< 히브리서 13 >

1 형제 사랑하기를 계속하고
Bari kaunar 'yan'uwa ta cigaba.
2 손님 대접하기를 잊지 말라 이로써 부지중에 천사들을 대접한 이들이 있었느니라
Kada ku manta da karrama baki, domin ta wurin yin haka, wasu suka marabci mala'iku ba tare da saninsu ba.
3 자기도 함께 갇힌 것같이 갇힌 자를 생각하고 자기도 몸을 가졌은즉 학대 받는 자를 생각하라
Ku tuna da wadanda ke cikin kurkuku, kamar dai kuna tare da su cikin wannan hali. Kuma ku tuna da masu shan azaba kamar tare kuke cikin wannan hali
4 모든 사람은 혼인을 귀히 여기고 침소를 더럽히지 않게 하라 음행하는 자들과 간음하는 자들을 하나님이 심판하시리라
Bari kowa ya girmama aure, bari kuma a tsarkake gadon aure, gama Allah zai shar'anta fasikai da mazinata.
5 돈을 사랑치 말고 있는 바를 족한 줄로 알라 그가 친히 말씀하시기를 내가 과연 너희를 버리지 아니하고 과연 너희를 떠나지 아니하리라 하셨느니라
Bari halinku ya kubuta daga kaunar kudi. Ku dangana da abubuwan da kuke dasu, domin Allah da kansa yace, “Bazan barku ba, ba kuma zan yashe ku ba.”
6 그러므로 우리가 담대히 가로되 주는 나를 돕는 자시니 내가 무서워 아니하겠노라 사람이 내게 어찌하리요 하노라
Bari mu zama da dangana domin mu sami gabagadin cewa, “Ubangiji ne mai taimakona, ba zan ji tsoro ba. To me mutum zai iya yi mani?”
7 하나님의 말씀을 너희에게 이르고 너희를 인도하던 자들을 생각하며 저희 행실의 종말을 주의하여 보고 저희 믿음을 본받으라
Ku fa lura da wadanda ke shugabanninku, wadanda suka horar da ku cikin maganar Allah, kuma ku lura da sakamakon rayuwarsu, ku yi koyi da bangaskiyarsu.
8 예수 그리스도는 어제나 오늘이나 영원토록 동일하시니라 (aiōn g165)
Yesu Almasihu daya ne a jiya, da yau, da har abada. (aiōn g165)
9 여러 가지 다른 교훈에 끌리지 말라 마음은 은혜로써 굳게 함이 아름답고 식물로써 할 것이 아니니 식물로 말미암아 행한 자는 유익을 얻지 못하였느니라
Kada ku kauce zuwa ga bakin koyarwa daban daban, domin yana da kyau zuciya ta ginu ta wurin alheri, amma ba da dokoki game da abinci ba, wadanda basu taimaki wadanda suka kiyayesu ba.
10 우리에게 제단이 있는데 그 위에 있는 제물은 장막에서 섬기는 자들이 이 제단에서 먹을 권이 없나니
Muna da bagadin da wadanda ke hidima a cikin alfarwa basu da ikon su ci daga bisansa.
11 이는 죄를 위한 짐승의 피는 대제사장이 가지고 성소에 들어가고 그 육체는 영문 밖에서 불사름이니라
Babban firist na shiga wuri mai tsarki da jinin dabbobin da aka yanka, hadayar zunubai, amma namansu a kan kai bayan sansani a kone shi.
12 그러므로 예수도 자기 피로써 백성을 거룩케 하려고 성문 밖에서 고난을 받느니라
Domin haka Yesu shima ya sha wahala a bayan kofar birnin, domin ya tsarkake mutane ta wurin jininsa.
13 그런즉 우리는 그 능욕을 지고 영문밖으로 그에게 나아가자
Domin haka bari mu tafi gare shi a bayan sansani dauke da kunyarsa.
14 우리가 여기는 영구한 도성이 없고 오직 장차 올 것을 찾나니
Domin bamu da wani birni dawwamamme a nan. Maimako haka muna bidar birni dake zuwa.
15 이러므로 우리가 예수로 말미암아 항상 찬미의 제사를 하나님께 드리자 이는 그 이름을 증거하는 입술의 열매니라
Ta wurin sa kuma, bari kullum mu mika hadayu na yabo ga Allah, yabon kuwa shine kalmomin bakinmu da ke daukaka sunansa.
16 오직 선을 행함과 서로 나눠 주기를 잊지 말라 이같은 제사는 하나님이 기뻐하시느니라
Kada kuma mu manta da yin nagarta da kuma taimakon juna, domin Allah na farin ciki sosai da irin wadannan hadayun.
17 너희를 인도하는 자들에게 순종하고 복종하라 저희는 너희 영혼을 위하여 경성하기를 자기가 회계할 자인 것같이 하느니라 저희로 하여금 즐거움으로 이것을 하게 하고 근심으로 하게 말라 그렇지 않으면 너희에게 유익이 없느니라
Ku yi biyayya da sadaukarwa ga shugabanninku, domin suna aikin tsaro a kanku saboda rayukanku, kamar wadanda zasu bada lissafi. Kuyi biyayya gare su saboda su yi aikin lura daku cikin farin ciki, ba da bakin ciki ba, don in su yi da bakin ciki ba zai amfane ku ba.
18 우리를 위하여 기도하라 우리가 모든 일에 선하게 행하려 하므로 우리에게 선한 양심이 있는 줄을 확신하노니
Kuyi mana addu'a, domin mun tabbata muna da lamiri mai tsabta, kuma muna burin muyi rayuwar dake daidai cikin dukkan al'amura.
19 내가 더 속히 너희에게 돌아가기를 위하여 너희 기도함을 더욱 원하노라
Kuma ina karfafa ku dukka kuyi haka, domin in sami dawowa gareku da sauri.
20 양의 큰 목자이신 우리 주 예수를 영원한 언약의 피로 죽은 자 가운데서 이끌어 내신 평강의 하나님이 (aiōnios g166)
To bari Allahn salama, wanda ya tada babban makiyayin tumakin nan daga matattu, Ubangijinmu Yesu, ta wurin jinin madawwamin alkawari, (aiōnios g166)
21 모든 선한 일에 너희를 온전케 하사 자기 뜻을 행하게 하시고 그 앞에 즐거운 것을 예수 그리스도로 말미암아 우리 속에 이루시기를 원하노라 영광이 그에게 세세무궁토록 있을지어다! 아멘 (aiōn g165)
ya kammala ku da dukan abu mai kyau domin ku aikata nufinsa. Bari yayi aiki a cikinmu wanda zai gamshe shi sosai. Ta wurin Yesu Almasihu, bari daukaka ta tabbata gare shi har abada. Amin. (aiōn g165)
22 형제들아 내가 너희를 권하노니 권면의 말을 용납하라 내가 간단히 너희에게 썼느니라
'Yan'uwa, yanzu dai ina karfafa ku, da ku jurewa takaitacciyar maganar karfafawar da na rubuto maku.
23 우리 형제 디모데가 놓인 것을 너희가 알라 그가 속히 오면 내가 저와 함께 가서 너희를 보리라
Ina so ku sani an saki dan'uwan mu Timoti, tare da shi zan zo in gan ku idan ya iso da sauri.
24 너희를 인도하는 자와 및 모든 성도에게 문안하라 이달리야에서 온 자들도 너희에게 문안하느니라
Ku gaida shugabanninku dukka da kuma dukkan masu bada gaskiya. 'Yan'uwa daga can Italiya suna gaishe ku.
25 은혜가 너희 모든 사람에게 있을지어다!
Bari alheri ya kasance tare daku dukka.

< 히브리서 13 >