< 雅歌 5 >

1 わが妹、わが花嫁よ、わたしはわが園にはいって、わが没薬と香料とを集め、わが蜜蜂の巣と、蜜とを食べ、わがぶどう酒と乳とを飲む。友らよ、食らえ、飲め、愛する人々よ、大いに飲め。
Na zo lambuna,’yar’uwata, amaryata; na tattara mur nawa da kayan yajina. Na sha zumana da kuma kakinsa na sha ruwan inabina da kuma madarana. Ƙawaye Ku ci, ku kuma sha, ya ku ƙawaye; ku sha ku ƙoshi, ya ƙaunatattu.
2 わたしは眠っていたが、心はさめていた。聞きなさい、わが愛する者が戸をたたいている。「わが妹、わが愛する者、わがはと、わが全き者よ、あけてください。わたしの頭は露でぬれ、わたしの髪の毛は夜露でぬれている」と言う。
Na yi barci amma zuciyata tana a farke. Ku saurara! Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. “Buɗe mini,’yar’uwata, ƙaunatacciyata, kurciyata, marar laifina. Kaina ya jiƙe da raɓa, gashina ya yi danshin ɗiɗɗigar dare.”
3 わたしはすでに着物を脱いだ、どうしてまた着られようか。すでに足を洗った、どうしてまた、よごせようか。
Na tuɓe rigata, sai in sāke sa ta kuma? Na wanke ƙafafuna, sai in sāke ɓata su?
4 わが愛する者が掛けがねに手をかけたので、わが心は内におどった。
Ƙaunataccena ya turo hannunsa ta cikin ramin ƙofar; zuciyata ta fara juyayi a kansa.
5 わたしが起きて、わが愛する者のためにあけようとしたとき、わたしの手から没薬がしたたり、わたしの指から没薬の液が流れて、貫の木の取手の上に落ちた。
Na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena, sai hannuna ya jiƙe sharkaf da mur, yatsotsina suna ɗiga da mur, a hannuwan ƙofar.
6 わたしはわが愛する者のために開いたが、わが愛する者はすでに帰り去った。彼が帰り去ったとき、わが心は力を失った。わたしは尋ねたけれども見つからず、呼んだけれども答がなかった。
Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, amma ƙaunataccena ba ya nan, ya riga ya tafi. Zuciyata ta damu da tafiyarsa. Na neme shi amma ban same shi ba. Na yi ta kiransa amma bai amsa ba.
7 町をまわり歩く夜回りらはわたしを見ると、撃って傷つけ、城壁を守る者らは、わたしの上着をはぎ取った。
Masu gadi suka gamu da ni yayinda suke kai kawo a cikin birni. Suka yi mini dūka, suka yi mini rauni; suka ƙwace gyalena waɗannan masu gadin katanga!
8 エルサレムの娘たちよ、わたしはあなたがたに誓って、お願いする。もしわが愛する者を見たなら、わたしが愛のために病みわずらっていると、彼に告げてください。
’Yan matan Urushalima, ina roƙonku, in kun sami ƙaunataccena me za ku ce masa? Ku ce masa na suma saboda ƙauna.
9 女のうちの最も美しい者よ、あなたの愛する者は、ほかの人の愛する者に、なんのまさるところがあるか。あなたの愛する者は、ほかの人の愛する者に、なんのまさるところがあって、そのように、わたしたちに誓い、願うのか。
Mafiya kyau a cikin mata me ya sa ƙaunataccenki ya fi sauran? Don me kike roƙonmu mu faɗa masa yadda kike ji?
10 わが愛する者は白く輝き、かつ赤く、万人にぬきんで、
Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma, da ƙyar a sami irinsa ɗaya a cikin dubu goma.
11 その頭は純金のように、その髪の毛はうねっていて、からすのように黒い。
Kansa zinariya ce zalla; gashinsa dogaye ne baƙi wuluk kamar hankaka.
12 その目は泉のほとりのはとのように、乳で洗われて、良く落ち着いている。
Idanunsa sun yi kamar na kurciyoyin da suke kusa da ruwan rafi, da aka wanke da madara aka kuma kafa kamar kayan ado masu daraja.
13 そのほおは、かんばしい花の床のように、かおりを放ち、そのくちびるは、ゆりの花のようで、没薬の液をしたたらす。
Kumatunsa kamar lambun kayan yaji suna ba da turare. Leɓunansa sun yi kamar furen bi-rana suna ɗiga da mur.
14 その手は宝石をはめた金の円筒のごとく、そのからだはサファイヤをもっておおった象牙の細工のごとく、
Hannuwansa kamar sandunan zinariyar da aka sa musu duwatsu masu daraja. Jikinsa ya yi kamar gogaggen hauren giwan da aka yi masa ado da duwatsun saffaya.
15 その足のすねは金の台の上にすえた大理石の柱のごとく、その姿はレバノンのごとく、香柏のようで、美しい。
Ƙafafunsa sun yi kamar ginshiƙan dutsen alabastar da aka kafa su a cikin rammukar zinariya. Kamanninsa ya yi kamar Lebanon, mafi kyau kamar itacen al’ul nasa.
16 その言葉は、はなはだ美しく、彼はことごとく麗しい。エルサレムの娘たちよ、これがわが愛する者、これがわが友なのです。
Bakinsa zaƙi ne kansa; komensa yana da kyau. Haka ƙaunataccena, abokina, yake’yan matan Urushalima.

< 雅歌 5 >