< マルコの福音書 4 >

1 彼は再び海辺で教え始めた。大群衆が彼のもとに集まって来た。そのため彼は,海上の舟の中に入って座った。群衆は皆,海辺の陸地にいた。
Ya kuma fara koyarwa a bakin teku. Akwai babban taro kewaye da shi, sai ya shiga cikin jirgin ruwa a cikin tekun, ya kuwa zauna. Duk taron kuwa na kan tudu a bakin tekun.
2 彼はたとえを用いて多くの事を教え,自分の教えの中で人々に言った,
Ya koya masu abubuwa da yawa da misalai, a cikin koyawarsa ya ce masu,
3 「聞きなさい! 見よ,ある耕作人が種をまきに出かけた。
“ku saurara! wani mai shuka ya tafi shuka.
4 そして,種をまいているときのこと,ある種は道ばたに落ち,鳥たちがやって来て,それをむさぼり食ってしまった。
Yana cikin yafa iri, sai wadansu iri suka fadi a kan hanya, tsuntsaye kuma suka zo suka tsince su.
5 別の種は土の少ない岩地の上に落ちた。そして,土が深くなかったので,すぐに芽を出した。
Wadansu kuma suka fadi a kan dutse inda ba kasa dayawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin kasa.
6 太陽が昇ると焦がされ,根がないために枯れ果ててしまった。
Da rana fa ta daga, sai suka yankwane da yake ba su da saiwa sosai, sai suka bushe.
7 別の種はイバラの間に落ち,イバラが伸びて来てそれをふさぎ,それは実を生じなかった。
Wadansu kuma suka fadi cikin kayayuwa su ka yi girma sai kayayuwan suka shake su, ba su yi tsaba ba.
8 それ以外の種は良い土に落ち,成長して大きくなり,実を生じた。あるものは三十倍,あるものは六十倍,あるものは百倍もの実を生み出した」 。
Wadansu kuma suka fadi a kasa mai kyau, suka yi yabanya, suka yi tsaba, suka yi girma, wadansu ribi talattin wadansu sittin, wadansu kuma dari”.
9 彼は言った,「だれでも聞く耳のある者は聞きなさい」 。
Sai ya ce, Duk mai kunnen ji, ya ji,”
10 彼がひとりになった時,十二人と共に彼の周りにいた者たちは,このたとえについて彼に尋ねた。
Sa'adda Yesu yake shi kadai, wadanda suke kusa dashi tare da sha biyun suka tambaye shi ma'anar misalan.
11 彼は彼らに言った,「あなた方には神の王国の秘密が与えられているが,外にいる者たちにはすべての事がたとえで与えられる。
Sai ya ce masu, “ku an yardar maku, ku san asirin mulkin Allah, amma ga wadanda ba su cikinku, komai sai a cikin Misalai,
12 それは,『彼らが見るには見るが分からず,聞くには聞くが理解せず,何かの拍子に立ち返って,その罪が許されることのないため』だ」 。
don gani da ido sun gani, amma ba su gane ba. ji kuma, sun ji, amma ba su fahimta ba, don kada su juyo a gafarta masu,”
13 彼らに言った,「あなた方はこのたとえが理解できないのか。どのようにしてほかのすべてのたとえを理解するつもりなのか。
Ya ce masu, “Ashe, ba ku fahimci wannan misalin ba? yaushe za ku fahimci sauran?
14 耕作人はみ言葉をまくのだ。
Mai shukan nan fa maganar Allah yake shukawa.
15 道ばたにみ言葉がまかれたものとは,こういう人たちのことだ。彼らが聞くと,すぐにサタンがやって来て,彼らの内にまかれたみ言葉を取り去るのだ。
Wadanda suka fadi a hanyar kuwa, su ne kwatancin wadanda. a aka shuka mganar a zuciyarsu, Da suka ji, nan da nan sai shaidan ya zo ya dauke Maganar da aka shuka a zuciyarsu.
16 同じように,岩地の上にまかれたものとは,こういう人たちのことだ。み言葉を聞くと,喜んですぐに受け入れる。
Haka kuma wadanda aka shuka a wuri mai duwatsu, sune wadanda da zarar sun ji Maganar sai su karba da farin ciki.
17 自分の内に根がないので,短命だ。み言葉のために圧迫や迫害が生じると,すぐにつまずく。
Su kuwa basu da tushe, ba su da karfi, idan kunci ko tsanani ya zo saboda kalmar, nan da nan sai su yi tuntube.
18 イバラの間にまかれたものとは,別の者たちのことだ。これはみ言葉を聞いた人たちだが,
Wadansu kuma su ne kwatacin wadanda suka fadi cikin kayayuwa, sune wadanda suka ji Maganar,
19 この時代の思い煩いや,富の欺きや,ほかの物事に関する欲望が入り込んでみ言葉をふさぎ,それは実を結ばなくなる。 (aiōn g165)
amma abubuwan duniya, da rudin dukiya da kuma kwadayin wadansu abubuwa, sukan shiga su shake Maganar, har ta zama marar amfani. (aiōn g165)
20 良い土の上にまかれたものとは,こういう人たちのことだ。み言葉を聞いて受け入れ,ある者は三十倍,ある者は六十倍,ある者は百倍の実を結ぶのだ」 。
Wadanda aka shuka a kasa mai kyau kuwa, sune kwatancin wadanda suke jin Maganar, su karba, su kuma yin amfani da ita wadansu ribi talatin, wadansu sittin, wadansu dari.”
21 彼らに言った,「ともし火が持って来られるのは,かごの下や寝台の下に置かれるためだろうか。燭台の上に置かれるためではないか。
ya ce masu, “Shin, ana kawo fitila a cikin gida don a rufe ta da kwando ko a ajiye ta a karkashin gado? ku kan kawo ta ne don ku dora ta a kan madorinta.
22 というのは,知られるためでないのに隠されているものはなく,明るみに出るためでないのに秘密にされているものはないからだ。
Ba abin da yake boye, da baza a sani ba ko kuma ba abinda ke asirce da bazaya bayyana a fili ba.
23 だれでも聞く耳のある者は聞きなさい」 。
Bari mai kunnen ji, ya ji!''
24 彼らに言った,「自分が聞いていることに注意を払いなさい。あなた方が量るそのはかりで,あなた方に量られるだろう。そして,聞いている者にはさらに与えられるだろう。
Sai ya ce masu, ku mai da hankali a kan abin da kuka ji, Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a kara maka.
25 持っている者にはさらに与えられ,持っていない者からは持っているものまでも取り去られることになるからだ」 。
Domin mai abu akan karawa, marar abu kuma za a karba daga wurinsa a kuma karawa mai shi.”
26 彼は言った,「神の王国は次のようなものだ。人が地に種をまき,
Sai ya ce, “Mulkin Allah kamar mutum yake mai yafa iri a kasa.
27 夜昼,寝起きしているうちに,種は芽が出て成長する。どのようにしてかを彼は知らない。
A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma bai kuwa san ta yaya aka yi ba.
28 地が実を生み出すのであって,最初に葉,それから穂,それから豊かな穀粒を生み出すからだ。
Kasa da kanta, takan ba da amfani, tsiro shine ne na farko,
29 しかし,実が熟するとすぐに彼はかまを入れる。収穫の時が来たからだ」 。
Sai kai, sa'anan sai kwaya mai kwari. Sa, adda amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nan da nan, wato kaka ta yi kenan.”
30 彼は言った,「わたしたちは,神の王国をどのようにたとえようか。あるいは,どんなたとえで説明しようか。
Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta Mulki Allah? ko kuwa da wane misali za mu misalta shi?
31 それは一粒のからしの種のようなものだ。それは,地にまかれる時は地上のあらゆる種よりも小さい。
Kamar kwayar zarra yake wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi kankanta cikin kwayoyi a duniya.
32 だがいったんまかれると,成長し,あらゆる草よりも大きくなり,大きな枝を張り,その陰で空の鳥たちが巣を作れるほどになる」 。
Duk da haka in an shuka ta, sai ta yi girma fiye da duk sauran ita-tuwan da ke a jeji tayi manyan rassa, har tsuntsaye su iya yin sheka arassanta.”
33 彼は,人々の聞くことができる程度に応じて,このようなたとえを多く用いてみ言葉を語った。
Da misalai da yawa, irin wadannan ya yi masu Magana, dadai gwargwadon ganewarsu,
34 たとえなしでは人々に語らなかった。しかし,弟子たちに対しては,ひそかにすべてのことを説明した。
ba ya fada masu kome sai da misali, amma a kebe, yakan bayyana wa almajiransa dukan abu.
35 その日,夕方になった時,彼は彼らに「向こう岸に渡ろう」 と言った。
A ranan nan da yama ta yi yace masu “Mu haye wancan ketaren.”
36 彼らは,群衆を残して,舟に乗っているままで彼を連れて行った。他の小舟も彼と共にいた。
Sai suka bar taron, suka tafi tare da shi acikin cikin jirgin. wadansu jirage kuma na tare da shi.
37 激しい風あらしが起こり,波が舟の中に打ちつけて,舟はもはや水でいっぱいになるほどであった。
Sai babban hadari da iska mai karfi ya taso, rakuman ruwa kuma na ta girgizawa cikin jirgin, har jirgin ya cika.
38 彼自身は船尾にいて,まくらをして眠っていた。そこで彼らは彼を起こして告げた,「先生,わたしたちが死にかかっていても平気なのですか」。
Yesu kuwa na daga karshen bayan jirgin a kan kujera, yana barci, sai suka tashe shi, suka ce masa “Malam za mu hallaka ba ka kula ba?”
39 彼は目を覚まし,風をしかりつけ,海に言った,「静まれ! 静かになれ!」 風はやみ,大なぎになった。
Sai ya farka, ya tsawata wa Iskar. Ya kuma ce wa ruwan tekun, “Ka natsu! ka yi shiru!” Sai Iskar ta kwanta, wurin duk ya yi shiru.
40 彼は彼らに言った,「なぜそんなに恐れるのか。信仰がないのはどうしてか」 。
Ya ce masu, “Don me kuka firgita haka? Har yanzu baku da bangaskiya ne?”
41 彼らは非常に恐れて,互いに言い合った,「風や海さえも従うとは,いったいこの方はどなただろう」。
Sai suka tsorata kwarai suka ce wa juna, “wanene wannan kuma, wanda har Iska da teku ma suke yi masa biyayya?”

< マルコの福音書 4 >