< 고린도후서 11 >
1 원컨대 너희는 나의 좀 어리석은 것을 용납하라 청컨대 나를 용납하라
Ina fatan za ku jure da ni cikin wauta kadan. Ko da yake lallai kuna jurewa da ni!
2 내가 하나님의 열심으로 너희를 위하여 열심 내노니 내가 너희를 정결한 처녀로 한 남편인 그리스도께 드리려고 중매함이로다
Domin ina kishi sabili da ku. Kishi na kuwa irin na Allah ne domin ku. Tun da na alkawartar da ku a cikin aure ga miji daya. Na kuma yi alkawarin in gabatar da ku kamar budurwa mai tsarki ga Almasihu.
3 뱀이 그 간계로 이와를 미혹케 한 것같이 너희 마음이 그리스도를 향하는 진실함과 깨끗함에서 떠나 부패할까 두려워하노라
Gama ina fargaba a kan ku, ko watakila, kamar yadda macijin ya yaudari Hauwa'u ta wurin kissarsa, Ya zamana tunaninku ya kauce daga sahihiyar sadaukarwa ga Almasihu.
4 만일 누가 가서 우리의 전파하지 아니한 다른 예수를 전파하거나 혹 너희의 받지 아니한 다른 영을 받게 하거나 혹 너희의 받지 아니한 다른 복음을 받게할 때에는 너희가 잘 용납하는구나
Anar misali idan wani ya zo ya kawo shelar wani Yesu daban da wanda muka yi maku wa'azinsa. Ko kuma kun karbi wani ruhu daban da wanda muka karba. Ko kuma kun karbi wata bishara daban da wadda muka karba. Amincewar da kuka yi wa wadannan abubuwa ta isa!
5 내가 지극히 큰 사도들보다 부족한 것이 조금도 없는 줄 생각하노라
Don kuwa ina tsammanin ba a baya nake ba ga sauran wadanda ake kira manyan manzanni.
6 내가 비록 말에는 졸(拙)하나 지식에는 그렇지 아니하니 이것을 우리가 모든 사람 가운데서 모든 일로 너희에게 나타내었노라
To ko ma ba a ilimantar da ni ba akan yin jawabi, ban rasa horarwar ilimi ba. Ta kowace hanya kuma cikin abubuwa duka mun sanar da ku wannan.
7 내가 너희를 높이려고 나를 낮추어 하나님의 복음을 값 없이 너희에게 전함으로 죄를 지었느냐
Na yi zunubi ne da na kaskantar da kai na domin a daukaka ku? Domin na yi maku wa'azin bisharar Allah kyauta.
8 내가 너희를 섬기기 위하여 다른 여러 교회에서 요(料)를 받은 것이 탈취한 것이라
Na yi wa sauran Ikilisiyoyi kwace ta wurin karbar gudummuwa daga wurin su domin inyi maku hidima.
9 또 내가 너희에게 있어 용도가 부족하되 아무에게도 누를 끼치지 아니함은 마게도냐에서 온 형제들이 나의 부족한 것을 보충하였음이라 내가 모든 일에 너희에게 폐를 끼치지 않기 위하여 스스로 조심하였거니와 또 조심하리라
Lokacin da ina tare da ku kuma na sami kai na cikin bukata, ban dora wa kowa nauyi ba. Domin 'yan'uwa da suka zo daga Makidoniya sun biya bukatuna. A cikin komai na kebe kaina daga zama nawaya a gare ku, kuma zan cigaba da yin haka.
10 그리스도의 진리가 내 속에 있으니 아가야 지방에서 나의 이 자랑이 막히지 아니하리라
Kamar yadda gaskiyar Almasihu ke ciki na, ba zan yi shiru da wannan fahariya tawa ba a cikin dukan kasar Akaya.
11 어떠한 연고뇨 내가 너희를 사랑하지 아니함이냐 하나님이 아시느니라
Don me? Saboda ba na kaunar ku? Allah ya sani.
12 내가 하는 것을 또 하리니 기회를 찾는 자들의 그 기회를 끊어 저희로 하여금 그 자랑하는 일에 대하여 우리와 같이 되게 하려 함이로라
Amma abinda na ke yi, zan cigaba da yi. Zan yi haka ne domin in yanke zarafin wadanda ke son samun zarafi kamar mu akan abubuwan da suke fahariya da shi.
13 저런 사람들은 거짓 사도요 궤휼의 역군(役軍)이니 자기를 그리스도의 사도로 가장하는 자들이니라
Don irin wadannan mutane manzannin karya ne masu aikin yaudara. Suna badda kama kamar manzannin Almasihu.
14 이것이 이상한 일이 아니라 사단도 자기를 광명의 천사로 가장하나니
Wannan ba abin mamaki ba ne, domin shaidan ma yakan badda kama ya fito kamar mala'ikan haske.
15 그러므로 사단의 일군들도 자기를 의의 일군으로 가장하는 것이 또한 큰 일이 아니라 저희의 결국은 그 행위대로 되리라
Ba wani babban abin mamaki ba ne idan bayin sa sun badda kamanninsu don a dauka bayin adalci ne su. Karshen su zai zama sakamakon abin da suka aikata.
16 내가 다시 말하노니 누구든지 나를 어리석은 자로 여기지 말라 만일 그러하더라도 나로 조금 자랑하게 어리석은 자로 받으라
Ina kara fadi: Kada wani ya yi zaton ni wawa ne. Idan kun yi zaton hakan, to ku dauke ni kamar wawan don inyi fahariya kadan.
17 내가 말하는 것은 주를 따라 하는 말이 아니요 오직 어리석은 자와 같이 기탄 없이 자랑하노라
Abinda nake fadi game da wannan gabagadi mai fahariya ba bisa ga amincewar Ubangiji ba ne, amma ina magana a matsayin wawa.
18 여러 사람이 육체를 따라 자랑하니 나도 자랑하겠노라
Tun da mutane dayawa suna fahariya bisa ga jiki, ni ma zan yi fahariya.
19 너희는 지혜로운 자로서 어리석은 자들을 기쁘게 용납하는구나
Gama kuna murnar tarayya da wawaye. Ku masu hikima ne!
20 누가 너희로 종을 삼거나 잡아 먹거나 사로잡거나 자고하다 하거나 뺨을 칠지라도 너희가 용납하는도다
Kuma kuna hakuri da wanda zai bautar da ku, idan ya tauye ku, yana amfani da ku don ribar kansa, idan ya dauki kansa fiye da ku, ko ya mammare ku a fuska.
21 우리가 약한 것같이 내가 욕되게 말하노라 그러나 누가 무슨 일에 담대하면 어리석은 말이나마 나도 담대하리라
Ina mai cewa mun kunyata da muka rasa gabagadin yi maku haka. Duk da haka idan wani zai yi fahariya-Ina magana kamar wawa-Ni ma zan yi fahariya.
22 저희가 히브리인이냐 나도 그러하며 저희가 이스라엘인이냐? 나도 그러하며 저희가 아브라함의 씨냐? 나도 그러하며
Su yahudawa ne? Ni ma haka. Su Isra'ilawa ne? Nima haka. Su zuriyar Ibrahim ne? Nima haka.
23 저희가 그리스도의 일군이냐 정신 없는 말을 하거니와 나도 더욱 그러하도다 내가 수고를 넘치도록 하고 옥에 갇히기도 더 많이 하고, 매도 수없이 맞고, 여러 번 죽을 뻔하였으니
Su bayin Almasihu ne? (Ina magana kamar ba ni cikin hankalina) na fi su ma. Na ma yi aiki tukuru fiye da su duka, shiga kurkuku fiye da kowa, a shan duka babu misali, a fuskantar haduran mutuwa da yawa.
24 유대인들에게 사십에 하나 감한 매를 다섯 번 맞았으며
Daga hannun yahudawa sau biyar na sha bulala ''Arba'in ba daya''.
25 세 번 태장으로 맞고 한 번 돌로 맞고 세 번 파선하는데 일주야를 깊음에서 지냈으며
Sau uku na sha dibga da sanduna. Sau daya aka jejjefe ni da duwatsu. Sau uku na yi hadari a jirgin ruwa. Na yi tsawon dare da yini guda a tsakiyar teku.
26 여러 번 여행에 강의 위험과, 강도의 위험과, 동족의 위험과, 이방인의 위험과, 시내의 위험과, 광야의 위험과, 바다의 위험과, 거짓 형제 중의 위험을 당하고
Ina shan tafiye tafiye, cikin hadarin koguna, cikin hadarin 'yan fashi, cikin hadari daga mutane na, cikin hadari daga al'ummai, cikin hadarin birni, cikin hadarin jeji, cikin hadarin teku, cikin hadarin 'yan'uwan karya.
27 또 수고하며 애쓰고 여러 번 자지 못하고 주리며 목마르고 여러번 굶고 춥고 헐벗었노라
Na sami kaina ina aiki tukuru cikin mawuyacin hali, cikin yin dare dayawa ba barci, cikin yunwa da kishin ruwa, cikin yawan azumi, cikin sanyi da tsiraici.
28 이 외의 일은 고사하고 오히려 날마다 내 속에 눌리는 일이 있으니 곧 모든 교회를 위하여 염려하는 것이라
Baya ga wadannan duka, akwai nauyi a kaina kullayaumin saboda damuwata akan Ikkilisiyoyi duka.
29 누가 약하면 내가 약하지 아니하며 누가 실족하게 되면 내가 애타하지 않더냐
Waye kumama, wanda ban zama kumama akan shi ba? Wanene aka sa yayi tuntube, kuma ban kuna ba?
30 내가 부득불 자랑할진대 나의 약한 것을 자랑하리라!
Idan zan yi fahariya, zan yi fahariya akan abinda ke nuna kasawata.
31 주 예수의 아버지 영원히 찬송할 하나님이 나의 거짓말 아니하는 줄을 아시느니라 (aiōn )
Allah kuma Uba na Ubangijinmu Yesu, wanda ya isa yabo har abada, ya san ba karya nake yi ba! (aiōn )
32 다메섹에서 아레다 왕의 방백이 나를 잡으려고 다메섹 성을 지킬새
A Damasku, gwamnan da ke mulki karkashin sarki Aritas yasa aka yi tsaron birnin Damasku domin a kama ni.
33 내가 광주리를 타고 들창문으로 성벽을 내려가 그 손에서 벗어났노라
Amma ta taga cikin kwando aka ziraro ni bayan ganuwar birni, na kuwa kucce daga hannunsa.