< サムエル記Ⅱ 11 >
1 春になって、王たちが戦いに出るに及んで、ダビデはヨアブおよび自分と共にいる家来たち、並びにイスラエルの全軍をつかわした。彼らはアンモンの人々を滅ぼし、ラバを包囲した。しかしダビデはエルサレムにとどまっていた。
Da bazara, a lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, sai Dawuda ya aiki Yowab tare da mutanen sarki, da dukan Isra’ila. Suka je suka hallaka Ammonawa, suka kuma yi wa Rabba kwanton ɓauna. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.
2 さて、ある日の夕暮、ダビデは床から起き出て、王の家の屋上を歩いていたが、屋上から、ひとりの女がからだを洗っているのを見た。その女は非常に美しかった。
Wata rana da yamma, Dawuda ya tashi daga gadonsa, ya zaga kewaye a rufin fadansa. Daga rufin ya ga wata mace tana wanka. Matar kyakkyawa ce ƙwarai.
3 ダビデは人をつかわしてその女のことを探らせたが、ある人は言った、「これはエリアムの娘で、ヘテびとウリヤの妻バテシバではありませんか」。
Sai Dawuda ya aiki wani yă bincika ko wace ce ita, sai mutumin ya dawo ya ce, “Wannan ba Batsheba ba ce,’yar Eliyam matar Uriya, mutumin Hitti?”
4 そこでダビデは使者をつかわして、その女を連れてきた。女は彼の所にきて、彼はその女と寝た。(女は身の汚れを清めていたのである。)こうして女はその家に帰った。
Sa’an nan Dawuda ya aiki manzanni su kawo masa ita. Ta zo wurinsa shi kuma ya kwana da ita (A lokacin kuwa ta gama tsarkake kanta ke nan daga jinin haila.) Sa’an nan ta tafi gida.
5 女は妊娠したので、人をつかわしてダビデに告げて言った、「わたしは子をはらみました」。
Matar ta yi ciki, ta kuwa aika wa Dawuda, tana cewa, “Ina da ciki.”
6 そこでダビデはヨアブに、「ヘテびとウリヤをわたしの所につかわせ」と言ってやったので、ヨアブはウリヤをダビデの所につかわした。
Saboda haka Dawuda ya aika saƙo wa Yowab ya ce, “Ka aiko mini da Uriya mutumin Hitti.” Yowab kuwa ya aika da shi wajen Dawuda.
7 ウリヤがダビデの所にきたので、ダビデは、ヨアブはどうしているか、民はどうしているか、戦いはうまくいっているかとたずねた。
Da Uriya ya zo wurinsa, sai Dawuda ya tambaye shi lafiyar Yowab da sojojin, da kuma yaya yaƙin yake tafiya.
8 そしてダビデはウリヤに言った、「あなたの家に行って、足を洗いなさい」。ウリヤは王の家を出ていったが、王の贈り物が彼の後に従った。
Sa’an nan Dawuda ya ce wa Uriya, “Gangara gidanka ka wanke ƙafafunka.” Saboda haka Uriya ya bar fadar, sarki kuma ya aika masa da kyauta.
9 しかしウリヤは王の家の入口で主君の家来たちと共に寝て、自分の家に帰らなかった。
Amma Uriya ya kwanta a ƙofar fada tare da dukan bayin maigidansa, bai kuwa tafi gidansa ba.
10 人々がダビデに、「ウリヤは自分の家に帰りませんでした」と告げたので、ダビデはウリヤに言った、「旅から帰ってきたのではないか。どうして家に帰らなかったのか」。
Da aka gaya wa Dawuda, “Uriya bai tafi gida ba,” sai Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Ba ka zo daga wuri mai nisa ba? Me ya sa ba ka je gida ba?”
11 ウリヤはダビデに言った、「神の箱も、イスラエルも、ユダも、小屋の中に住み、わたしの主人ヨアブと、わが主君の家来たちが野のおもてに陣を取っているのに、わたしはどうして家に帰って食い飲みし、妻と寝ることができましょう。あなたは生きておられます。あなたの魂は生きています。わたしはこの事をいたしません」。
Sai Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin Alkawari, da Isra’ila, da Yahuda suna zama cikin tentuna, kuma maigidana Yowab da mutanen ranka yă daɗe suna a sansani a fili. Yaya zan je gidana in ci in sha in kuma kwana da matata? Muddin kana a raye, ba zan yi irin wannan abu ba!”
12 ダビデはウリヤに言った、「きょうも、ここにとどまりなさい。わたしはあす、あなたを去らせましょう」。そこでウリヤはその日と次の日エルサレムにとどまった。
Sai Dawuda ya ce masa, “Ka ƙara dakata a nan kwana ɗaya, gobe kuwa in sallame ka.” Saboda haka Uriya ya dakata a Urushalima a ranar, da kuma ta biye.
13 ダビデは彼を招いて自分の前で食い飲みさせ、彼を酔わせた。夕暮になって彼は出ていって、その床に、主君の家来たちと共に寝た。そして自分の家には下って行かなかった。
Dawuda ya gayyace shi, ya kuwa ci ya sha tare da shi, Dawuda ya sa ya bugu tilis. Amma da yamma Uriya ya koma ya kwanta a tabarmarsa cikin bayin maigidan sarki; bai je gida ba.
14 朝になってダビデはヨアブにあてた手紙を書き、ウリヤの手に託してそれを送った。
Da safe Dawuda ya rubuta wa Yowab wasiƙa ya ba wa Uriya.
15 彼はその手紙に、「あなたがたはウリヤを激しい戦いの最前線に出し、彼の後から退いて、彼を討死させよ」と書いた。
A ciki wasiƙar ya rubuta, “Tura Uriya a gaba inda yaƙi ya fi zafi. Sa’an nan ka janye daga gare shi don a buge shi yă mutu.”
16 ヨアブは町を囲んでいたので、勇士たちがいると知っていた場所にウリヤを置いた。
Saboda haka yayinda Yowab ya kai yaƙi kusa da birnin, sai tura Uriya a inda ya sani akwai jarumawan Ammon na gaske.
17 町の人々が出てきてヨアブと戦ったので、民のうち、ダビデの家来たちにも、倒れるものがあり、ヘテびとウリヤも死んだ。
Sa’ad da mutanen garin suka fito suka yaƙi Yowab, sai waɗansu mutane daga sojojin Dawuda suka mutu; Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.
18 ヨアブは人をつかわして戦いのことをつぶさにダビデに告げた。
Yowab ya aika wa Dawuda cikakken labari batun yaƙin.
19 ヨアブはその使者に命じて言った、「あなたが戦いのことをつぶさに王に語り終ったとき、
Ya umarci manzon ya ce, “Da ka gama yin wa sarki wannan batun yaƙin,
20 もし王が怒りを起して、『あなたがたはなぜ戦おうとしてそんなに町に近づいたのか。彼らが城壁の上から射るのを知らなかったのか。
wataƙila sarki yă husata, yă tambaye ka, ‘Me ya sa kuka je kusa da birnin don ku yi yaƙi? Ba ku san cewa za su yi harbi daga katanga ba?
21 エルベセテの子アビメレクを撃ったのはだれか。ひとりの女が城壁の上から石うすの上石を投げて彼をテベツで殺したのではなかったか。あなたがたはなぜそんなに城壁に近づいたのか』と言われたならば、その時あなたは、『あなたのしもべ、ヘテびとウリヤもまた死にました』と言いなさい」。
Wane ne ya kashe Abimelek ɗan Yerub-Beshet? Ba mace ce ta jefa dutsen niƙa a kansa daga katanga, ta haka ya mutu a Tebez ba? Me ya sa kuka je kurkusa da katangar?’ In ya tambaye ka wannan, sai ka ce masa, ‘Har bawanka Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.’”
22 こうして使者は行き、ダビデのもとにきて、ヨアブが言いつかわしたことをことごとく告げた。
Manzon ya tashi ya tafi, da ya iso kuwa sai ya gaya wa Dawuda dukan abin da Yowab ya aike shi yă faɗa.
23 使者はダビデに言った、「敵はわれわれよりも有利な位置を占め、出てきてわれわれを野で攻めましたが、われわれは町の入口まで彼らを追い返しました。
Manzon ya ce wa Dawuda, “Mutanen sun sha kanmu suka fito suka yaƙe mu a fili, amma muka kore su har ƙofar birni.
24 その時、射手どもは城壁からあなたの家来たちを射ましたので、王の家来のある者は死に、また、あなたの家来ヘテびとウリヤも死にました」。
Sa’an nan maharba suka yi ta harbi daga katanga har waɗansu mutanen sarki suka mutu. Ban da haka ma, Uriya mutumin Hitti bawan sarki ya mutu.”
25 ダビデは使者に言った、「あなたはヨアブにこう言いなさい、『この事で心配することはない。つるぎはこれをも彼をも同じく滅ぼすからである。強く町を攻めて戦い、それを攻め落しなさい』と。そしてヨアブを励ましなさい」。
Dawuda ya ce wa manzon, “Ka gaya wa Yowab, ‘Kada ka bar wannan yă dame ka; yadda takobi ya lamushe wannan, haka zai lamushe wancan ma. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku hallaka shi.’ Ka faɗa haka don ka ƙarfafa Yowab.”
26 ウリヤの妻は夫ウリヤが死んだことを聞いて、夫のために悲しんだ。
Da matar Uriya ta ji cewa mijinta ya mutu, sai ta yi makoki saboda shi.
27 その喪が過ぎた時、ダビデは人をつかわして彼女を自分の家に召し入れた。彼女は彼の妻となって男の子を産んだ。しかしダビデがしたこの事は主を怒らせた。
Bayan kwanakin makoki suka ƙare, Dawuda ya sa aka kawo ta gidansa, ta kuwa zama matarsa, ta kuma haifa masa ɗa. Sai dai abin da Dawuda ya yi bai gamshi Ubangiji ba.