< 고린도전서 5 >
1 너희 중에 심지어 음행이 있다 함을 들으니 이런 음행은 이방인 중에라도 없는 것이라 누가 그 아비의 아내를 취하였다 하는도다
Mun ji cewa akwai lalata mai kazanta a cikin ku, irin lalatar ba ba a yarda da ita ba ko a cikin al'ummai. Labarin da na samu shine, wani daga cikin ku yana kwana da matar mahaifinsa.
2 그리하고도 너희가 오히려 교만하여져서 어찌하여 통한히 여기지 아니하고 그 일 행한 자를 너희 중에서 물리치지 아니하였느냐
Kuma kuna fahariya sosai! Ba bakinciki ya kamata ku yi ba? Shi wanda ya yi haka, dole a fitar da shi daga cikin ku.
3 내가 실로 몸으로는 떠나 있으나 영으로는 함께 있어서 거기 있는 것같이 이 일 행한 자를 이미 판단하였노라
Gama Kodashike ba ni tare da ku cikin jiki, amma ina tare daku a ruhu, na rigaya na hukunta wanda yayi wannan, tamkar ina wurin.
4 주 예수의 이름으로 너희가 내 영과 함께 모여서 우리 주 예수의 능력으로
Lokacin da ku ka taru a cikin sunan Ubangijinmu Yesu, ruhuna yana nan tare da ku cikin ikon Ubangiji Yesu, na rigaya na hukunta wannan mutum.
5 이런 자를 사단에게 내어주었으니 이는 육신은 멸하고 영은 주 예수의 날에 구원 얻게 하려 함이라
Na yi haka ne domin in mika wannan mutum ga Shaidan domin a hallaka jikin, don ruhunsa ya tsira a ranar Ubangiji.
6 너희의 자랑하는 것이 옳지 아니하도다 적은 누룩이 온 덩어리에 퍼지는 것을 알지 못하느냐
Fahariyarku bata yi kyau ba. Ko baku sani ba yisti dan kadan ya kan bata dukan dunkule?
7 너희는 누룩 없는 자인데 새 덩어리가 되기 위하여 묵은 누룩을 내어 버리라 우리의 유월절 양 곧 그리스도께서 희생이 되셨느니라
Ku tsarkake kan ku daga tsohon yisti domin ku zama sabon dunkule, wato gurasar da ba ta da yisti. Gama an yi hadayar Almsihu, dan ragonmu na idi.
8 이러므로 우리가 명절을 지키되 묵은 누룩도 말고 괴악하고 악독한 누룩도 말고 오직 순전함과 진실함의 누룩 없는 떡으로 하자
Don haka, bari mu yi idinmu ba da tsohon yisti ba, wato yisti irin na rashin tabi'a da mugunta. Maimakon haka, bari muyi bukin idi da gurasa marar yisti ta aminci da gaskiya.
9 내가 너희에게 쓴 것에 음행하는 자들을 사귀지 말라 하였거니와
Na rubuta maku a cikin wasikata cewa kada ku yi hudda da fasikan mutane.
10 이 말은 이 세상의 음행하는 자들이나 탐하는 자들과 토색하는 자들이나 우상 숭배하는 자들을 도무지 사귀지 말라 하는 것이 아니니 만일 그리하려면 세상 밖으로 나가야 할 것이라
Ba ina nufin fasikan mutane na wannan duniya ba, ko masu zari, ko 'yan'damfara, ko masu bautar gumaka, tunda kafin ku rabu da su sai kun bar wannan duniya.
11 이제 내가 너희에게 쓴 것은 만일 어떤 형제라 일컫는 자가 음행하거나 탐람하거나 우상 숭배를 하거나 후욕하거나 술 취하거나 토색하거든 사귀지도 말고 그런 자와는 함께 먹지도 말라 함이라
Amma yanzu ina rubuta maku cewa kada ku yi hudda da duk wanda ake kira dan'uwa amma yana zama cikin fasikanci, ko zari, ko bautar gumaka, ko in shi mai ashar ne, ko mashayi, ko dan'damfara. Kada ko abinci ku ci da irin wannan mutum.
12 외인들을 판단하는데 내게 무슨 상관이 있으리요마는 교중 사람들이야 너희가 판단치 아니하랴
Domin ta yaya zan iya shar'anta wadanda ba 'yan Ikklisiya ba? Maimakon haka, ba ku ne zaku shar'anta wadanda ke cikin ikilisiya ba?
13 외인들은 하나님이 판단 하시려니와 이 악한 사람은 너희 중에서 내어 쫓으라
Amma Allah ke shar'anta wadanda ke waje. “Ku fitar da mugun mutumin daga cikin ku.”