< 베드로후서 2 >

1 그러나 민간에 또한 거짓 선지자들이 일어났었나니 이와 같이 너희 중에도 거짓 선생들이 있으리라 저희는 멸망케 할 이단을 가만히 끌어들여 자기들을 사신 주를 부인하고 임박한 멸망을 스스로 취하는 자들이라
Annabawan karya sun zo ga mutane, hakannan kuma malaman karya suma sun zo. A asirce za su zo maku da karkatacciyar koyarwa mai hallakarwa, su kuma yi musun sanin Ubangiji da ya fanshe su. Su na jawowa kansu hallaka da sauri.
2 여럿이 저희 호색하는 것을 좇으리니 이로 인하여 진리의 도가 훼방을 받을 것이요
Da yawa za su bi gurbinsu, kuma ta wurinsu za a sabawa sahihiyar gaskiya.
3 저희가 탐심을 인하여 지은 말을 가지고 너희로 이를 삼으니 저희 심판은 옛적부터 지체하지 아니하며 저희 멸망은 자지 아니하느니라
Ta wurin hadama za su ribace ku ta wurin maganganunsu na yaudara. Hallakarsu ba za ta yi jinkiri ba; hukuncinsu na nan tafe.
4 하나님이 범죄한 천사들을 용서치 아니하시고 지옥에 던져 어두운 구덩이에 두어 심판 때까지 지키게 하셨으며 (Tartaroō g5020)
Allah bai kebe mala'ikkun da suka yi zunubi ba. Maimakon haka ya tura su a cikin bakin duhun jahannama daure da sarkoki, har ya zuwa ranar shari'a. (Tartaroō g5020)
5 옛 세상을 용서치 아니하시고 오직 의를 전파하는 노아와 그 일곱 식구를 보존하시고 경건치 아니한 자들의 세상에 홍수를 내리셨으며
Hakan nan kuma bai kebe duniya ta zamanin da ba. Maimakon haka, ya kebe Nuhu, wanda yake wa'azin adalci, tare da mutane bakwai, lokacin da ya kawo ambaliyar ruwan Tsufana a fuskar duniyar marasa bin Allah.
6 소돔과 고모라 성을 멸망하기로 정하여 재가 되게 하사 후세에 경건치 아니할 자들에게 본을 삼으셨으며
Sa'annan Allah ya kone biranen Sadoma da Gomrata da wuta ya maishe su toka, wannan ya zama misalin abin da zai faru da marasa ibada.
7 무법한 자의 음란한 행실을 인하여 고통하는 의로운 롯을 건지셨으니
Amma ga adalinnan Lutu, wanda ya zaku a ransa ta wurin miyagun halayen mutanen, Ubangiji kuwa ya cece shi.
8 (이 의인이 저희 중에 거하여 날마다 저 불법한 행실을 보고 들음으로 그 의로운 심령을 상하니라)
Ga wannan mutum mai adalci, wanda yayi zama a cikinsu kowace rana ransa na baci, domin abin da yake gani yake kuma ji.
9 주께서 경건한 자는 시험에서 건지시고 불의한 자는 형벌 아래 두어 심판 날까지 지키시며
Saboda haka Allah ya san yadda zai ceci masu adalci daga gwaji, da yadda kuma zai kama masu rashin adalci da hukunci a ranar shari'a.
10 육체를 따라 더러운 정욕 가운데서 행하며 주관하는 이를 멸시하는 자들에게 특별히 형벌하실 줄을 아시느니라 이들은 담대하고 고집하여 떨지 않고 영광 있는 자를 훼방하거니와
Wannan kuwa musamman gaskiya ce ga wadanda suka ci gaba da ayyuka na jiki suka kuma raina masu mulki. Suna da taurin kai da kuma yin ganin dama. Ba sa tsoron sabo ga wadanda aka daukaka.
11 더 큰 힘과 능력을 가진 천사들이라도 주 앞에서 저희를 거스려 훼방하는 송사를 하지 아니하느니라
Ko da shike mala'iku suna da karfi da iko fiye da su, amma basu kawo karar batanci a kansu a gaban Ubangiji ba.
12 그러나 이 사람들은 본래 잡혀 죽기 위하여 난 이성 없는 짐승 같아서 그 알지 못한 것을 훼방하고 저희 멸망 가운데서 멸망을 당하며
Amma wadannan dabbobi marassa tunani an yi su ne musamman domin a kama a yanka. Suna sabawa abin da ba su sani ba. Zasu halaka.
13 불의의 값으로 불의를 당하며 낮에 연락을 기쁘게 여기는 자들이니 점과 흠이라 너희와 함께 연회할 때에 저희 간사한 가운데 연락하며
Za su sami sakamakon mugun aikinsu. Suna tunanin yin nishadi da rana abin annashuwa ne. Su kan su tababbu ne. Suna jin dadin ayyukansu na yaudara yayin da suke liyafa tare da ku.
14 음심이 가득한 눈을 가지고 범죄하기를 쉬지 아니하고 굳세지 못한 영혼들을 유혹하며 탐욕에 연단된 마음을 가진 자들이니 저주의 자식이라
Suna da idanun sha'awace sha'awacen mata mazinata; ba sa koshi da aikata zunubi. Suna rinjayar wandanda ba su da tsayayyan hankali zuwa ga munanan ayyuka, kuma sun kafa zukatansu ga hadama, su 'ya'yan la'ana ne!
15 저희가 바른 길을 떠나 미혹하여 브올의 아들 발람의 길을 좇는도다 그는 불의의 삯을 사랑하다가
Sun bar bin hanyar gaskiya. Sun bijire kuma sun bi hanyar Bal'amu dan Be'or wanda yake kaunar ribar rashin adalci.
16 자기의 불법을 인하여 책망을 받되 말 못하는 나귀가 사람의 소리로 말하여 이 선지자의 미친 것을 금지하였느니라
Amma ya karbi tsautawa domin zunubinsa. Jaki ma da baya magana ya tsauta wa haukan annabin da muryar dan adam.
17 이 사람들은 물 없는 샘이요 광풍에 밀려 가는 안개니 저희를 위하여 캄캄한 어두움이 예비되어 있나니
Wadannan mutane suna kamar mabulbullai da babu ruwa. suna nan kamar gizagizai da iska ke korawa. Duhu mai tsanani yana jiransu.
18 저희가 허탄한 자랑의 말을 토하여 미혹한 데 행하는 사람들에게서 겨우 피한 자들을 음란으로써 육체의 정욕 중에서 유혹하여
Su masu babatu ne da girman kai. suna yadaurar mutane ta wurin sha'awowin jiki. Suna yaudarar mutane da suke kokarin su tsere daga wadanda suke rayuwa cikin kuskure.
19 저희에게 자유를 준다 하여도 자기는 멸망의 종들이니 누구든지 진 자는 이긴 자의 종이 됨이니라
Suna masu alkawarin yanci, amma su da kan su bayi ne ga zunubi. Domin mutum bawa ne ga duk abinda ya rinjaye shi.
20 만일 저희가 우리 주 되신 구주 예수 그리스도를 앎으로 세상의 더러움을 피한 후에 다시 그 중에 얽매이고 지면 그 나중 형편이 처음보다 더 심하리니
Duk wanda ya kubuta daga shashanci na duniya ta wurin sanin Ubangiji da mai Ceto Yesu Almasihu, sa'annan ya koma cikin shashaci, yanayinsu na karshe ya zama da muni fiye da na farkon.
21 의의 도를 안 후에 받은 거룩한 명령을 저버리는 것보다 알지 못하는 것이 도리어 저희에게 나으니라
Da ma zai fi masu kada su san hanyar adalci da su san ta amma sa'annan su juya daga ka'ida mai tsarki wanda aka damka masu.
22 참 속담에 이르기를 개가 그 토하였던 것에 돌아가고 돼지가 씻었다가 더러운 구덩이에 도로 누웠다 하는 말이 저희에게 응하였도다
Wannan karin magana ya zama gaskiya a kan su: “Kare ya dawo yana lashe amansa. Aladen da akayi masa wanka ya koma cikin tabo.”

< 베드로후서 2 >