< 고린도전서 16 >

1 성도를 위하는 연보에 대하여는 내가 갈라디아 교회들에게 명한 것같이 너희도 그렇게 하라
To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa.
2 매주일 첫날에 너희 각 사람이 이(利)를 얻은 대로 저축하여 두어서 내가 갈 때에 연보를 하지 않게 하라
A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba.
3 내가 이를 때에 너희의 인정한 사람에게 편지를 주어 너희의 은혜를 예루살렘으로 가지고 가게 하리니
In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima.
4 만일 나도 가는 것이 합당하면 저희가 나와 함께 가리라
In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni.
5 내가 마게도냐를 지날 터이니 마게도냐를 지난 후에 너희에게 나아가서
Bayan na zazzaga Makidoniya, zan zo wurinku, domin zan ratsa ta Makidoniya.
6 혹 너희와 함께 머물며 과동(過冬)할 듯도 하니 이는 너희가 나를 나의 갈 곳으로 보내어 주게 하려 함이라
Wataƙila zan ɗan jima a wajenku, ko ma in ci damina a can, domin ku yi mini rakiya a tafiyata, duk inda za ni.
7 이제는 지나는 길에 너희 보기를 원치 하니하노니 이는 주께서 만일 허락하시면 얼마 동안 너희와 함께 유하기를 바람이라
Ba na so in gan ku yanzu in wuce kawai, ina fata zan yi’yan kwanaki tare da ku, in Ubangiji ya yarda.
8 내가 오순절까지 에베소에 유하려 함은
Sai dai zan kasance a Afisa har lokacin Fentekos,
9 내게 광대하고 공효(功效)를 이루는 문(門)이 열리고 대적하는 자가 많음이니라
domin an buɗe mini wata hanya mai fāɗi don aiki mai amfani, ko da yake akwai mutane da yawa masu gāba da ni.
10 디모데가 이르거든 너희는 조심하여 저로 두려움이 없이 너희 가운데 있게 하라 이는 저도 나와 같이 주의 일을 힘쓰는 자임이니라
In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.
11 그러므로 누구든지 저를 멸시하지 말고 평안히 보내어 내게로 오게하라 나는 저가 형제들과 함께 오기를 기다리노라
Kada fa wani yă ƙi karɓansa. Ku sallame shi lafiya, domin yă koma wurina. Ina duban hanyarsa tare da’yan’uwa.
12 형제 아볼로에 대하여는 저더러 형제들과 함께 너희에게 가라고 내가 많이 권하되 지금은 갈 뜻이 일절 없으나 기회가 있으면 가리라
Batun ɗan’uwanmu Afollos kuwa, na roƙe shi sosai yă zo wurinku tare da’yan’uwa. Bai so zuwa yanzu ba, amma zai zo in ya sami zarafi.
13 깨어 믿음에 굳게 서서 남자답게 강건하여라!
Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.
14 너희 모든 일을 사랑으로 행하라!
Ku yi kome da ƙauna.
15 형제들아 스데바나의 집은 곧 아가야의 첫 열매요 또 성도 섬기기로 작정한 줄을 너희가 아는지라 내가 너희를 권하노니
Kun san cewa iyalin gidan Istifanas ne suka fara tuba a Akayya. Sun kuma ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima. Ina roƙonku’yan’uwa,
16 이 같은 자들과 또 함께 일하며 수고하는 모든 자에게 복종하라
ku ba da kanku ga irin waɗannan, ga kuma kowa da ya haɗa hannu a aikin, yana kuma faman a cikinsa.
17 내가 스데바나와, 브드나도와, 아가이고의 온 것을 기뻐하노니 저희가 너희의 부족한 것을 보충하였음이니라
Na yi farin ciki da isowar Istifanas, Fortunatus da Akaikus, domin sun biya bukatar da ba ku iya biya ba.
18 저희가 나와 너희 마음을 시원케 하였으니 그러므로 너희는 이런 자들을 알아 주라
Gama sun wartsake ruhuna da kuma naku. Ya kamata ku girmama irin waɗannan mutane.
19 아시아의 교회들이 너희에게 문안하고 아굴라와, 브리스가와 및 그 집에 있는 교회가 주 안에서 너희에게 간절히 문안하고
Ikkilisiyoyin da suke a lardin Asiya suna gaisuwa. Akwila da Firiskila suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji, haka ma ikkilisiyar da takan taru a gidansu.
20 모든 형제도 너희에게 문안하니 너희는 거룩하게 입맞춤으로 서로 문안하라
Dukan’yan’uwa a nan suna gaisuwa. Ku gai da juna da sumba mai tsarki.
21 나 바울은 친필로 너희에게 문안하노니
Ni, Bulus nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna.
22 만일 누구든지 주를 사랑하지 아니하거든 저주를 받을지어다 주께서 임하시느니라
Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji, la’ana ta zauna a kansa. Zo, ya Ubangiji!
23 주 예수 그리스도의 은혜가 너희와 함께 하고
Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da ku.
24 나의 사랑이 그리스도 예수의 안에서 너희 무리와 함께 할지어다
Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙaunata cikin Kiristi Yesu. Amin.

< 고린도전서 16 >