< 사도행전 13 >
1 안디옥 교회에 선지자들과 교사들이 있으니 곧 바나바와 니게르라하는 시므온과 구레네 사람 루기오와 분봉왕 헤롯의 젖동생 마나엔과 및 사울이라
A cikin iklisiyar da take Antakiya, akwai annabawa da malamai. Sune su Barnabas, Saminu (wadda ake kira Baki) da Lukiya Bakurame da Manayin (wanda aka yi renon su tare da sarki Hiridus mai mulki) da Shawulu.
2 주를 섬겨 금식할 때에 성령이 가라사대 `내가 불러 시키는 일을 위하여 바나바와 사울을 따로 세우라' 하시니
Sa'adda suke bauta wa Allah tare da azumi, sai Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku kebe mani Barnaba da Shawulu domin aikin da na kiraye su”.
3 이에 금식하며 기도하고 두 사람에게 안수하여 보내니라
Bayan taron sun yi addu'a da azumi, sai suka sa masu hannu, su suka sallame su.
4 두 사람이 성령의 보내심을 받아 실루기아에 내려가 거기서 배 타고 구브로에 가서
Sai Shawulu da Barnabas suka yi biyayya da Ruhu Mai Tsarki suka tafi Sulukiya; daga nan suka ketare zuwa tsibirin Kuburus.
5 살라미에 이르러 하나님의 말씀을 유대인의 여러 회당에서 전할새 요한을 수종자로 두었더라
Sa'adda suke garin Salami, suka koyar da maganar Ubangiji a majami'un Yahudawa, suna kuma tare da Yahaya Markus mai taimakonsu.
6 온 섬 가운데로 지나서 바보에 이르러 바예수라 하는 유대인 거짓 선지자 박수를 만나니
Bayan sun zaga tsibirin duka har Bafusa, nan suka iske wani Bayahude mai suna Bar-yeshua mai tsafi kuma annabin karya.
7 그가 총독 서기오 바울과 함께 있으니 서기오 바울은 지혜 있는 사람이라 바나바와 사울을 불러 하나님 말씀을 듣고자 하더라
Wannan mai tsafin wanda ke tare da Makaddas, shi Sarjus Bulus mutum mai basira ne. Wannan kuwa ya kira Shawulu da Barnaba domin yana so ya ji maganar Allah.
8 이 박수 엘루마는 (이 이름을 번역하면 박수라) 저희를 대적하여 총독으로 믿지 못하게 힘쓰니
Amma Elimas “mai tsafi” (fasarar sunansa kenan) ya yi adawa da su; yana so ya baudar da Makaddashin daga bangaskiya.
9 바울이라고 하는 사울이 성령이 충만하여 그를 주목하고
Amma Shawulu wanda ake ce da shi Bulus yana cike da Ruhu Mai Tsarki ya kafa masa ido.
10 가로되 `모든 궤계와 악행이 가득한 자요, 마귀의 자식이요, 모든 의의 원수여, 주의 바른 길을 굽게 하기를 그치지 아니하겠느냐?
Sai ya ce, “Kai dan iblis, kana cike da kowace irin yaudara da mugunta. Kai abokin gabar kowanne irin adalci ne. Ba za ka daina karkata mikakkakun hanyoyin Ubangiji ba?
11 보라, 이제 주의 손이 네 위에 있으니 네가 소경이 되어 얼마 동안 해를 보지 못하리라' 하니 즉시 안개와 어두움이 그를 덮어 인도할 사람을 두루 구하는지라
Yanzu ga hannun Ubangiji bisa kanka, zaka zama makaho. Ba za ka ga rana ba nan da dan lokaci.” Nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi ya fara yawo yana neman mutane su yi masa jagora.
12 이에 총독이 그렇게 된 것을 보고 믿으며 주의 가르치심을 기이히 여기니라
Bayan da Makaddashin ya ga abin da ya faru ya ba da gaskiya saboda ya yi mamakin koyarwa game da Ubangiji.
13 바울과 및 동행하는 사람들이 바보에서 배 타고 밤빌리아에 있는 버가에 이르니 요한은 저희에게서 떠나 예루살렘으로 돌아가고
Bulus da abokansa suka shirya suka ketare a jirgin ruwa daga Bafusa zuwa Firjiya a Bamfiliya. Amma Yahaya ya bar su ya koma Urushalima.
14 저희는 버가로부터 지나 비시디아 안디옥에 이르러 안식일에 회당에 들어가 앉으니라
Bulus da abokansa suka tafi daga Firjiya zuwa Antakiya na kasar Bisidiya. Nan suka shiga majami'a ran Asabaci suka zauna.
15 율법과 선지자의 글을 읽은 후에 회당장들이 사람을 보내어 물어 가로되 `형제들아, 만일 백성을 권할 말이 있거든 말하라' 하니
Bayan karatun dokoki da annabawa, shugabanin iklisiyar suka tura sako cewa, “'Yan'uwa, idan kuna da wani sakon karfafawa ga jama'a ku fadi.”
16 바울이 일어나 손짓하며 말하되 `이스라엘 사람들과 및 하나님을 경외하는 사람들아 들으라!
Bulus kuwa ya tashi ya yi alama da hannunsa ya ce, “Mutanen Isra'ila da ku wadanda kuke girmama Allah, ku ji.
17 이 이스라엘 백성의 하나님이 우리 조상들을 택하시고 애굽 땅에서 나그네 된 그 백성을 높여 큰 권능으로 인도하여 내사
Allahn Isar'ila ya zabi kakkaninmu ya kuma ribabbanya su sa'adda suke kasar Masar da kuma madaukakin iko ya fito da su daga cikinta.
18 광야에서 약 사십 년간 저희 소행을 참으시고
Ya yi hakuri da su a jeji har na tsawon shekara arba'in.
19 가나안 땅 일곱 족속을 멸하사 그 땅을 기업으로 주시고 (약 사백 오십 년간)
Bayan ya hallaka kasashe bakwai a kasar Kan'ana, ya ba kakkaninmu kasar nan gado.
20 그 후에 선지자 사무엘 때까지 사사를 주셨더니
Duk wadanan abubuwan sun faru shekaru dari hudu da hamsin da suka wuce. Bayan wadannan, Allah ya ba su alkalai har sai da annabi Sama'ila ya zo.
21 그 후에 저희가 왕을 구하거늘 하나님이 베냐민 지파 사람 기스의 아들 사울을 사십 년간 주셨다가
Sai jama'a suka roka a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Saul dan Kish, mutumin kabilar Binyamin ya zama sarki har na tsawon shekara arba'in.
22 폐하시고 다윗을 왕으로 세우시고 증거하여 가라사대 내가 이새의 아들 다윗을 만나니 내 마음에 합한 사람이라 내 뜻을 다 이루게 하리라 하시더니
Allah kuwa ya cire shi daga kan kujerar sarauta, ya daga Dauda ya zama sarkinsu. A kan Dauda ne Allah ya ce, 'Na sami Dauda dan Yessi, mutumin da zuciyata ke so; zai yi duk abin da nake so'.
23 하나님이 약속하신 대로 이 사람의 씨에서 이스라엘을 위하여 구주를 세우셨으니 곧 예수라
Daga zuriyar mutumin nan Allah ya fito da mai ceto, Yesu, kamar yadda aka alkawarta zai yi.
24 그 오시는 앞에 요한이 먼저 회개의 세례를 이스라엘 모든 백성에게 전파하니라
Wannan ya faru kafin Yesu ya zo, Yahaya ya yi shelar baftimar tuba ga jamma'ar Isra'ila.
25 요한이 그 달려 갈 길을 마칠 때에 말하되 너희가 나를 누구로 생각하느냐? 나는 그리스도가 아니라 내 뒤에 오시는 이가 있으니 나는 그 발의 신 풀기도 감당치 못하리라 하였으니
Sa'adda Yahaya ya gama aikin sa, sai ya ce, 'Wanene ni a tsamanin ku? Ba nine shi ba. Amma ku saurara, akwai wani mai zuwa bayana wanda maballin takalminsa ban isa in kwance ba.'
26 형제들 아브라함의 후예와 너희 중 하나님을 경외하는 사람들아! 이 구원의 말씀을 우리에게 보내셨거늘
Yan'uwa 'ya'ya daga zuriyar Ibrahim, da wadanda ke bautar Allah a cikinku, saboda mune aka turo sakon ceto.
27 예루살렘에 사는 자들과 저희 관원들이 예수와 및 안식일마다 외우는 바 선지자들의 말을 알지 못하므로 예수를 정죄하여 선지자들의 말을 응하게 하였도다
Saboda wadanda ke zaune cikin Urushalima, da masu mulkinsu, ba su gane shi ba, kuma sun cika fadin annabawa da a ke karantawa kowace ranar Asabaci ta wurin kashe shi.
28 죽일 죄를 하나도 찾지 못하였으나 빌라도에게 죽여 달라 하였으니
Duk da cewa ba su sami dalilin mutuwa a kansa ba, suka roki Bilatus ya kashe shi.
29 성경에 저를 가리켜 기록한 말씀을 다 응하게 한 것이라 후에 나무에서 내려다가 무덤에 두었으나
Bayan sun gama duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka sauke shi daga giciye suka sa shi a cikin kabari.
30 하나님이 죽은 자 가운데서 저를 살리신지라
Amma Allah ya tashe shi daga matattu.
31 갈릴리로부터 예루살렘에 함께 올라간 사람들에게 여러 날 보이셨으니 저희가 이제 백성 앞에 그의 증인이라
Mutanen da suka zo tare da shi daga Galili da Urushalima kuwa suka yi ta ganinsa har kwanaki da yawa. Wadanan mutane kuma sune shaidunsa ga jama'a a yanzu.
32 우리도 조상들에게 주신 약속을 너희에게 전파하노니
Mun kawo maku labari mai dadi game da alkawaran da aka yi wa kakkaninmu.
33 곧 하나님이 예수를 일으키사 우리 자녀들에게 이 약속을 이루게 하셨다 함이라 시편 둘째 편에 기록한 바와 같이 너는 내 아들이라 오늘 너를 낳았다 하셨고
Ubangiji ya bar mana alkawaran. Don haka ya ta da Yesu daga matattu. Kamar yadda ya ke a littafin zabura ta biyu: ''Kai da na ne yau na zama mahaifinka.''
34 또 하나님께서 죽은 자 가운데서 저를 일으키사 다시 썩음을 당하지 않게 하실 것을 가르쳐 가라사대 내가 다윗의 거룩하고 미쁜 은사를 너희에게 주리라 하셨으니
Kuma dalilin tayar da shi daga matattu shine saboda kada jikinsa ya rube, ya yi magana kamar haka: ''Zan baku albarkun Dauda masu tsarki tabatattu.''
35 그러므로 또 다른 편에 일렀으되 주의 거룩한 자로 썩음을 당하지 않게 하시리라 하셨느니라
Wannan shine dalilin da ya yi magana kuma a wata Zabura, 'Ba za ka bar Mai Tsarkinka ya rube ba.'
36 다윗은 당시에 하나님의 뜻을 좇아 섬기다가 잠들어 그 조상들과 함께 묻혀 썩음을 당하였으되
Bayan Dawuda ya yi wa Allah bauta a cikin zuciyarsa da kuma abin da Allah yake so, ya mutu, aka binne shi tare da kakkaninsa, ya kuma ruba,
37 하나님의 살리신 이는 썩음을 당하지 아니하였나니
amma wanda Allah ya tayar bai ga ruba ba.
38 그러므로 형제들아 너희가 알것은 이 사람을 힘입어 죄 사함을 너희에게 전하는 이것이며
'Yan'uwa, ku sani cewa ta wurin mutumin nan aka yi maku wa'azin gafarar zunubai.
39 또 모세의 율법으로 너희가 의롭다 하심을 얻지 못하던 모든 일에도 이 사람을 힘입어 믿는 자마다 의롭다 하심을 얻는 이것이라
Ta wurinsa ne duk wanda ya ba da gaskiya zai kubuta daga dukan abin da dokar Musa bata 'yantar da ku a kai ba.
40 그런즉 너희는 선지자들로 말씀하신 것이 너희에게 미칠까 삼가라
Saboda haka ku yi hankali da abubuwan da annabawa suka fada kada su faru a kanku:
41 일렀으되 보라, 멸시하는 사람들아 너희는 놀라고 망하라 내가 너희 때를 당하여 한 일을 행할 것이니 사람이 너희에게 이를지라도 도무지 믿지 못할 일이라 하였느니라' 하니라
'Ku masu reni, za ku rude don mamaki, ku kuma shude; saboda ina aiki a cikin kwananakinku, aikin da ba za ku yarda ba ko da wani ya gaya maku.”
42 저희가 나갈새 사람들이 청하되 다음 안식일에도 이 말씀을 하라 하더라
Da Bulus da Barnaba suna fita kenan, sai jama'a suka rokesu, su sake yin irin wannan magana ranar Assabaci mai zuwa.
43 폐회한 후에 유대인과 유대교에 입교한 경건한 사람들이 많이 바울과 바나바를 좇으니 두 사도가 더불어 말하고 항상 하나님의 은혜 가운데 있으라 권하니라
Bayan da sujadar ta kare, Yahudawa da yawa da kuma wadanda suka shiga addinin Yahudanci suka bi Bulus da Barnaba, sai suka gargade su da su cigaba da aikin alherin Allah.
44 그 다음 안식일에는 온 성이 거의 다 하나님 말씀을 듣고자 하여 모이니
Da Asabaci ta kewayo, kusan dukan garin suka taru domin su ji maganar Ubangiji.
45 유대인들이 그 무리를 보고 시기가 가득하여 바울의 말한 것을 변박하고 비방하거늘
Sa'adda Yahudawa suka ga taron jama'a, sai suka cika da kishi suna karyata abubuwan da Bulus ya fada suka kuma aibata shi.
46 바울과 바나바가 담대히 말하여 가로되 `하나님의 말씀을 마땅히 먼저 너희에게 전할 것이로되 너희가 버리고 영생 얻음에 합당치 않은 자로 자처하기로 우리가 이방인에게로 향하노라 (aiōnios )
Amma Bulus da Barnaba sun yi magana gabagadi suka ce, “Dole ne a fara fada maku maganar Allah. Amma da yake kun ture ta, kun nuna baku cancanci rai madawwami ba soboda haka zamu juya ga al'ummai. (aiōnios )
47 주께서 이같이 우리를 명하시되 내가 너를 이방의 빛을 삼아 너로 땅 끝까지 구원하게 하리라 하셨느니라' 하니
Don haka Ubangiji ya umarce mu, cewa, 'Na sa ku haske ga al'ummai, saboda ku kawo ceto ga iyakar duniya.'”
48 이방인들이 듣고 기뻐하여 하나님의 말씀을 찬송하며 영생을 주시기로 작정된 자는 다 믿더라 (aiōnios )
Da al'ummai suka ji haka, sai suka yi murna suka kuma yabi kalmar Ubangiji. Dukan wadanda aka kaddarawa samin rai madawwami suka tuba. (aiōnios )
Kalmar Ubangiji kuwa ta bazu a kowanne bangaren yankin.
50 이에 유대인들이 경건한 귀부인들과 그 성내 유력자들을 선동하여 바울과 바나바를 핍박케 하여 그 지경에서 쫓아내니
Amma Yahudawan suka zuga wadansu mata masu sujada, masu daraja da kuma shugabannin mazan garin. Wannan ya tayar da tsanani ga Bulus da Barnaba har suka fitar da su daga iyakar garinsu.
51 두 사람이 저희를 향하여 발에 티끌을 떨어 버리고 이고니온으로 가거늘
Amma Bulus da Barnaba suka kade masu kurar kafarsu. Suka tafi garin Ikoniya.
Amma almajiran suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.