< 히브리서 7 >

1 이 멜기세덱은 살렘 왕이요 지극히 높으신 하나님의 제사장이라 여러 임금을 쳐서 죽이고 돌아오는 아브라함을 만나 복을 빈 자라
Wannan Melkizedek sarkin Salem ne da kuma firist na Allah Mafi Ɗaukaka. Shi ne ya sadu da Ibrahim ya albarkace shi sa’ad da Ibrahim ya dawowa daga cin nasara a bisa sarakuna,
2 아브라함이 일체 십분의 일을 그에게 나눠 주니라 그 이름을 번역한 즉 첫째 의의 왕이요 또 살렘 왕이니 곧 평강의 왕이요
Ibrahim kuwa ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome. Ma’anar sunan Melkizedek ita ce, “sarkin adalci.” Amma da yake Salem yana nufin “salama,” shi kuma “Sarkin salama” ne.
3 아비도 없고 어미도 없고 족보도 없고 시작한 날도 없고 생명의 끝도 없어 하나님 아들과 방불하여 항상 제사장으로 있느니라
Ba shi da mahaifi ko mahaifiya, ba shi da asali, ba shi da farko ko ƙarshe, shi dai kamar Ɗan Allah ne kuma firist ne har abada.
4 이 사람의 어떻게 높은 것을 생각하라 조상 아브라함이 노략물 중 좋은 것으로 십분의 일을 저에게 주었느니라
Ku dubi irin girman da Melkizedek mana. Ko kakanmu Ibrahim ma ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na ganima!
5 레위의 아들들 가운데 제사장의 직분을 받는 자들이 율법을 좇아 아브라함의 허리에서 난 자라도 자기 형제인 백성에게서 십분의 일을 취하라는 명령을 가졌으나
Yanzu doka ta umarci zuriyar Lawi waɗanda suka zama firistoci su karɓi kashi ɗaya bisa goma daga wurin mutane, wato,’yan’uwansu, ko da yake’yan’uwansu zuriyar Ibrahim ne.
6 레위 족보에 들지 아니한 멜기세덱은 아브라함에게서 십분의 일을 취하고 그 얻은 자를 위하여 복을 빌었나니
Ko da yake Melkizedek ba daga zuriyar Lawi ba ne, duk da haka Ibrahim ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na abin da yake da shi, Melkizedek kuwa ya sa masa albarka, shi da aka yi wa alkawura.
7 폐일언하고 낮은 자가 높은 자에게 복 빎을 받느니라
Kowa ya sani cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka.
8 또 여기는 죽을 자들이 십분의 일을 받으나 저기는 산다고 증거를 얻은 자가 받았느니라
Firistoci ake ba wa kashi ɗaya bisa goma na abin da mutane suke samu. Amma dukan firistoci sukan mutu, sai dai Melkizedek, kuma nassi ya ce yana da rai.
9 또한 십분의 일을 받는 레위도 아브라함으로 말미암아 십분의 일을 바쳤다 할 수 있나니
Ana ma iya cewa zuriyar Lawi, mai karɓar kashi ɗaya bisa goma daga mutane, ya ba da kashi ɗaya bisa goma ta wurin Ibrahim,
10 이는 멜기세덱이 아브라함을 만날 때에 레위는 아직 자기 조상의 허리에 있었음이니라
wannan ya kasance haka domin an haifi Lawi daga baya a iyalin Ibrahim wanda ya ba wa Melkizedek kashi ɗaya bisa goma.
11 레위 계통의 제사 직분으로 말미암아 온전함을 얻을 수 있었으면 백성이 그 아래서 율법을 받았으니 어찌하여 아론의 반차를 좇지 않고 멜기세덱의 반차를 좇는 별다른 한 제사장을 세울 필요가 있느뇨
Ko da yake Dokar Musa ta ce dole firistoci su kasance zuriyar Lawi, waɗannan firistoci ba su iya sa wani yă zama cikakke ba. Saboda akwai bukata wani firist kamar Melkizedek ya zo, a maimakon wani daga iyalin Haruna.
12 제사 직분이 변역한즉 율법도 반드시 변역하리니
Gama in aka canja yadda ake zaɓan firist, dole a canja Dokar ita ma.
13 이것은 한 사람도 제단 일을 받들지 않는 지파에 속한 자를 가리켜 말한 것이라
Mutumin da muke wannan zance a kai, ai, shi na wata kabila ce dabam, wadda ba wani daga kabilar da ya taɓa yin hidima a bagade.
14 우리 주께서 유다로 좇아 나신 것이 분명하도다 이 지파에는 모세가 제사장들에 관하여 말한 것이 하나도 없고
Kowa ya san cewa Ubangijinmu ya fito ne daga zuriyar Yahuda ne, kuma Musa bai taɓa ce firistoci za su fito daga wannan kabila ba.
15 멜기세덱과 같은 별다른 한 제사장이 일어난 것을 보니 더욱 분명하도다
Canjin nan a Dokar Allah ya ƙara fitowa fili da wani firist dabam wanda yake kamar Melkizedek ya bayyana.
16 그는 육체에 상관된 계명의 법을 좇지 아니하고 오직 무궁한 생명의 능력을 좇아 된 것이니
Ya zama firist ne ba saboda ya cika wata ƙa’ida ta zama zuriyar Lawi ba, sai dai bisa ga ikon ran da ba a iya hallakawa.
17 증거하기를 네가 영원히 멜기세덱의 반차를 좇는 제사장이라 하였도다 (aiōn g165)
Gama nassi ya ce, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.” (aiōn g165)
18 전엣 계명이 연약하며 무익하므로 폐하고
Ta haka aka kawar da ƙa’ida marar ƙarfi da kuma marar amfani
19 (율법은 아무 것도 온전케 못할지라)이에 더 좋은 소망이 생기니 이것으로 우리가 하나님께 가까이 가느니라
(gama doka ba tă mai da wani abu cikakke ba), yanzu kuwa bege mafi kyau ya ɗauki matsayinta. Ta haka kuma muka matso kusa da Allah.
20 또 예수께서 제사장 된 것은 맹세 없이 된 것이 아니니
Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. Waɗansu sun zama firistocin ba tare da wata rantsuwa ba,
21 (저희는 맹세 없이 제사장이 되었으되 오직 예수는 자기에게 말씀하신 자로 말미암아 맹세로 되신 것이라 주께서 맹세하시고 뉘우치지 아니하시리니 네가 영원히 제사장이라 하셨도다) (aiōn g165)
shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, ba kuwa zai canja zuciyarsa ba, ‘Kai firist ne na har abada.’” (aiōn g165)
22 이와 같이 예수는 더 좋은 언약의 보증이 되셨느니라
Saboda wannan rantsuwa, Yesu ya zama tabbacin alkawari mafi kyau.
23 저희 제사장 된 자의 수효가 많은 것은 죽음을 인하여 항상 있지 못함이로되
To, akwai waɗannan firistoci da yawa, da yake mutuwa ta hana su cin gaba da aikin zaman firist;
24 예수는 영원히 계시므로 그 제사 직분도 갈리지 아니하나니 (aiōn g165)
amma Yesu ba zai mutu ba, don haka zai zama firist har abada. (aiōn g165)
25 그러므로 자기를 힘입어 하나님께 나아가는 자들을 온전히 구원하실 수 있으니 이는 그가 항상 살아서 저희를 위하여 간구하심이니라
Saboda haka ya iya ba da ceto gaba ɗaya ga masu zuwa wurin Allah ta wurinsa, gama kullum a raye yake saboda yă yi roƙo dominsu.
26 이러한 대제사장은 우리에게 합당하니 거룩하고 악이 없고 더러움이 없고 죄인에게서 떠나 계시고 하늘보다 높이 되신 자라
Irin wannan babban firist ne muke bukata, shi mai tsarki ne, marar aibi, mai tsabta, ba kamar mu masu zunubi ba sam. An ɗaukaka shi fiye da kome a sama.
27 저가 저 대제사장들이 먼저 자기 죄를 위하고 다음에 백성의 죄를 위하여 날마다 제사 드리는 것과 같이 할 필요가 없으니 이는 저가 단번에 자기를 드려 이루셨음이니라
Ba ya bukata yă yi ta miƙa hadayu kowace rana saboda zunubansa, sa’an nan saboda zunuban mutane kamar sauran firistoci. Ya miƙa hadaya sau ɗaya tak, sa’ad da ya miƙa kansa.
28 율법은 약점을 가진 사람들을 제사장으로 세웠거니와 율법 후에 하신 맹세의 말씀은 영원히 온전케 되신 아들을 세우셨느니라 (aiōn g165)
Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada. (aiōn g165)

< 히브리서 7 >