< 베드로전서 1 >
1 예수 그리스도의 사도 베드로는 본도, 갈라디아, 갑바도기아, 아시아와 비두니아에 흩어진 나그네
Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zababbu wadanda suke baki, a warwatse cikin Buntus, Galatiya, kappadokiya, Asiya, da Bitiniya.
2 곧 하나님 아버지의 미리 아심을 따라 성령의 거룩하게 하심으로 순종함과 예수 그리스도의 피 뿌림을 얻기 위하여 택하심을 입은자들에게 편지하노니 은혜와 평강이 너희에게 더욱 많을찌어다
Bisa ga rigasanin Allah Uba, Ta wurin tsarkakewar Ruhu, zuwa biyayya da yayyafar jinin Yesu Almasihu. Alheri da salama su yawaita a gareku.
3 찬송하리로다 우리 주 예수 그리스도의 아버지 하나님이 그 많으신 긍휼대로 예수 그리스도의 죽은 자 가운데서 부활하심으로 말미암아 우리를 거듭나게 하사 산 소망이 있게 하시며
Albarka ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu. Ta wurin jinkansa mai girma, ya maya haihuwarmu zuwa bege mai rai ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu.
4 썩지 않고 더럽지 않고 쇠하지 아니하는 기업을 잇게 하시나니 곧 너희를 위하여 하늘에 간직하신 것이라
Zuwa gado marar lalacewa, marar baci, ba kuma zai kode ba. Wanda aka kebe a sama dominku.
5 너희가 말세에 나타내기로 예비하신 구원을 얻기 위하여 믿음으로 말미암아 하나님의 능력으로 보호하심을 입었나니
Ku da ikon Allah ya kiyaye ta wurin bangaskiya domin ceto wanda za'a bayyana a karshen zamanai.
6 그러므로 너희가 이제 여러 가지 시험을 인하여 잠간 근심하게 되지 않을 수 없었으나 오히려 크게 기뻐하도다
Cikin wannan kuna murna da yawa, duk da ya ke ya zama wajibi gare ku yanzu ku yi bakin ciki, a cikin jarabobi iri iri.
7 너희 믿음의 시련이 불로 연단하여도 없어질 금보다 더 귀하여 예수 그리스도의 나타나실 때에 칭찬과 영광과 존귀를 얻게 하려함이라
Wannan kuwa da nufin a iske aunawar bangaskiyarku ne, bangaskiyar da tafi zinariya daraja, wadda takan lalace ko da an gwada ta da wuta. Wannan ya faru domin bangaskiyan nan taku ta jawo maku yabo da girma da daukaka a bayyanuwar Yesu Almasihu.
8 예수를 너희가 보지 못하였으나 사랑하는도다 이제도 보지 못하나 믿고 말할 수 없는 영광스러운 즐거움으로 기뻐하니
Wanda kuke kauna, ko da yake baku ganshi ba. Ko da yake baku ganinsa yanzu, duk da haka kun bada gaskiya gare shi murnar da ku ke yi kwarai da farin ciki wanda tafi gaban a fadi cike da daukaka.
Kuna karbar sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku.
10 이 구원에 대하여는 너희에게 임할 은혜를 예언하던 선지자들이 연구하고 부지런히 살펴서
Annabawan da su ka yi annabcin ceton da ya zama naku su ka yi bidassa suka bincike kuma da himma.
11 자기 속에 계신 그리스도의 영이 그 받으실 고난과 후에 얻으실 영광을 미리 증거하여 어느 시, 어떠한 때를 지시하시는지 상고하니라
Sun nemi su san ko wanene da kuma kowanne lokaci ne Ruhun Almasihu da ke cikinsu yake bayyana ma su. Wannan ya faru ne sa'adda yake gaya ma su tun da wuri game da shan wahalar Almasihu da kuma daukakar da zata biyo baya.
12 이 섬긴 바가 자기를 위한 것이 아니요 너희를 위한 것임이 계시로 알게 되었으니 이것은 하늘로부터 보내신 성령을 힘입어 복음을 전하는 자들로 이제 너희에게 고한 것이요 천사들도 살펴보기를 원하는 것이니라
An kuwa bayyana wa annabawan cewa ba kansu suke hidimtawa ba, amma ku suke yi wa hidima. Wannan shine abin da suke yi game da abin da aka rigaya aka gaya maku, ta wurin wadanda da Ruhu mai Tsarki ya bishe su. Wanda aka aiko daga sama. Wadannan sune abubuwan da mala'iku ma suka yi marmarin a bayyana masu.
13 그러므로 너희 마음의 허리를 동이고 근신하여 예수 그리스도의 나타나실 때에 너희에게 가져올 은혜를 온전히 바랄찌어다
Domin wannan fa ku natsu. Ku yi dammara a hankalinku. Ku kafa begenku sarai akan alherin da za'a kawo maku a lokacin bayyanuwar Yesu Almasihu.
14 너희가 순종하는 자식처럼 이전 알지 못할 때에 좇던 너희 사욕을 본 삼지 말고
Kamar 'ya'ya masu biyyaya, kada ku biyewa sha'awoyinku na da a zamanin jahilcinku.
15 오직 너희를 부르신 거룩한 자처럼 너희도 모든 행실에 거룩한 자가 되라
Amma yadda shi wanda ya kira ku mai tsarki ne, kuma ku zama da tsarki cikin dukkan al'amuranku.
16 기록하였으되 내가 거룩하니 너희도 거룩할찌어다 하셨느니라
Domin a rubuce yake, “Ku zama da tsarki, gama ni mai tsarki ne.”
17 외모로 보시지 않고 각 사람의 행위대로 판단하시는 자를 너희가 아버지라 부른즉 너희의 나그네로 있을 때를 두려움으로 지내라
Idan ku na kira bisa gare shi “Uba” shi wanda yake hukuntawa ba da tara ba, amma gwar-gwadon aikin kowane mutum, sai kuyi zaman bakuncinku da tsoro da bangirma.
18 너희가 알거니와 너희 조상의 유전한 망령된 행실에서 구속된 것은 은이나 금같이 없어질 것으로 한 것이 아니요
Kun san cewa ba da azurfa ko zinariya mai lalacewa aka fanshe ku ba, daga halinn wauta da kuka gada daga wurin iyayenku.
19 오직 흠 없고 점 없는 어린 양 같은 그리스도의 보배로운 피로 한 것이니라
Maimakon haka an fanshe ku da jinin Almasihu mai daraja, marar aibu kamar na dan rago.
20 그는 창세 전부터 미리 알리신 바 된 자나 이 말세에 너희를 위하여 나타내신 바 되었으니
An zabi Almasihu tun kafin kafawar duniya, amma a karshen zamanu ya bayyanu a gare ku.
21 너희는 저를 죽은 자 가운데서 살리시고 영광을 주신 하나님을 그리스도로 말미암아 믿는 자니 너희 믿음과 소망이 하나님께 있게 하셨느니라
Ku da kuka bada gaskiya ga Allah ta wurinsa, wanda ya tashe shi daga matattu ya kuma bashi daukaka domin bangaskiyarku da begenku su kasance cikin Allah.
22 너희가 진리를 순종함으로 너희 영혼을 깨끗하게 하여 거짓이 없이 형제를 사랑하기에 이르렀으니 마음으로 뜨겁게 피차 사랑하라
Da shike kun tsarkake rayukanku cikin biyayyar ku ga gaskiya zuwa ga sahihiyar kauna ta 'yan'uwa, sai ku kaunaci junanku da zuciya mai gaskiya.
23 너희가 거듭난 것이 썩어질 씨로 된 것이 아니요 썩지 아니할 씨로 된 것이니 하나님의 살아 있고 항상 있는 말씀으로 되었느니라 (aiōn )
da shike an sake hai'huwarku ba daga iri mai lalacewa ba amma daga iri marar rubewa, ta wurin maganar Allah wadda take rayuwa ta kuma dawwama. (aiōn )
24 그러므로 모든 육체는 풀과 같고 그 모든 영광이 풀의 꽃과 같으니 풀은 마르고 꽃은 떨어지되
Gama “dukkan jiki kamar ciyawa yake, dukkan darajarsa kuwa kamar furen ciyawa take. Ciyawa takan yi yaushi, furenta ya kan yankwane ya fadi,
25 오직 주의 말씀은 세세토록 있도다 하였으니 너희에게 전한 복음이 곧 이 말씀이니라 (aiōn )
amma maganar Ubangiji tabbatacciya ce har abada. “Wannan ita ce maganar bishara wadda akayi maku wa'azinta.” (aiōn )