< 역대상 17 >

1 다윗이 그 궁실에 거할 때에 선지자 나단에게 이르되 나는 백향목 궁에 거하거늘 여호와의 언약궤는 휘장 밑에 있도다
Bayan Dawuda ya zauna a fadansa, sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar da aka yi da al’ul, yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yana a ƙarƙashin tenti.”
2 나단이 다윗에게 고하되 하나님이 왕과 함께 계시니 무릇 마음에 있는 바를 행하소서
Natan ya amsa wa Dawuda ya ce, “Duk abin da kake tunani a zuciya, ka yi, gama Allah yana tare da kai.”
3 그 밤에 하나님의 말씀이 나단에게 임하여 가라사대
A daren nan maganar Allah ta zo wa Natan cewa,
4 가서 내 종 다윗에게 말하기를 여호와의 말씀이 너는 나의 거할 집을 건축하지 말라
“Ka tafi ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ba kai ba ne za ka gida mini gidan da zan zauna a ciki.
5 내가 이스라엘을 올라오게 한날부터 오늘날까지 집에 거하지 아니하고 오직 이 장막과 저 장막에 있으며 이 성막과 저 성막에 있었나니
Ban taɓa zama a gida daga ranar da na fito da Isra’ila daga Masar ba har wa yau. Na yi ta yawo daga gefen da aka kafa tenti zuwa wani, daga wannan wuri zuwa wancan.
6 무릇 이스라엘 무리로 더불어 행하는 곳에서 내가 내 백성을 먹이라고 명한 이스라엘 어느 사사에게 내가 말하기를 너희가 어찌하여 나를 위하여 백향목 집을 건축하지 아니하였느냐고 말하였느냐 하고
Duk inda na tafi tare da Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani daga cikin shugabanninsu waɗanda na umarta su yi kiwon mutanena, “Don me ba ku gida mini gidan al’ul ba?”’
7 연하여 내 종 다윗에게 이처럼 말하라 만군의 여호와께서 이처럼 말씀하시기를 내가 너를 목장 곧 양을 따르는 데서 취하여 내 백성 이스라엘의 주권자를 삼고
“Yanzu, ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauke ka daga makiyaya da kuma daga bin garke, don ka zama mai mulki a bisa mutanena Isra’ila.
8 네가 어디를 가든지 내가 너와 함께 있어 네 모든 대적을 네 앞에서 멸하였은즉 세상에서 존귀한 자의 이름 같은 이름을 네게 만들어 주리라
Na kasance tare da kai ko’ina ka tafi, na kuma yanke dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka kamar sunayen mutane mafi girma na duniya.
9 내가 또 내 백성 이스라엘을 위하여 한 곳을 정하여 저희를 심고 저희로 자기 곳에 거하여 다시는 옮기지 않게 하며 악한 유로 전과 같이 저희를 해하지 못하게 하여
Zan kuma tanada wuri domin mutanena Isra’ila, zan kuma kafa su saboda za su kasance da gidan kansu ba kuwa za a ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara zaluntar su ba, yadda suka yi da farko
10 전에 내가 사사를 명하여 내 백성 이스라엘을 다스리던 때와 같지 않게 하고 또 모든 대적으로 네게 복종하게 하리라 또 네게 이르노니 여호와가 너를 위하여 집을 세울지라
da kuma suka yi tun lokacin da na sa shugabanni a bisa mutanen Isra’ila. Zan rinjaye dukan abokan gābanka. “‘Na furta maka cewa Ubangiji zai gina maka gida,
11 네 수한이 차서 네가 열조에게로 돌아가면 내가 네 뒤에 네씨 곧 네 아들 중 하나를 세우고 그 나라를 견고하게 하리니
sa’ad da kwanakinka suka ƙare ka kuma tafi don ka kasance da kakanninka, zan tā da ɗaya cikin’ya’yanka maza, daga zuriyarka yă gāje ka, zan kuma kafa mulkinka.
12 저는 나를 위하여 집을 건축할것이요 나는 그 위를 영원히 견고하게 하리라
Shi ne zai gina gida domina, zan kuma kafa sarautarsa har abada.
13 나는 그 아비가 되고 그는 나의 아들이 되리니 나의 자비를 그 에게서 빼앗지 아니하기를 내가 네 전에 있던 자에게서 빼앗음과 같이 하지 않을 것이며
Zan zama Ubansa, zai kuma zama ɗana. Ba zan taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi, kamar yadda na ɗauke ta daga wanda ya riga ka ba.
14 내가 영영히 그를 내 집과 내 나라에 세우리니 그 위가 영원히 견고하리라 하셨다 하라
Zan sa shi a bisa gidana da mulkina har abada; kujerar sarautarsa za tă kahu har abada.’”
15 나단이 이 모든 말씀과 이 모든 묵시대로 다윗에게 고하니라
Natan ya faɗa wa Dawuda dukan kalmomin wahayin nan.
16 다윗 왕이 여호와 앞에 들어가 앉아서 가로되 여호와 하나님이여 나는 누구오며 내 집은 무엇이관대 나로 이에 이르게 하셨나이까
Sai Sarki Dawuda ya shiga ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, kuma wane ne iyalina, da ka kawo ni har zuwa nan?
17 하나님이여 주께서 이것을 오히려 작게 여기시고 또 종의 집에 대하여 먼 장래까지 말씀하셨사오니 여호와 하나님이여 나를 존귀한 자 같이 여기셨나이다
Kuma sai ka ce wannan bai isa ba a idonka, ya Allah, ka yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Ka dube ni sai ka ce ni ne mafi ɗaukaka cikin mutane, ya Ubangiji Allah.
18 주께서 주의 종에게 베푸신 존귀에 대하여 다윗이 다시 무슨 말씀을 하오리이까 주께서는 주의 종을 아시나이다
“Me kuma Dawuda zai ce maka saboda girmamawar da ka yi wa bawanka? Gama ka san bawanka,
19 여호와여 주께서 주의 종을 위하여 주의 뜻대로 이 모든 큰 일을 행하사 이 모든 큰 일을 알게 하셨나이다
Ya Ubangiji. Gama saboda bawanka da kuma bisa ga nufinka, ka yi wannan babban abu, ka kuma sanar da dukan manyan alkawura.
20 여호와여 우리 귀로 들은 대로는 주와 같은 이가 없고 주 외에는 참 신이 없나이다
“Babu wani kamar ka, ya Ubangiji, babu kuma Allah sai kai, kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.
21 땅의 어느 한 나라가 주의 백성 이스라엘과 같으리이까 하나님이 가서 구속하사 자기 백성을 삼으시고 크고 두려운 일로 인하여 이름을 얻으시고 애굽에서 구속하신 자기 백성 앞에서 열국을 쫓아내셨사오며
Wane ne kuma yake kamar mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allahnta ya fita don yă fanshi mutane wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa masu banmamaki masu banrazana ta wurin korin al’ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka fansa daga Masar?
22 주께서 주의 백성 이스라엘로 영원히 주의 백성을 삼으셨사오니 여호와여 주께서 저희 하나님이 되셨나이다
Ka mai da mutanenka Isra’ila na kanka har abada, kuma kai, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.
23 여호와여 이제 주의 종과 그 집에 대하여 말씀하신 것을 영원히 견고케 하시며 말씀하신 대로 행하사
“Yanzu kuwa, Ubangiji, bari alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa yă kahu har abada. Yi kamar yadda ka yi alkawari,
24 견고케 하시고 사람으로 영원히 주의 이름을 높여 이르기를 만군의 여호와는 이스라엘의 하나님 곧 이스라엘에게 하나님이시라 하게 하시며 주의 종 다윗의 집이 주 앞에서 견고히 서게 하옵소서
saboda zai kahu kuma sunanka zai zama mai girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki, Allah a bisa Isra’ila, Allahn Isra’ila ne!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka.
25 나의 하나님이여 주께서 종을 위하여 집을 세우실 것을 이미 듣게 하셨으므로 주의 종이 주 앞에서 이 기도로 구할 마음이 생겼나이다
“Kai, Allahna, ka bayyana ga bawanka cewa za ka gina gida dominsa. Ta haka bawanka ya sami ƙarfin gwiwa ya yi addu’a gare ka.
26 여호와여 오직 주는 하나님이시라 주께서 이 좋은 것으로 주의 종에게 허락하시고
Ya Ubangiji, kai ne Allah! Ka yi alkawari abubuwa masu kyau wa bawanka.
27 이제 주께서 종의 집에 복을 주사 주 앞에 영원히 두시기를 기뻐하시나이다 여호와여 주께서 복을 주셨사오니 이 복을 영원히 누리리이다 하니라
Yanzu ka ji daɗi don ka albarkace gidan bawanka, don yă ci gaba har abada a gabanka; gama kai, ya Ubangiji, ka albarkace shi, ya kuma sami albarka ke nan har abada.”

< 역대상 17 >