< 사도행전 15 >
1 어떤 사람들이 유대로부터 내려와서 형제들을 가르치되 `너희가 모세의 법대로 할례를 받지 아니하면 능히 구원을 얻지 못하리라' 하니
Wadansu mutane suka zo daga Yahudiya suka koyar da 'yan'uwa, cewa, “Idan ba yi maku kaciya bisa ga al'addar Musa ba, ba za ku sami ceto ba.”
2 바울과 바나바와 저희 사이에 적지 아니한 다툼과 변론이 일어난지라 형제들이 이 문제에 대하여 바울과 바나바와 및 그 중에 몇사람을 예루살렘에 있는 사도와 장로들에게 보내기로 작정하니
Da Bulus da Barnaba suka tunkare su da mahawara, sai 'yan'uwa suka yanke shawara Bulus da Barnaba da wasu su je Urushalima wurin manzanni da dattawa a kan wannan magana.
3 저희가 교회의 전송을 받고 베니게와 사마리아로 다녀가며 이방인들의 주께 돌아온 일을 말하여 형제들을 다 크게 기쁘게 하더라
Da shike iklisiya ce ta aike su, sai suka bi ta Finikiya da ta Samariya suka sanar da tuban al'ummai. Ya kawo murna mai yawa a wurin 'yan'uwa.
4 예루살렘에 이르러 교회와 사도와 장로들에게 영접을 받고 하나님이 자기들과 함께 계셔 행하신 모든 일을 말하매
Bayan sun zo Urushalima, sai iklisiya da manzanni da dattawa, suka marabce su, sai suka fada masu abin da Allah ya yi ta wurinsu.
5 바리새파 중에 믿는 어떤 사람들이 일어나 말하되 `이방인에게 할례주고 모세의 율법을 지키라 명하는 것이 마땅하다' 하니라
Amma wadansu mutane wadanda suka ba da gaskiya daga cikin Farisawa, suka tashi suka ce, “Dole ne a yi masu kaciya a kuma umarce su su kiyaye dokar Musa.”
Sai manzanin da dattawan suka taru don su duba wannan lamari.
7 많은 변론이 있은 후에 베드로가 일어나 말하되 `형제들아, 너희도 알거니와 하나님이 이방인들로 내 입에서 복음의 말씀을 들어 믿게 하시려고 오래 전부터 너희 가운데서 나를 택하시고
Bayan mahawara mai tsanani, sai Bitrus ya tashi ya ce masu, “'Yan'uwa, kun san lokacin baya da ya wuce, Allah ya yi zabi a cikinku, cewa ta bakina ne al'ummai za su ji bishara, su kuma ba da gaskiya.
8 또 마음을 아시는 하나님이 우리에게와 같이 저희에게도 성령을 주어 증거하시고
Allah, wanda ya san zuciya, ya yi masu shaida, ya kuma basu Ruhu Mai Tsarki kamar yadda ya yi mana;
9 믿음으로 저희 마음을 깨끗이 하사 저희나 우리나 분간치 아니하셨느니라
kuma bai bambanta mu da su ba, ya tsabtace zuciyarsu ta wurin bangaskiya.
10 그런데 지금 너희가 어찌하여 하나님을 시험하여 우리 조상과 우리도 능히 메지 못하던 멍에를 제자들의 목에 두려느냐
To, saboda haka don me kuke gwada Allah, kuna sa wa almajirai nauyi a wuya wanda ubanninmu duk da mu ba mu iya dauka ba?
11 우리가 저희와 동일하게 주 예수의 은혜로 구원 받는 줄을 믿노라' 하니라
Amma mun gaskanta za mu samu ceto ta wurin alherin Ubangiji Yesu, kamar yadda suke.”
12 온 무리가 가만히 있어 바나바와 바울이 하나님이 자기들로 말미암아 이방인 중에서 행하신 표적과 기사 고하는 것을 듣더니
Dukan taron jama'ar suka yi shiru sa'adda suke sauraron sakon shaidar da mamakin abin da Allah ya yi ta wurin Bulus da Barnaba a cikin al'ummai.
13 말을 마치매 야고보가 대답하여 가로되 `형제들아 내 말을 들으라
Bayan sun gama magana, Yakubu ya amsa, ya ce, “'Yan'uwa, ku ji ni.
14 하나님이 처음으로 이방인 중에서 자기 이름을 위할 백성을 취하시려고 저희를 권고하신 것을 시므온이 고하였으니
Saminu ya fada yadda Allah ya fara nuna jinkai ga al'ummai domin ya dauke jama'a daga cikinsu domin sunansa.
15 선지자들의 말씀이 이와 합하도다 기록된 바
Maganar annabawa ta yarda da wannan, kamar yadda yake a rubuce,
16 이 후에 내가 돌아와서 다윗의 무너진 장막을 다시 지으며 또 그 퇴락한 것을 다시 지어 일으키리니
'Bayan wadannan abubuwa zan dawo, zan gina gidan Dauda wanda ya fadi kasa; in sake gina bangonsa, in tsayar da shi,
17 이는 그 남은 사람들과 내 이름으로 일컬음을 받는 모든 이방인들로 주를 찾게 하려 함이라 하셨으니
saboda sauran jama'a su nemi fuskar Ubangiji, har da al'ummai da ake kira da sunana.
18 즉 예로부터 이것을 알게 하시는 주의 말씀이라 함과 같으니라 (aiōn )
Wannan shine abin da Ubangiji ya fadi, shi wanda ya yi wadannan abubuwa da aka sani tun zamanin da. (aiōn )
19 그러므로 내 의견에는 이방인중에서 하나님께로 돌아 오는 자들을 괴롭게 말고
Saboda haka, a gani na kada mu matsa wa al'umman da suka juyo gun Allah;
20 다만 우상의 더러운 것과 음행과 목매어 죽인 것과 피를 멀리하라고 편지하는 것이 가하니
amma zamu rubuta masu da cewa, su guje wa gumaka da zina da faskanci da maye da cin mushe.
21 이는 예로부터 각 성에서 모세를 전하는 자가 있어 안식일마다 회당에서 그 글을 읽음이니라' 하더라
Tun zamanin da akwai mutane a kowanne birni wadanda suke wa'azi da karatun Musa a majami'u kowanne Asabaci.”
22 이에 사도와 장로와 온 교회가 그 중에서 사람을 택하여 바울과 바나바와 함께 안디옥으로 보내기를 가결하니 곧 형제 중에 인도자인 바사바라 하는 유다와 실라더라
Sai ya yi wa manzanin kyau su da dattawa da dukan iklisiyar su zabi Yahuza da Barnaba da Sila da dattawan iklisiya a tura su Antakiya tare da Bulus da Barnaba.
23 그 편에 편지를 부쳐 이르되 `사도와 장로된 형제들은 안디옥과 수리아와 길리기아에 있는 이방인 형제들에게 문안하노라
Sai suka rubuta wasika, “Manzani da dattawa da 'yan'uwa zuwa ga al'ummai 'yan'uwa a Antakiya da Suriya da Kilikiya, gaisuwa mai yawa.
24 들은즉 우리 가운데서 어떤 사람들이 우리의 시킨 것도 없이 나가서 말로 너희를 괴롭게 하고 마음을 혹하게 한다 하기로
Mun ji cewa wasu mutane daga cikinmu wadanda ba mu umarce su ba, sun fita daga cikinmu sun yi maku koyarwar da ta daga maku hankali.
25 사람을 택하여 우리 주 예수 그리스도의 이름을 위하여 생명을 아끼지 아니하는 자인 우리의 사랑하는 바나바와 바울과 함께 너희에게 보내기를 일치 가결하였노라
Ya yi kyau da dukanmu, muka amince mu zabi wadansu mutane mu tura su wurinku tare da Bulus da Barnaba,
mutane wadanda suka sadaukar da ransu domin sunan Ubangiji Yesu Almasihu.
27 그리하여 유다와 실라를 보내니 저희도 이 일을 말로 전하리라
Mun aika Yahuza da Sila su gaya maku wadannan abubuwa.
28 성령과 우리는 이 요긴한 것들 외에 아무 짐도 너희에게 지우지 아니하는 것이 가한 줄 알았노니
Saboda haka ya yi kyau Ruhu Mai Tsarki da mu, kada mu sa maku nauyi fiye da wadannan abubuwan:
29 우상의 제물과 피와 목매어 죽인 것과 음행을 멀리 할지니라 이에 스스로 삼가면 잘되리라 평안함을 원하노라' 하였더라
ku bar yi wa gumaka hadaya, ku bar cin mushe da shan kayan maye da zina da faskanci, in kun kiyaye wadannan abubuwa za ku zauna lafiya. Ku huta lafiya.”
30 저희가 작별하고 안디옥에 내려가 무리를 모은 후에 편지를 전하니
Da aka sallame su, sai suka je Antakiya. Bayan sun tara jama'a sai suka ba su wasikar.
Bayan da suka karanta ta, sai suka yi murna sosai saboda karfafawa.
32 유다와 실라도 선지자라 여러말로 형제를 권면하여 굳게 하고
Yahuza da Sila, da shike su annabawa ne, suka karfafa 'yan'uwa da kalmomi masu yawa.
33 얼마 있다가 평안히 가라는 전송을 형제들에게 받고 자기를 보내던 사람들에게로 돌아가되
Bayan sun yi kwananki a wurin, sai aka sallame su zuwa wurin 'yan'uwa wadanda suka aiko su.
Amma ya gamshe Sila ya zauna a wurin.
35 바울과 바나바는 안디옥에서 유하여 다수한 다른 사람들과 함께 주의 말씀을 가르치며 전파하니라
Amma Bulus da Barnaba suka tsaya a Antakiya da sauran 'yan'uwa, suna koyar da maganar Ubangiji.
36 수일 후에 바울이 바나바더러 말하되 `우리가 주의 말씀을 전한 각 성으로 다시 가서 형제들이 어떠한가 방문하자' 하니
Bayan kwanaki kadan Bulus ya ce ma Barnaba, “Mu koma yanzu mu ziyarci dukan 'yan'uwa da muka yi masu bisharar Ubangiji, mu ga yadda suke.
37 바나바는 마가라 하는 요한도 데리고 가고자 하나
Barnaba yana so su dauki Yahaya wanda kuma ake kira Markus.
38 바울은 밤빌리아에서 자기들을 떠나 한가지로 일하러 가지 아니한 자를 데리고 가는 것이 옳지않다 하여
Amma Bulus ya yi tunanin bai kamata a tafi da Markus ba, tun da ya bar su a Bamfiliya bai ci gaba da su ba.
39 서로 심히 다투어 피차 갈라서니 바나바는 마가를 데리고 배 타고 구브로로 가고
Nan jayayya ta tashi tsakaninsu, har suka rabu da juna sai Barnaba ya tafi tare da Markus suka ketare zuwa Kuburus.
40 바울은 실라를 택한 후에 형제들에게 주의 은혜에 부탁함을 받고 떠나
Amma Bulus ya zabi Sila suka tafi, bayan 'yan'uwa sun yi masu addu'ar alherin Allah ya kiyaye su.
41 수리아와 길리기아로 다녀가며 교회들을 굳게 하니라
Bulus ya tafi ya zazzaga Suriya da Kilikiya yana ta karfafa iklisiyoyin.