< ヨハネの福音書 16 >
1 わたしがこれらのことを語ったのは、あなたがたがつまずくことのないためである。
“Na fada maku wannan ne domin kada kuyi tuntube.
2 人々はあなたがたを会堂から追い出すであろう。更にあなたがたを殺す者がみな、それによって自分たちは神に仕えているのだと思う時が来るであろう。
Zasu fitar da ku daga majami'u. Amma, sa'a tana zuwa, wadda idan wani ya kasheku, zai yi zaton aikin Allah yake yi.
3 彼らがそのようなことをするのは、父をもわたしをも知らないからである。
Za suyi haka ne kuwa domin ba su san Uban ko ni ba.
4 わたしがあなたがたにこれらのことを言ったのは、彼らの時がきた場合、わたしが彼らについて言ったことを、思い起させるためである。これらのことを初めから言わなかったのは、わたしがあなたがたと一緒にいたからである。
Na fada maku wadannan abubuwa ne domin in lokacin da zasu faru yayi, ku tuna na fada maku.” Ban fada maku wadannan abubuwa ba tun da farko, domin ina tare da ku.
5 けれども今わたしは、わたしをつかわされたかたのところに行こうとしている。しかし、あなたがたのうち、だれも『どこへ行くのか』と尋ねる者はない。
Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, 'Ina za ka?'
6 かえって、わたしがこれらのことを言ったために、あなたがたの心は憂いで満たされている。
Amma saboda na fada maku wadannan abubuwa, bakin ciki ya cika zuciyarku.
7 しかし、わたしはほんとうのことをあなたがたに言うが、わたしが去って行くことは、あなたがたの益になるのだ。わたしが去って行かなければ、あなたがたのところに助け主はこないであろう。もし行けば、それをあなたがたにつかわそう。
Amma ina gaya maku gaskiya: zai fi ye maku in na tafi. Domin in ban tafi ba, Mai Ta'aziyya ba zai zo gare ku ba, in kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku.
8 それがきたら、罪と義とさばきとについて、世の人の目を開くであろう。
Idan kuwa ya zo, Mai Ta'aziyyar zai fadarkar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci.
9 罪についてと言ったのは、彼らがわたしを信じないからである。
Game da zunubi, domin basu gaskata da ni ba,
10 義についてと言ったのは、わたしが父のみもとに行き、あなたがたは、もはやわたしを見なくなるからである。
Game da adalci, domin za ni wurin Uba, kuma ba za ku sake ganina ba,
11 さばきについてと言ったのは、この世の君がさばかれるからである。
game da hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulki duniyan nan hukunci.
12 わたしには、あなたがたに言うべきことがまだ多くあるが、あなたがたは今はそれに堪えられない。
“Akwai abubuwa da yawa da zan gaya maku, amma ba za ku iya fahimta a yanzu ba.
13 けれども真理の御霊が来る時には、あなたがたをあらゆる真理に導いてくれるであろう。それは自分から語るのではなく、その聞くところを語り、きたるべき事をあなたがたに知らせるであろう。
Saboda haka, sa'adda Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku a cikin dukan gaskiyar, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai fada, zai kuma sanar da ku al'amuran da zasu faru.
14 御霊はわたしに栄光を得させるであろう。わたしのものを受けて、それをあなたがたに知らせるからである。
Zai daukaka ni, domin zai dauko abubuwa dake nawa ya sanar da ku.
15 父がお持ちになっているものはみな、わたしのものである。御霊はわたしのものを受けて、それをあなたがたに知らせるのだと、わたしが言ったのは、そのためである。
Duk abinda Uba yake da shi, nawa ne. Domin wannan ne nace zai dauko abubuwa da yake nawa ya sanar da ku.
16 しばらくすれば、あなたがたはもうわたしを見なくなる。しかし、またしばらくすれば、わたしに会えるであろう」。
“Bayan dan lokaci kadan, ba zaku kara ganina kuma ba. bayan dan lokaci kadan kuma, zaku gan ni.”
17 そこで、弟子たちのうちのある者は互に言い合った、「『しばらくすれば、わたしを見なくなる。またしばらくすれば、わたしに会えるであろう』と言われ、『わたしの父のところに行く』と言われたのは、いったい、どういうことなのであろう」。
Sai wadansu almajiransa sukace wa juna, “Me nene wannan da yake fadi mana, 'Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni?' da kuma, ' zan tafi wurin Uba'?”
18 彼らはまた言った、「『しばらくすれば』と言われるのは、どういうことか。わたしたちには、その言葉の意味がわからない」。
Saboda haka sukace, “Me nene wannan da yake fada, 'Bayan dan lokaci kadan'? Bamu san abinda yake fada mana ba.”
19 イエスは、彼らが尋ねたがっていることに気がついて、彼らに言われた、「しばらくすればわたしを見なくなる、またしばらくすればわたしに会えるであろうと、わたしが言ったことで、互に論じ合っているのか。
Yesu kuwa ya ga suna so su tambaye shi, sai ya ce masu, “Wato kuna tambayar juna ne abinda nake nufi da cewa, “Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni'?
20 よくよくあなたがたに言っておく。あなたがたは泣き悲しむが、この世は喜ぶであろう。あなたがたは憂えているが、その憂いは喜びに変るであろう。
Hakika, hakika, ina gaya maku, zaku yi kuka da makoki, amma duniya za ta yi farin ciki, zaku cika da bakin ciki, amma bakin cikinku zai koma farin ciki.
21 女が子を産む場合には、その時がきたというので、不安を感じる。しかし、子を産んでしまえば、もはやその苦しみをおぼえてはいない。ひとりの人がこの世に生れた、という喜びがあるためである。
Mace takan ji zafi lokacin da take nakuda don lokacin haihuwa ya zo. Amma da zarar ta haifi jinjirin nan, ba ta kara tunawa da zafin, domin ta na fariciki an haifi mutum a duniya.
22 このように、あなたがたにも今は不安がある。しかし、わたしは再びあなたがたと会うであろう。そして、あなたがたの心は喜びに満たされるであろう。その喜びをあなたがたから取り去る者はいない。
To yanzu dai kuna bakin ciki, amma zan sake ganinku, kuma ba wanda zai iya kwace maku wannan farin ciki.
23 その日には、あなたがたがわたしに問うことは、何もないであろう。よくよくあなたがたに言っておく。あなたがたが父に求めるものはなんでも、わたしの名によって下さるであろう。
A rannan, ba zaku tambaye ni komai ba. Hakika hakika, ina gaya maku, komai kuka roki Uba a cikin sunana zai ba ku shi.
24 今までは、あなたがたはわたしの名によって求めたことはなかった。求めなさい、そうすれば、与えられるであろう。そして、あなたがたの喜びが満ちあふれるであろう。
Harwa yau, ba ku roki komai cikin sunana ba. Ku roka, zaku karba, domin farin cikin ku ya zama cikakke.”
25 わたしはこれらのことを比喩で話したが、もはや比喩では話さないで、あからさまに、父のことをあなたがたに話してきかせる時が来るであろう。
“Na fada maku wadannan abubuwa cikin karin magana. Amma sa'a tana zuwa da ba zan kara fada maku komai ba cikin karin magana, amaimakon haka zan gaya maku komai a sarari game da Uba.
26 その日には、あなたがたは、わたしの名によって求めるであろう。わたしは、あなたがたのために父に願ってあげようとは言うまい。
A ranar nan, zaku yi roko a cikin sunana kuma bance maku zan yi addu'a ga Uba a madadinku ba,
27 父ご自身があなたがたを愛しておいでになるからである。それは、あなたがたがわたしを愛したため、また、わたしが神のみもとからきたことを信じたためである。
domin Uba da kansa yana kaunarku, domin kun kaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito.
28 わたしは父から出てこの世にきたが、またこの世を去って、父のみもとに行くのである」。
Daga wurin Uban na fito, kuma na shigo duniya. Har wa yau, kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”
29 弟子たちは言った、「今はあからさまにお話しになって、少しも比喩ではお話しになりません。
Almajiransa sukace, duba, “Yanzu kake magana a sarari, ba cikin karin magana ba!
30 あなたはすべてのことをご存じであり、だれもあなたにお尋ねする必要のないことが、今わかりました。このことによって、わたしたちはあなたが神からこられたかたであると信じます」。
Yanzu mun sani ka san komai, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.”
31 イエスは答えられた、「あなたがたは今信じているのか。
Yesu ya amsa masu yace, “Ashe, yanzu kun gaskata?
32 見よ、あなたがたは散らされて、それぞれ自分の家に帰り、わたしをひとりだけ残す時が来るであろう。いや、すでにきている。しかし、わたしはひとりでいるのではない。父がわたしと一緒におられるのである。
Duba, sa'a na zuwa, I, sa'ar ta yi, da za a warwatsa ku, kowa ya koma gidansa, kuma ku bar ni ni kadai. Duk da haka kuwa ba ni kadai nake ba, domin Ubana yana tare da ni.
33 これらのことをあなたがたに話したのは、わたしにあって平安を得るためである。あなたがたは、この世ではなやみがある。しかし、勇気を出しなさい。わたしはすでに世に勝っている」。
Na fada maku wannan ne domin a ciki na ku sami salama. A duniya kuna shan tsanani, amma ku karfafa: na yi nasara da duniya,”