< ヨハネの福音書 21 >
1 其後イエズス、又チベリアデの湖辺にて己を弟子等に現し給ひしが、其現し給ひし次第は次の如し。
Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya. Ga yadda ya faru.
2 シモン、ペトロとチヂモと呼ばるるトマと、ガリレアのカナ生れなるナタナエルと、ゼベデオの子等と、尚外に二人の弟子共に在りけるに、
Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili,’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare.
3 シモン、ペトロ、我漁に往く、と云ひしかば彼等、我等も共に往く、と云ひて、皆出行きて船に乗りしに、其夜は何をも獲ざりき。
Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.
4 然て天明に至りてイエズス濱に立ち給へり、然りながら弟子等は其イエズスなる事を認めざれば、
Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.
5 イエズス彼等に向ひ、子等よ肴あるか、と曰ひしに彼等、無しと答へたり。
Sai ya ce musu, “Abokai, kuna da kifi kuwa?” Suka amsa suka ce, “A’a.”
6 イエズス、網を船の右に下せ、然らば獲物あらん、と曰ひければ、彼等下したるに、魚夥しくして、網を引くこと能はざれば、
Ya ce musu, “Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.” Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi.
7 イエズスの愛し給へる彼弟子ペトロに向ひて、主なり、と云ひしをシモン、ペトロ、主なりと聞くや、裸なりければ上衣を纏ひて湖に飛入り、
Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan.
8 他の弟子等は魚の満てる網を引きつつ船にて來れり、陸を距る事遠からず、凡そ五十間許なりければなり。
Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne.
9 陸に上りて見れば既に炭火ありて、其上に一の魚の乗せられたるあり、又麪ありき。
Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma’yan burodi.
10 イエズス彼等に向ひ、汝等が今獲りたる魚を持來れと曰ひしかば、
Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.”
11 シモン、ペトロ乗りて、大なる魚百五十三尾まで充満たる網を陸に引來りしが、斯くまで夥しかりしかど網は裂けざりき。
Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba.
12 イエズス彼等に、來りて食せよ、と曰ひしに、弟子等其主なることを知りて、汝は誰ぞと敢て問ふ者一人もなかりしが、
Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne.
13 イエズス近づき給ひ、麪を取りて彼等に與へ、魚も亦同じ様にし給へり。
Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin.
14 イエズスが死者の中より復活して、其弟子等に現れ給ひしは是にて既に三度目なりき。
Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.
15 然て彼等食したるに、イエズスシモン、ペトロに曰ひけるは、ヨハネの[子]シモン、汝は此人々に優りて我を愛するか、と。彼、主よ、然り、我が汝を愛するは汝の知り給ふ所なり、と云ひしかばイエズス、我羔を牧せよ、と曰へり。
Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?” Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Ciyar da’ya’yan tumakina.”
16 又再び、ヨハネの[子]シモン、汝は我を愛するか、と曰ひしに、彼、主よ、然り、我が汝を愛するは汝の知り給ふ所なり、と云ひしかばイエズス我羔を牧せよ、と曰へり。
Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?” Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”
17 三度之に向ひて、ヨハネの[子]シモン、汝は我を愛するか、と曰ひしかば、ペトロは、我を愛するかと三度まで言はれたるを憂ひしが、主よ、萬事を知り給へり、我が汝を愛するは汝の知り給ふ所なり、と云ひしに、イエズス之に曰ひけるは、我羊を牧せよ。
Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.” Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina.
18 誠に實に汝に告ぐ、汝若かりし時、自ら帯して好む處を歩み居たりしが、老いたらん後は手を伸べん、而して他の者汝に帯して、其好まざる處に導かん、と。
Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.”
19 是ペトロが如何なる死を遂げて神に光榮あらしむべきかを示して曰ひしなり。然て之を曰ひ果てて、我に從へ、とペトロが曰ひしが、
Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!”
20 ペトロ回顧りてイエズスの愛し居給ひし彼弟子、即ち晩餐の時イエズスの御胸に横はりて、主よ汝を付す者は誰なるぞ、と云ひし弟子の從へるを見たり。
Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”)
21 ペトロ之を見てイエズスに向ひ、主よ、彼は如何に、と云ひしに、
Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?”
22 イエズスペトロに曰ひけるは、我が來るまでに彼の留らん事を命ずとも、汝に於て何かあらん、汝は我に從へ、と。
Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.”
23 然れば彼弟子死せずとの説兄弟等の中に傳はりしが、彼死せず、とイエズスのペトロに曰ひしには非ず、唯我が來るまで彼の留らん事を命ずとも、汝に於て何かあらん、と曰ひしのみ。
Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?”
24 此等の事に就きて證明し、此等の事を書きし人は、即ち彼弟子にして、我等は其證明の眞實なる事を知る。
Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce.
25 然れどイエズスの為し給ひし事尚此他にも夥しく、若之を一々書記さば、我思ふに書記すべき書籍は、世界すらも載盡すこと能はざるべし。
Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.