< 창세기 46 >

1 이스라엘이 모든 소유를 이끌고 발행하여 브엘세바에 이르러 그 아비 이삭의 하나님께 희생을 드리니
Saboda haka Isra’ila ya kama hanya da dukan abin da yake nasa, sa’ad da ya kai Beyersheba, sai ya miƙa hadayu ga Allah na Ishaku, mahaifinsa.
2 밤에 하나님이 이상중에 이스라엘에게 나타나시고 불러 가라사대 야곱아! 야곱아! 하시는지라 야곱이 가로되 `내가 여기 있나이다` 하매
Allah kuwa ya yi magana ga Isra’ila a wahayi da dare ya ce, “Yaƙub! Yaƙub!” Yaƙub kuwa ya amsa ya ce, “Ga ni.”
3 하나님이 가라사대 나는 하나님이라 네 아비의 하나님이니 애굽으로 내려가기를 두려워 말라 내가 거기서 너로 큰 민족을 이루게 하리라
Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka. Kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama zan mai da kai al’umma mai girma a can.
4 내가 너와 함께 애굽으로 내려가겠고 정녕 너를 인도하여 다시 올라올 것이며 요셉이 그 손으로 네 눈을 감기리라 하셨더라
Zan gangara zuwa Masar tare da kai, tabbatacce zan sāke dawo da kai. Kuma hannun Yusuf zai rufe idanunka.”
5 야곱이 브엘세바에서 발행할새 이스라엘의 아들들이 바로의 태우려고 보낸 수레에 자기들의 아비 야곱과 자기들의 처자들을 태웠고
Sa’an nan Yaƙub ya bar Beyersheba,’ya’yan Isra’ila maza, suka ɗauki mahaifinsu Yaƙub da’ya’yansu da matansu a cikin wagonun da Fir’auna ya aika don a kawo shi.
6 그 생축과 가나안 땅에서 얻은 재물을 이끌었으며 야곱과 그 자손들이 다 함께 애굽으로 갔더라
Suka kuma ɗauki dabbobinsu da mallakarsu, da suka samu a Kan’ana, Yaƙub kuwa da dukan zuriyarsa suka tafi Masar.
7 이와 같이 야곱이 그 아들들과 손자들과, 딸들과, 손녀들 곧 그 모든 자손을 데리고 애굽으로 갔더라
Ya ɗauki’ya’yansa maza da jikokinsa da’ya’yansa mata da jikokinsa mata, dukan zuriyarsa zuwa Masar.
8 애굽으로 내려간 이스라엘 가족의 이름이 이러하니 야곱과 그 아들들 곧 야곱의 맏아들 르우벤과
Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Isra’ila maza (Yaƙub da zuriyarsa) waɗanda suka tafi Masar, Ruben ɗan farin Yaƙub.
9 르우벤의 아들 하녹과, 발루와, 헤스론과, 갈미요
’Ya’yan Ruben maza su ne, Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.
10 시므온의 아들 곧 여무엘과, 야민과, 오핫과, 야긴과, 스할과, 가나안 여인의 소생 사울이요
’Ya’yan Simeyon maza su ne, Yemuwel, Yamin, Ohad, Yakin, Zohar da Sha’ul ɗan mutuniyar Kan’ana.
11 레위의 아들 곧 게르손과, 그핫과, 므라리요
’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.
12 유다의 아들 곧 엘과, 오난과, 셀라와, 베레스와, 세라니, 엘과 오난은 가나안 땅에서 죽었고 또 베레스의 아들 곧 헤스론과, 하물이요
’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan, Shela, Ferez da Zera (amma Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan’ana).’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.
13 잇사갈의 아들 곧 돌라와, 부와와, 욥과, 시므론이요
’Ya’yan Issakar maza su ne, Tola, Fuwa, Yoshub da Shimron.
14 스불론의 아들 곧 세렛과, 엘론과, 얄르엘이니
’Ya’yan Zebulun maza su ne, Sered, Elon da Yaleyel.
15 이들은 레아가 밧단아람에서 야곱에게 낳은 자손들이라 그 딸 디나를 합하여 남자와 여자가 삼십 삼명이며
Waɗannan su ne’ya’yan Liyatu maza da ta haifa wa Yaƙub a Faddan Aram, ban da’yarsa Dina.’Ya’yansa maza da mata duka, mutum talatin da uku ne.
16 갓의 아들 곧 시뵨과, 학기와, 수니와, 에스본과, 에리와, 아로디와, 아렐리요
’Ya’yan Gad maza su ne, Zafon, Haggi, Shuni, Ezbon, Eri, Arodi da Areli.
17 아셀의 아들 곧 임나와, 이스와와, 이스위와, 브리아와 그들의 누이 세라며 또 브리아의 아들 곧 헤벨과, 말기엘이니
’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishbi da Beriya.’Yar’uwarsu ita ce Sera.’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel.
18 이들은 라반이 그 딸 레아에게 준 실바가 야곱에게 낳은 자손들이라 합 십 륙명이요
Waɗannan su ne’ya’yan da Zilfa ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa’yarsa Liyatu.’Ya’yan duka, su sha shida ne.
19 야곱의 아내 라헬의 아들 곧 요셉과, 베냐민이요
’Ya’yan Yaƙub maza waɗanda Rahila ta haifa su ne, Yusuf da Benyamin.
20 애굽 땅에서 온 제사장 보디베라의 딸 아스낫이 요셉에게 낳은 므낫세와 에브라임이요
A Masar, Asenat’yar Fotifera, firist na On ta haifi Manasse da Efraim wa Yusuf.
21 베냐민의 아들 곧 벨라와, 베겔과, 아스벨과, 게라와, 나아만과, 에히와, 로스와, 뭅빔과, 훔빔과, 아릇이니
’Ya’yan Benyamin maza su ne, Bela, Beker, Ashbel, Gera, Na’aman, Ehi, Rosh, Muffim, Huffim da Ard.
22 이들은 라헬이 야곱에게 낳은 자손이라 합 십 사명이요
Waɗannan su ne’ya’yan Rahila maza waɗanda ta haifa wa Yaƙub, dukansu mutum goma sha huɗu ne.
23 단의 아들 후심이요
Yaron Dan shi ne, Hushim.
24 납달리의 아들 곧 야스엘과, 구니와, 예셀과, 실렘이라
’Ya’yan Naftali maza su ne, Yazeyel, Guni, Yezer da Shillem.
25 이들은 라반이 그 딸 라헬에게 준 빌하가 야곱에게 낳은 자손이니 합이 칠명이라
Waɗannan su ne’ya’ya mazan da Bilha ta haifa wa Yaƙub, ita ce Laban ya ba wa’yarsa Rahila.’Ya’yan suka su bakwai ne.
26 야곱과 함께 애굽에 이른 자는 야곱의 자부 외에 육십 륙명이니 이는 다 야곱의 몸에서 나온 자며
Dukan waɗanda suka tafi Masar tare da Yaƙub, waɗanda suke zuriyarsa kai tsaye ban da matan’ya’yansa maza, su mutum sittin da shida ne.
27 애굽에서 요셉에게 낳은 아들이 두명이니 야곱의 집 사람으로 애굽에 이른 자의 도합이 칠십명이었더라
In aka haɗa da’ya’yan nan maza guda biyu waɗanda aka haifa wa Yusuf a Masar, membobin iyalin Yaƙub, waɗanda suka tafi Masar, duka su saba’in ne.
28 야곱이 유다를 요셉에게 미리 보내어 자기를 고센으로 인도하게 하고 다 고센 땅에 이르니
To, Yaƙub ya aiki Yahuda yă yi gaba yă sadu da Yusuf, don yă nuna musu hanyar da za su bi zuwa yankin Goshen. Da suka isa yankin Goshen,
29 요셉이 수레를 갖추고 고센으로 올라가서 아비 이스라엘을 맞으며 그에게 보이고 그 목을 어긋맞겨 안고 얼마동안 울매
sai Yusuf ya kintsa keken yaƙinsa ya haura zuwa Goshen don yă taryi mahaifinsa, Isra’ila. Nan da nan da isowar Yusuf a wurin mahaifinsa, sai ya rungumi mahaifinsa, ya yi kuka na dogon lokaci.
30 이스라엘이 요셉에게 이르되 `네가 지금까지 살아 있고 내가 네 얼굴을 보았으니 지금 죽어도 가하도다'
Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Yanzu ina a shirye in mutu, da yake na gani da kaina cewa har yanzu kana da rai.”
31 요셉이 그 형들과 아비의 권속에게 이르되 내가 올라가서 바로에게 고하여 이르기를 `가나안 땅에 있던 내 형들과 내 아비의 권속이 내게로 왔는데
Sa’an nan Yusuf ya ce wa’yan’uwansa da gidan mahaifinsa, “Zan haura in yi magana da Fir’auna, zan kuwa ce masa, ‘’Yan’uwana da gidan mahaifina, waɗanda suke zaune a ƙasar Kan’ana, sun zo wurina.
32 그들은 목자라 목축으로 업을 삼으므로 그 양과 소와 모든 소유를 이끌고 왔나이다 하리니
Mutanen fa, makiyaya ne; suna kiwon dabbobi, sun kuma zo tare da garkunansu da shanunsa da kuma kome da suka mallaka.’
33 바로가 당신들을 불러서 너희의 업이 무엇이냐? 묻거든
Sa’ad da Fir’auna ya kira ku ciki, ya yi tambaya, ‘Mece ce sana’arku?’
34 당신들은 고하기를 주의 종들은 어렸을 때부터 지금까지 목축하는 자이온데 우리와 우리 선조가 다 그러하니이다 하소서 애굽 사람은 다 목축을 가증히 여기나니 당신들이 고센 땅에 거하게 되리이다`
Ku amsa, ‘Bayinka suna kiwon dabbobi ne, tun muna samari har zuwa yanzu, kamar yadda kakanninmu suka yi.’ Ta haka za a bar ku ku zauna a yankin Goshen, gama Masarawa suna ƙyamar makiyaya.”

< 창세기 46 >