< 역대하 11 >
1 르호보암이 예루살렘에 이르러 유다와 베냐민 족속을 모으니 택한 용사가 십 팔만이라 이스라엘과 싸워 나라를 회복하여 르호보암에게 돌리려 하더니
Sa’ad da Rehobowam ya iso Urushalima, ya tattara mayaƙa dubu ɗari takwas daga gidan Yahuda da Benyamin, don su yi yaƙi da Isra’ila su sāke mai da mulki wa Rehobowam.
2 여호와의 말씀이 하나님의 사람 스마야에게 임하여 가라사대
Amma wannan maganar Ubangiji ta zo ga Shemahiya mutumin Allah.
3 솔로몬의 아들 유다 왕 르호보암과 유다와 베냐민의 이스라엘 무리에게 고하여 이르기를
“Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon sarkin Yahuda da kuma dukan Isra’ilawan da suke a Yahuda da Benyamin,
4 여호와의 말씀이 너희는 올라 가지 말라 너희 형제와 싸우지 말고 각기 집으로 돌아가라 이 일이 내게로 말미암아 난 것이라 하셨다 하라 하신지라 저희가 여호와의 말씀을 듣고 돌아가고 여로보암을 치러 가지 아니하였더라
‘Ga abin da Ubangiji ya ce kada ku haura don ku yi yaƙi da’yan’uwanku. Ku tafi gida kowannenku, gama wannan yi na ne.’” Saboda haka suka yi biyayya ga maganar Ubangiji suka kuma koma daga takawa don yaƙi da Yerobowam.
5 르호보암이 예루살렘에 거하여 유다 땅에 방비하는 성읍들을 건축하였으니
Rehobowam ya zauna a Urushalima ya kuma gina garuruwa don kāriya a cikin Yahuda.
10 소라와, 아얄론과, 헤브론이니 다 유다와 베냐민 땅에 있어 견고한 성읍이라
Zora, Aiyalon da Hebron. Waɗannan su ne garuruwan katanga a cikin Yahuda da Benyamin.
11 르호보암이 이 모든 성읍을 더욱 견고케 하고 장관을 그 가운데 두고 양식과 기름과 포도주를 저축하고
Ya ƙarfafa kāriyarsu ya kuma sa shugabannin mayaƙa a cikinsu, tare da tanadin abinci, man zaitun da kuma ruwan inabi.
12 각 성읍에 방패와 창을 두어 심히 강하게 하니라 유다와 베냐민이 르호보암에게 속하였더라
Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen, ya kuma sa suka zama da ƙarfi. Saboda haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa.
13 온 이스라엘의 제사장과 레위 사람이 그 모든 지방에서부터 르호보암에게 돌아오되
Firistoci da Lawiyawa daga dukan yankuna ko’ina a Isra’ila suka haɗa kai da shi.
14 레위 사람이 그 향리와 산업을 떠나 유다와 예루살렘에 이르렀으니 이는 여로보암과 그 아들들이 저희를 폐하여 여호와께 제사장의 직분을 행치 못하게 하고
Lawiyawa suka ma bar makiyayansu da mallakarsu, suka zo Yahuda da Urushalima domin Yerobowam da’ya’yansa maza sun ƙi su a matsayin firistocin Ubangiji.
15 여로보암이 여러 산당과 수염소 우상과 자기가 만든 송아지 우상을 위하여 스스로 제사장들을 세움이라
Yerobowam ya naɗa firistocinsa domin masujadan kan tudu da kuma domin gumakan nan na akuya da maraƙin da ya yi.
16 이스라엘 모든 지파 중에 마음을 오로지하여 이스라엘 하나님 여호와를 구하는 자들이 레위사람을 따라 예루살렘에 이르러 그 열조의 하나님 여호와께 제사하고자 한지라
Waɗanda suke daga kowane kabilar Isra’ila waɗanda suka sa zuciya a kan neman Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka bi Lawiyawa zuwa Urushalima don su miƙa hadayu ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
17 그러므로 삼년동안 유다 나라를 도와 솔로몬의 아들 르호보암을 강성하게 하였으니 이는 무리가 삼년을 다윗과 솔로몬의 길로 행하였음이더라
Suka ƙarfafa mulkin Yahuda suka kuma goyi bayan Rehobowam ɗan Solomon shekaru uku, suna tafiya a hanyoyin Dawuda da Solomon a wannan lokaci.
18 르호보암이 다윗의 아들 여리못의 딸 마할랏으로 아내를 삼았으니 마할랏은 이새의 아들 엘리압의 딸 아비하일의 소생이라
Rehobowam ya auri Mahalat,’yar Yerimot ɗan Dawuda wadda Abihayil’yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa.
19 그가 아들들 곧 여우스와 스마랴와 사함을 낳았으며
Ta haifa masa’ya’ya maza. Yewush, Shemariya da Zaham.
20 그 후에 압살롬의 딸 마아가에게 장가들었더니 저가 아비야와 앗대와 시사와 슬로밋을 낳았더라
Sa’an nan ya auri Ma’aka’yar Absalom, wadda ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza da kuma Shelomit.
21 르호보암이 아내 십 팔과 첩 육십을 취하여 아들 이십 팔과 딸 육십을 낳았으나 압살롬의 딸 마아가를 모든 처첩보다 더 사랑하여
Rehobowam ya ƙaunaci Ma’aka’yar Absalom fiye da sauran matansa da ƙwarƙwaransa. Duka-duka dai ya auri mata goma sha takwas da ƙwarƙwarai sittin, yana da’ya’ya maza ashirin da takwas da’ya’ya mata sittin.
22 마아가의 아들 아비야를 세워 장자를 삼아 형제 중에 머리가 되게 하였으니 이는 저로 왕이 되게 하고자 함이라
Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma’aka yă zama babba yerima a cikin’yan’uwansa, don dai yă naɗa shi sarki.
23 르호보암이 지혜롭게 행하여 그 모든 아들을 유다와 베냐민의 온 땅 모든 견고한 성읍에 흩어 살게 하고 양식을 후히 주고 아내를 많이 구하여 주었더라
Ya yi hikima, ya watsar da waɗansu’ya’yansa a dukan yankunan Yahuda da Benyamin, da kuma a dukan birane masu katanga. Ya ba su tanadi mai yawa ya kuma aurar musu mata masu yawa.