< 에스겔 46 >

1 나 주 여호와가 말하노라 안 뜰 동향한 문을 일하는 육일 동안에는 닫되 안식일에는 열며 월삭에도 열고
“‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a rufe ƙofa ta fili na can cikin da take fuskantar gabas ranaku shida na aiki, amma a ranar Asabbaci da kuma a ranar ganin Sabuwar Wata a buɗe ta.
2 왕은 바깥 문 현관을 통하여 들어와서 문 벽 곁에 서고 제사장은 그를 위하여 번제와 감사제를 드릴 것이요 왕은 문통에서 경배한 후에 밖으로 나가고 그 문은 저녁까지 닫지 말 것이며
Sarki zai shiga daga waje ta shirayin hanyar shiga yă tsaya a madogarar ƙofa. Firistoci za su miƙa hadayarsa ta ƙonawa da hadayunsa na salama. Zai yi sujada a madogarar ƙofar hanyar shiga sa’an nan ya fita, amma ba za a rufe ƙofar ba sai da yamma.
3 이 땅 백성도 안식일과 월삭에 이 문통에서 나 여호와 앞에 경배할 것이며
A Asabbatai da kuma a Sabuwar Wata mutanen ƙasar za su yi sujada a gaban Ubangiji a mashigin wannan hanyar shiga.
4 안식일에 왕이 여호와께 드릴 번제는 흠 없는 어린 양 여섯과 흠없는 수양 하나라
Hadaya ta ƙonawar da sarki ya kawo wa Ubangiji a ranar Asabbaci’yan raguna shida ne da rago guda, dukansu marasa lahani.
5 그 소제는 수양 하나에는 밀가루 한 에바요 모든 어린 양에는 그 힘대로 할 것이며 밀가루 한 에바에는 기름 한 힌씩이니라
Hadayar garin da aka bayar tare da ragon efa guda ne, hadayar garin da’yan ragunan yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa.
6 월삭에는 흠 없는 수송아지 하나와 어린 양 여섯과 수양 하나를 드리되 모두 흠 없는 것으로 할 것이며
A ranar Sabuwar Wata zai miƙa ɗan bijimi,’yan raguna guda shida da kuma rago guda, dukansu marasa lahani.
7 또 소제를 갖추되 수송아지에는 밀가루 한 에바요 수양에도 밀가루 한 에바며 모든 어린 양에는 그 힘대로 할 것이요 밀가루 한 에바에는 기름 한 힌씩이며
Zai tanada a matsayin hadaya ta gari, efa guda tare da bijimi, efa guda tare da’yan raguna, da kuma’yan raguna yadda ya ga dama, tare da kwalabar mai don kowace efa.
8 왕이 올 때에는 이 문 현관을 통하여 들어오고 나갈 때에도 그리할지니라
Sa’ad da sarki zai shiga, zai shiga ta shirayin hanyar shiga, zai kuma fita ta nan.
9 그러나 모든 정한 절기에 이 땅 거민이 나 여호와 앞에 나아올 때에는 북문으로 들어와서 경배하는 자는 남문으로 나가고 남문으로 들어오는 자는 북문으로 나갈지라 들어온 문으로 도로 나가지 말고 그 몸이 앞으로 향한대로 나갈지며
“‘Sa’ad da mutanen ƙasar suka zo gaban Ubangiji a ƙayyadaddun bukukkuwa, duk wanda ya shiga ta ƙofar arewa don yă yi sujada sai ya fita ta ƙofar kudu; kuma duk wanda ya shiga ta ƙofar kudu sai ya fita ta ƙofar arewa. Ba wanda zai koma ta ƙofar da ya shiga, amma kowa zai fita a ƙofar ɗaura da wadda ya shiga.
10 왕은 무리 가운데 있어서 그들의 들어올 때에 들어오고 그들의 나갈 때에 나갈지니라
Sarki zai kasance a cikinsu, zai shiga sa’ad da suke shiga ya kuma fita sa’ad da suka fita.
11 절기와 성회 때에 그 소제는 수송아지 하나에 밀가루 한 에바요 수양 하나에도 한 에바요 모든 어린 양에는 그 힘대로 할 것이며 밀가루 한 에바에는 기름 한 힌씩이며
“‘A bukukkuwa da ƙayyadaddun bukukkuwa, hadaya ta gari zai zama efa tare da bijimi, efa da rago, da kuma’yan raguna da ya ga dama, haɗe da kwalabar mai.
12 만일 왕이 자원하여 번제를 갖추거나 혹 자원하여 감사제를 갖추어 나 여호와께 드릴 때에는 그를 위하여 동향한 문을 열고 그가 번제와 감사제를 안식일에 드림 같이 드리고 밖으로 나갈지며 나간 후에 문을 닫을지니라
Sa’ad da sarki ya ba da hadaya ta yardar rai ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa ce ko hadayun salama ne, sai a buɗe masa ƙofar da take fuskantar gabas. Zai miƙa hadayarsa ta ƙonawa ko hadayarsa ta salama yadda yakan yi a ranar Asabbaci. Sa’an nan ya fita, bayan kuma ya fita, sai a rufe ƙofar.
13 아침마다 일년 되고 흠 없는 어린 양 하나로 번제를 갖추어 나 여호와께 드리고
“‘Kullum za ku tanada ɗan rago bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji; kowace safiya za ku tanada shi.
14 또 아침마다 그것과 함께 드릴 소제를 갖추되 곧 밀가루 에바 육분지 일과 기름 힌 삼분지 일을 섞을 것이니 이는 영원한 규례를 삼아 항상 나 여호와께 드릴 소제라
Tare da shi za ku tanada hadaya ta gari kowace safiya, da ya haɗa da kashi ɗaya bisa shida na efa tare da kashi ɗaya bisa uku na mai ga garin da aka cuɗa. Miƙawar wannan hadaya ta gari ga Ubangiji dawwammamiyar farilla ce.
15 이와 같이 아침마다 그 어린 양과 밀가루와 기름을 갖추어 항상 드리는 번제를 삼을지니라
Saboda haka za a tanada ɗan rago da hadaya ta gari da kuma mai kowace safiya don hadaya ta ƙonawa ta kullum.
16 나 주 여호와가 말하노라 왕이 만일 한 아들에게 선물을 준즉 그의 기업이 되어 그 자손에게 속하나니 이는 그 기업을 이어 받음이어니와
“‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa in sarkin ya ba wa ɗaya daga cikin’ya’yansa kyauta daga gādonsa, zai kuwa zama na zuriyar; zai kuwa zama mallakarsu ta wurin gādo.
17 왕이 만일 그 기업으로 한 종에게 선물로 준즉 그 종에게 속하여 희년까지 이르고 그 후에는 왕에게로 돌아갈 것이니 왕의 기업은 그 아들이 이어 받을 것임이니라
In kuma ya ba wa ɗaya daga cikin bayinsa kyauta daga gadonsa, bawan zai iya riƙe shi sai shekarar’yantarwa; sa’an nan ya mayar wa sarkin. Gādon sarki na’ya’yansa maza ne kaɗai; na su ne.
18 왕은 백성의 기업을 취하여 그 산업에서 쫓아내지 못할지니 왕이 자기 아들에게 기업으로 줄 것은 자기 산업으로만 할 것임이니라 백성으로 각각 그 산업을 떠나 흩어지지 않게 할 것이니라
Kada sarki ya ƙwace gādon mutane, yana korinsu daga mallakarsu. Zai ba wa’ya’yansa maza gādonsu daga cikin mallakarsa, don kada a raba wani daga mutanena da mallakarsa.’”
19 그 후에 그가 나를 데리고 문곁 통행구로 말미암아 제사장의 북향한 거룩한 방에 들어가시니 그 방뒤 서편에 한 처소가 있더라
Sa’an nan mutumin ya fitar da ni ta ƙofar shiga a gefen ƙofar zuwa tsarkakakkun ɗakuna waɗanda suke fuskantar arewa, waɗanda suke na firistoci, ya kuma nuna mini wani wuri daga can ƙurewar yamma.
20 그가 내게 이르시되 이는 제사장이 속건제와 속죄제 희생을 삶으며 소제 제물을 구울 처소니 그들이 이 성물을 가지고 바깥 뜰에 나가면 백성을 거룩하게 할까 함이니라 하시고
Ya ce mini, “Wannan shi ne wurin da firistoci za su dafa hadaya don laifi, da hadaya don zunubi, a nan ne kuma za su toya hadaya ta gari, domin kada su kai su a filin da yake waje, su tsarkake mutane.”
21 나를 데리고 바깥 뜰로 나가서 나로 뜰 네 구석을 지나가게 하시는데 본즉 그 뜰 매 구석에 또 뜰이 있는데
Sa’an nan ya kawo ni filin da yake waje ya kuma bi da ni kewaye da kusurwoyi huɗunsa, na kuma ga kowace kusurwa na wani fili.
22 뜰 네 구석에 있는 그 뜰에 담이 둘렸으니 뜰의 장이 사십척이요 광이 삼십척이라 구석의 네 뜰이 한 척수며
A kusurwoyi huɗu na filin da yake waje akwai waɗansu filaye a haɗe, tsawonsu kamu arba’in fāɗinsu kuwa kamu talatin; kowane fili a kusurwoyi huɗun nan girmansu ɗaya ne.
23 그 작은 네 뜰 사면으로 돌아가며 부엌이 있고 그 사면 부엌에 삶는 기구가 설비되었었는데
Kewaye da cikin kowane filin huɗun nan akwai ginin dutse, da murhu da aka gina a kewaye a ƙarƙashin ginin.
24 그가 내게 이르시되 이는 삶는 부엌이니 전에 수종드는 자가 백성의 제물을 여기서 삶을 것이니라 하시더라
Sai ya ce mini, “Waɗannan su ne ɗakunan dahuwa inda masu hidima a haikali za su dafa hadayun da jama’a.”

< 에스겔 46 >