< 예레미야 8 >
1 나 여호와가 말하노라 그 때에 사람들이 유다 왕들의 뼈와 그 방백들의 뼈와 제사장들의 뼈와 선지자들의 뼈와 예루살렘 거민의 뼈를 그 묘실에서 끌어내어
“‘A wancan lokaci, in ji Ubangiji, za a fitar da ƙasusuwan sarakuna da na shugabannin Yahuda, ƙasusuwan firistoci da na annabawa, da kuma ƙasusuwan mutanen Urushalima daga kaburbura.
2 그들의 사랑하며 섬기며 순종하며 구하며 경배하던 해와 달과 하늘의 뭇 별 아래 쬐리니 그 뼈가 거두이거나 묻히지 못하여 지면에서 분토 같을 것이며
Za a shimfiɗa su a rana da wata da kuma dukan taurarin sammai, waɗanda suka ƙaunata suka kuma bauta wa, waɗanda suka bi suka nemi shawarar suka kuma yi wa sujada. Ba za a tattara su ko a binne su ba, amma za su zama kamar juji a jibge a ƙasa.
3 이 악한 족속의 남아 있는자, 무릇 내게 쫓겨 나서 각처에 남아 있는 자가 사는 것보다 죽는 것을 원하리라 만군의 여호와의 말이니라
Duk inda na kore su zuwa, dukan waɗanda suka ragu na wannan muguwar al’umma za su gwammaci mutuwa da rai, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’
4 너는 또 그들에게 말하기를 여호와의 말씀에 사람이 엎드러지면 어찌 일어나지 아니하겠으며 사람이 떠나 갔으면 어찌 돌아오지 아니하겠느냐?
“Fada musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, “‘Sa’ad da mutane suka fāɗi, ba sa tashi ne? Sa’ad da mutum ya kauce, ba ya dawowa?
5 이 예루살렘 백성이 항상 나를 떠나 물러감은 어찜이뇨 그들이 거짓을 고집하고 돌아오기를 거절하도다
To, me ya sa waɗannan mutane suka kauce? Me ya sa Urushalima kullum take kaucewa? Sun manne wa ƙarya; suka ƙi su dawo.
6 내가 귀를 기울여 들은즉 그들이 정직을 말하지 아니하며 그 악을 뉘우쳐서 나의 행한 것이 무엇인고 말하는 자가 없고 전장을 향하여 달리는 말같이 각각 그 길로 행하도다
Na saurara sosai, amma ba su faɗi wata maganar kirki ba. Ba wanda ya tuba daga muguntarsa, sai ma cewa yake, “Me na yi?” Kowa ta kai-ta-kai yake kamar dokin da ya kutsa kai a fagen fama.
7 공중의 학은 그 정한 시기를 알고 반구와 제비와 두루미는 그 올때를 지키거늘 내 백성은 여호와의 규례를 알지 못하도다 하셨다 하라
Ko shamuwa ta sararin sama ma takan san lokutan da aka tsara mata, kurciya, mashirare da kuma zalɓe sukan lura da lokacin ƙauransu. Amma mutanena ba su san abubuwan da Ubangiji yake bukata ba.
8 너희가 어찌 우리는 지혜가 있고 우리에게는 여호와의 율법이 있다 말하겠느뇨 참으로 서기관의 거짓 붓이 거짓되게 하였나니
“‘Yaya za ku ce, “Muna da hikima, gama muna da dokar Ubangiji,” alhali alƙalamin ƙarya na magatakarda ya yi ƙarya?
9 지혜롭다 하는 자들은 수욕을 받으며 경황 중에 잡히리라 보라 그들이 나 여호와의 말을 버렸으니 그들에게 무슨 지혜가 있으랴
Za a kunyatar da masu hikima; za su yi fargaba a kuma kama su. Da yake sun ƙi maganar Ubangiji, wace irin hikima kuka ce kuke da ita?
10 그러므로 내가 그들의 아내를 타인에게 주겠고 그들의 전지를 그 차지할 자들에게 주리니 그들은 가장 작은 자로부터 큰 자까지 다 탐남하며 선지자로부터 제사장까지 다 거짓을 행함이라
Saboda haka zan ba da matansu ga waɗansu gonakinsu kuma ga waɗansu da suka ci da yaƙi. Tun daga ƙarami har zuwa babba, kowannensu yana haɗamar cin muguwar riba; har da annabawa da firistoci ma, kowannensu yana ƙarya.
11 그들이 딸 내 백성의 상처를 심상히 고쳐주며 말하기를 평강하다, 평강하다 하나 평강이 없도다
Sukan ɗaura mikin mutanena sai ka ce mikin ba shi da matsala. Suna cewa, “Lafiya, Lafiya,” alhali kuwa ba lafiya.
12 그들이 가증한 일을 행할 때에 부끄러워하였느냐? 아니라 조금도 부끄러워 아니할 뿐 아니라 얼굴도 붉어지지 아니하였느니라 그러므로 그들이 엎드러질 자와 함께 엎드러질 것이라 내가 그들을 벌할 때에 그들이 거꾸러지리라 여호와의 말이니라
Sukan ji kunyar halin banƙyamarsu kuwa? Sam, ba su da kunya ko kaɗan; ba su ma san yadda za su ji kunya ba. Saboda haka sukan fāɗi tare da fāɗaɗɗu; za su fāɗi sa’ad da aka hukunta su, in ji Ubangiji.
13 여호와께서 말씀하시되 내가 그들을 진멸하리니 포도나무에 포도가 없을 것이며 무화과 나무에 무화과가 없을 것이며 그 잎사귀가 마를 것이라 내가 그들에게 준 것이 없어지리라 하셨나니
“‘Zan ƙwace girbinsu, in ji Ubangiji. Ba a za sami inabi a kuringa ba. Ba za a sami’ya’ya a itacen ɓaure ba, ganyayensu kuwa za su bushe. Abin da na ba su za a ƙwace.’”
14 우리가 어찌 가만히 앉았으랴 모일지어다 우리가 견고한 성읍들로나 들어가서 거기서 멸망하자 우리가 여호와께 범죄하였으므로 우리 하나님 여호와께서 우리를 멸하시며 우리에게 독한 물을 마시우심이니라
Me ya sa muke zama a nan? Mu tattaru! Mu gudu zuwa birane masu katanga mu mutu a can! Gama Ubangiji Allahnmu ya ƙaddara mana mutuwa ya kuma ba mu ruwan dafi mu sha, domin mun yi masa zunubi.
15 우리가 평강을 바라나 좋은 것이 없으며 고치심을 입을 때를 바라나 놀라움 뿐이로다
Mun sa zuciya ga salama amma ba lafiya, mun sa zuciya ga lokacin warkarwa amma sai ga razana.
16 그 말의 부르짖음이 단에서부터 들리고 그 준마들의 우는 소리에 온 땅이 진동하며 그들이 이르러 이 땅과 그 소유와 성읍과 그 중의 거민을 삼켰도다
Daga Dan ana jin tirjin dawakan abokin gāba; da jin haniniyar ingarmunsu dukan ƙasar ta girgiza. Sun zo su cinye ƙasar da kome da yake cikinta, birni da dukan mazaunanta.
17 여호와께서 말씀하시되 내가 술법으로도 제어할 수 없는 뱀과 독사를 너희 중에 보내리니 그것들이 너희를 물리라 하시도다
“Duba, zan aika macizai masu dafi a cikinku, kāsā, waɗanda ba su da maƙari, za su kuwa sassare ku,” in ji Ubangiji.
18 슬프다, 나의 근심이여 어떻게 위로를 얻을 수 있을까? 나의 중심이 번뇌하도다
Ya mai ta’aziyyata a cikin baƙin ciki, zuciyata ta ɓaci ƙwarai.
19 딸, 내 백성의 심히 먼 땅에서 부르짖는 소리로다 이르기를 여호와께서 시온에 계시지 아니한가, 그 왕이 그 중에 계시지 아니한가 그러나 여호와께서는 이르시기를 그들이 어찌하여 그 조각한 신상과 이방의 헛된 것들로 나를 격노케 하였는고 하시니
Ka saurari kukan mutanena daga ƙasa mai nisa suna cewa, “Ubangiji ba ya a Sihiyona ne? Sarkinta ba ya can ne kuma?” “Me ya sa suka tsokane ni da gumakansu har na yi fushi, da baƙin gumakansu marasa amfani?”
20 추수할 때가 지나고 여름이 다하였으나 우리는 구원을 얻지 못한다 하는도다
“Girbi ya wuce, damuna ta ƙare, ba a kuwa cece mu ba.”
21 딸 내 백성이 상하였으므로 나도 상하여 슬퍼하며 놀라움에 잡혔도다
Da yake an ragargazar da mutanena, an ragargaza ni ke nan; na yi kuka, tsoro ya kama ni.
22 길르앗에는 유향이 있지 아니한가 그곳에는 의사가 있지 아니한가 딸 내 백성이 치료를 받지 못함은 어찜인고
Ba magani ne a Gileyad? Ba likita ne a can? To, me ya sa ba warkarwa wa raunin mutanena?