< 사도행전 16 >

1 바울이 더베와 루스드라에도 이르매 거기 디모데라 하는 제자가 있으니 그 모친은 믿는 유대 여자요 부친은 헬라인이라
Bulus ya kuma isa Darbe da Listira, in da akwai wani almajiri mai suna Timoti a wurin, dan wata Bayahudiya wadda ta ba da gaskiya; ubansa kuwa Baheline ne.
2 디모데는 루스드라와 이고니온에 있는 형제들에게 칭찬 받는 자니
Ana maganar kirki a kansa ta bakin 'yan'uwa da ke Listira da Ikoniyan.
3 바울이 그를 데리고 떠나고자 할 새 그 지경에 있는 유대인을 인하여 그를 데려다가 할례를 행하니 이는 그 사람들이 그의 부친은 헬라인인 줄 다 앎이러라
Bulus ya yi wa Timoti kaciya, domin yana so su yi tafiya tare, domin kuma saboda Yahudawan da ke wurin, sun san cewa ubansa Baheline ne.
4 여러 성으로 다녀 갈 때에 예루살렘에 있는 사도와 장로들의 작정한 규례를 저희에게 주어 지키게 하니
Suna shiga cikin biranen, suna yi wa iklisiyoyi gargadi da su yi biyayya da umurnan da Manzanni da dattawa suka rubuta a Urushalima.
5 이에 여러 교회가 믿음이 더 굳어지고 수가 날마다 더하니라
Bangaskiyar iklisiyoyi kuwa ta karu, ana kuma samun karuwa na wadanda suke ba da gaskiya kowace rana.
6 성령이 아시아에서 말씀을 전하지 못하게 하시거늘 브루기아와 갈라디아 땅으로 다녀가
Bulus da abokan aikin sa sun shiga cikin lardin Firigiya da Galatiya, tun da Ruhu Mai Tsarki ya hana su wa'azin kalmar a cikin yankin Asiya.
7 무시아 앞에 이르러 비두니아로 가고자 애쓰되 예수의 영이 허락지 아니하시는지라
Sun zo kusa da Misiya, da nufin shiga cikin Bitiniya, Ruhun Yesu ya hana su.
8 무시아를 지나 드로아로 내려 갔는데
Da suka ratse ta cikin Misiya, sai suka shiga birnin Taruwasa.
9 밤에 환상이 바울에게 보이니 마게도냐 사람 하나가 서서 그에게 청하여 가로되 `마게도냐로 건너와서 우리를 도우라' 하거늘
Bulus ya ga wahayi cikin dare, wani mutumin Makidoniya na kiransa, yana cewa. ''Ka zo Makidoniya ka taimake mu''.
10 바울이 이 환상을 본 후에 우리가 곧 마게도냐로 떠나기를 힘쓰니 이는 하나님이 저 사람들에게 복음을 전하라고 우리를 부르신줄로 인정함이러라
Bulus, da ganin haka, ya kama hanya zuwa Makidoniya, da tunanin Allah ne ya ke so su kai wa mutanen Makidoniya bishara.
11 드로아에서 배로 떠나 사모드라게로 직행하여 이튿날 네압볼리로 가고
Da barin Taruwasa, Bulus da kungiyarsa sun shiga jirgin ruwa zuwa Samutaraki, da gari ya waye kuma sun tafi Niyafolis;
12 거기서 빌립보에 이르니 이는 마게도냐 지경 첫성이요 또 로마의 식민지라 이 성에서 수일을 유하다가
Daga nan kuma suka tafi Filibi, birni na Makidoniya, mai muhimmanci ne a yankin Roma, in da mun yi zango kwanaki da dama.
13 안식일에 우리가 기도처가 있는가 하여 문 밖 강가에 나가 거기 앉아서 모인 여자들에게 말하더니
Ranar Asabaci mun je kofar gari, gefen rafi, da tunanin samun wurin addu'a. Mun zauna mun kuma yi magana da matan da sun taru a wurin.
14 두아디라성의 자주 장사로서 하나님을 공경하는 루디아라 하는 한 여자가 들었는데 주께서 그 마음을 열어 바울의 말을 청종하게 하신지라
Wata mace mai suna Lidiya, 'yar kasuwa ce a birnin Tiyatira, mai bautar Allah ce, ta saurare mu. Ubangiji ya bude zuciyarta, ta mai da hankali ga maganar da Bulus ke fadi.
15 저와 그 집이 다 세례를 받고 우리에게 청하여 가로되 `만일 나를 주 믿는 자로 알거든 내 집에 들어와 유하라' 하고 강권하여 있게 하니라
Sa'anda da aka yi mata Baftisma tare da mutanen gidanta, ta ce da mu, “Idan kun dauke ni mai bautar Allah, ku zo gidana ku zauna.” Sai ta rinjaye mu.
16 우리가 기도하는 곳에 가다가 점하는 귀신 들린 여종 하나를 만나니 점으로 그 주인들을 크게 이(利)하게 하는지라
A daidai wannan lokaci, muna tafiya wurin addu'a, wata yarinya mai ruhun duba ta hadu da mu. Iyayen gijinta na arziki da ita sosai.
17 바울과 우리를 좇아와서 소리 질러 가로되 `이 사람들은 지극히 높은 하나님의 종으로 구원의 길을 너희에게 전하는 자라' 하며
Tana bin Bulus, tare da mu, tana fadi da murya mai karfi cewa, ''Wadannan mutanen, bayin Allah mafi daukaka ne, suna sanar maku hanyar ceto ne''.
18 이같이 여러 날을 하는지라 바울이 심히 괴로와하여 돌이켜 그 귀신에게 이르되 `예수 그리스도의 이름으로 내가 네게 명하노니 그에게서 나오라' 하니 귀신이 즉시 나오니라
Ta dauki kwanaki tana haka. Amma Bulus ya yi fushi da ita ainun, ya juya ya umarci ruhun, ya ce, ''Na umarce ka, ka rabu da ita a cikin sunan Yesu Almasihu''. Ruhun ya yi biyayya ya rabu da ita nan take.
19 종의 주인들은 자기 이익의 소망이 끊어진 것을 보고 바울과 실라를 잡아 가지고 저자로 관원들에게 끌어 갔다가
Da iyayengijinta suka ga cewa hanyar shigar kudinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su cikin kasuwa suka kai su gaban mahunkunta.
20 상관들 앞에 데리고 가서 말하되 `이 사람들이 유대인인데 우리 성을 심히 요란케 하여
Da suka kai su Kotu, suka ce, ''Wadannan mutane Yahudawa ne, suna kawo tashin hankali a birninmu.
21 로마 사람인 우리가 받지도 못하고 행치도 못할 풍속을 전한다' 하거늘
Suna koyar da abubuwa da ba su karbuwa a gare mu, balle mu aikata, a matsayinmu na Romawa.”
22 무리가 일제히 일어나 송사하니 상관들이 옷을 찢어 벗기고 매로 치라 하여
Sai jama'a gaba daya sun tayar wa Bulus da Sila; alkalan kuma sun yage rigunansu, sun ba da umarni a duki Bulus da Sila da bulala.
23 많이 친 후에 옥에 가두고 간수에게 분부하여 `든든히 지키라' 하니
Bayan dukan, an jefa su Bulus a kurkuku, an ba mai tsaron kurkukun umurni ya kulle su da kyau, kada su gudu.
24 그가 이러한 영을 받아 저희를 깊은 옥에 가두고 그 발을 착고에 든든히 채웠더니
Shi kuma ya yi hakanan, ya sa masu sarkoki a kafafun su, kamar yadda aka umurce shi.
25 밤중쯤 되어 바울과 실라가 기도하고 하나님을 찬미하매 죄수들이 듣더라
Da tsakar dare, Bulus da Sila suna yin adu'a, su na raira wakoki ga Allah, sauran 'yan sarkar su na jin su.
26 이에 홀연히 큰 지진이 나서 옥터가 움직이고 문이 곧 다 열리며 모든 사람의 매인 것이 다 벗어진지라
Nan da nan sai ga wata girgizar kasa, wadda ta sa ginshikan kurkukun sun kadu, nan da nan kofofin kurkukun sun bude, 'yan sarka kuma, sarkokin su sun karkatse.
27 간수가 자다가 깨어 옥문들이 열린 것을 보고 죄수들이 도망한 줄 생각하고 검을 빼어 자결하려 하거늘
Mai tsaron kurkukun ya tashi daga barci ya ga kofofin kurkukun a bude, ya zaro takobi, zai kashe kan sa, a tunanin sa, 'yan sarkar sun gudu.
28 바울이 크게 소리질러 가로되 `네 몸을 상하지 말라 우리가 다 여기 있노라' 하니
Amma Bulus ya ta da murya da karfi, ya ce, ''kada kayi wa kanka barna, domin dukan mu muna nan''.
29 간수가 등불을 달라고 하며 뛰어 들어가 무서워 떨며 바울과 실라 앞에 부복하고
Mai tsaron kurkukun ya aika a kawo fitila, ya shiga ciki a gurguje da rawan jiki, ya fadi a gaban Bulus da Sila,
30 저희를 데리고 나가 가로되 `선생들아, 내가 어떻게 하여야 구원을 얻으리이까?' 하거늘
ya fitar da su waje ya ce, ''Shugabanni, me ya kamata in yi domin in tsira?''
31 가로되 `주 예수를 믿으라! 그리하면 너와 네 집이 구원을 얻으리라!' 하고
Sun ce masa, ''ka ba da gaskiya ga Yesu Ubangiji, da kai da gidan ka, za ku sami tsira''.
32 주의 말씀을 그 사람과 그 집에 있는 모든 사람에게 전하더라
Bulus da Sila suka fada masa maganar Ubangiji, tare da iyalinsa.
33 밤 그 시에 간수가 저희를 데려다가 그 맞은 자리를 씻기고 자기와 그 권속이 다 세례를 받은 후
Shi mai tsaron kurkukun ya dauke su cikin daren, ya wanke raunukansu, an kuma yi masa Baftisma nan da nan tare da iyalinsa.
34 저희를 데리고 자기 집에 올라가서 음식을 차려 주고 저와 온 집이 하나님을 믿었으므로 크게 기뻐하니라
Ya kai Bulus da Sila gidansa, ya ba su abinci. Murna ta cika gidan mai tsaron kurkukun, domin iyalin sa duka sun ba da gaskiya ga Allah.
35 날이 새매 상관들이 아전을 보내어 `이 사람들을 놓으라' 하니
Da gari ya waye, alkalai sun ba da sako a saki Bulus da Sila.
36 간수가 이 말대로 바울에게 고하되 `상관들이 사람을 보내어 너희를 놓으라 하였으니 이제는 나가서 평안히 가라' 하거늘
Mai tsaron kurkukun kuwa ya sanar wa Bulus wannan magana ta alkalan, saboda haka ya ce wa Bulus, ''Ku tafi cikin salama''.
37 바울이 이르되 `로마 사람인 우리를 죄도 정치 아니하고 공중 앞에서 때리고 옥에 가두었다가 이제는 가만히 우리를 내어 보내고자 하느냐? 아니라 저희가 친히 와서 우리를 데리고 나가야 하리라' 한대
Amma Bulus ya ce masu, “Sun yi mana duka a fili a gaban mutane mu da muke Romawa, ba a kashe mu ba, sun kuma sa mu a kurkuku; suna koran mu a asirce? Su zo da kansu su fitar da mu.
38 아전들이 이 말로 상관들에게 고하니 저희가 로마 사람이라 하는 말을 듣고 두려워하여
Masu tsaron kurkuku sun mayar da maganar Bulus ga alkalan, wanda ya sa sun firgita, da jin cewa Bulus da Sila Romawa ne.
39 와서 권하여 데리고 나가 성에서 떠나기를 청하니
Alkalai da kansu sun zo sun roki Bulus da Sila; da suka fitar da su daga kurkukun, sun ce wa Bulus da Sila su bar birnin.
40 두 사람이 옥에서 나가 루디아의 집에 들어가서 형제들을 만나 보고 위로하고 가니라
Da hakanan ne Bulus da Sila suka fita daga kurkuku, sun je gidan Lidiya. Da Bulus da Sila sun ga 'yan'uwa, sun karfafa su, sa'annan suka bar birnin.

< 사도행전 16 >