai ƙwace shi.
30 그 날에 그들이 바다 물결 소리 같이 백성을 향하여 부르짖으리니 사람이 그 땅을 바라보면 흑암과 고난이 있고 빛은 구름에 가리워져서 어두우리라
A wannan rana za su yi ta ruri a kansa kamar rurin teku. Kuma in wani ya dubi ƙasar, zai ga duhu da damuwa; haske ma zai zama duhu ta wurin gizagizai.

< 이사야 5 >