< ゼカリヤ書 3 >
1 時に主は大祭司ヨシュアが、主の使の前に立ち、サタンがその右に立って、これを訴えているのをわたしに示された。
Sa’an nan ya nuna mini Yoshuwa babban firist a tsaye a gaban mala’ikan Ubangiji, Shaiɗan kuma yana tsaye a damansa don yă tuhume shi.
2 主はサタンに言われた、「サタンよ、主はあなたを責めるのだ。すなわちエルサレムを選んだ主はあなたを責めるのだ。これは火の中から取り出した燃えさしではないか」。
Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ubangiji ya tsawata maka, Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima, ya tsawata maka! Ashe, mutumin nan ba shi ne sandar da take ƙonewa da aka ciro daga cikin wuta ba?”
3 ヨシュアは汚れた衣を着て、み使の前に立っていたが、
Yanzu an sa wa Yoshuwa tufafi masu dauda sa’ad da yake tsaye a gaban mala’ikan.
4 み使は自分の前に立っている者どもに言った、「彼の汚れた衣を脱がせなさい」。またヨシュアに向かって言った、「見よ、わたしはあなたの罪を取り除いた。あなたに祭服を着せよう」。
Mala’ikan ya ce wa waɗanda suke tsaye a gabansa, “Ku cire masa tufafinsa masu dauda.” Sai ya ce wa Yoshuwa, “Duba, na ɗauke zunubanka, zan sa maka tufafi masu tsada.”
5 わたしは言った、「清い帽子を頭にかぶらせなさい」。そこで清い帽子を頭にかぶらせ、衣を彼に着せた。主の使はかたわらに立っていた。
Sai na ce, “Sa masa rawani mai tsabta a kansa.” Aka sa masa rawani mai tsabta a kansa aka kuma sa masa tufafi yayinda mala’ikan Ubangiji yake tsaye a wurin.
Mala’ikan Ubangiji ya yi wa Yoshuwa wannan gargaɗi.
7 「万軍の主は、こう仰せられる、あなたがもし、わたしの道に歩み、わたしの務を守るならば、わたしの家をつかさどり、わたしの庭を守ることができる。わたしはまた、ここに立っている者どもの中に行き来することを得させる。
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘In za ka yi tafiya a hanyoyina ka kuma kiyaye abubuwan da nake so, za ka zama shugaban haikalina, ka kuma lura da ɗakunan shari’ata, zan kuma ba ka wuri cikin waɗannan da suke tsaye a nan.
8 大祭司ヨシュアよ、あなたも、あなたの前にすわっている同僚たちも聞きなさい。彼らはよいしるしとなるべき人々だからである。見よ、わたしはわたしのしもべなる枝を生じさせよう。
“‘Ka saurara, ya babban firist Yoshuwa, kai da abokanka da suke zaune a gabanka, ku da kuke alamun abubuwan da za su zo. Zan kawo bawana, wanda yake Reshe.
9 万軍の主は言われる、見よ、ヨシュアの前にわたしが置いた石の上に、すなわち七つの目をもっているこの一つの石の上に、わたしはみずから文字を彫刻する。そしてわたしはこの地の罪を、一日の内に取り除く。
Dubi dutsen da na ajiye a gaban Yoshuwa! Akwai idanu bakwai a kan wannan dutse guda, zan kuma yi rubutu a kansa,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘zan kuma kawar da zunubin ƙasan nan a rana ɗaya.
10 万軍の主は言われる、その日には、あなたがたはめいめいその隣り人を招いて、ぶどうの木の下、いちじくの木の下に座すのである」。
“‘A wannan rana kowannenku zai gayyaci maƙwabcinsa yă zauna a ƙarƙashin itacen inabi da kuma na ɓaure,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.”