< ローマ人への手紙 9 >
Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki.
2 我に大なる憂あることと心に絶えざる痛あることとを、我が良心も聖 靈によりて證す。
Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata.
3 もし我が兄弟わが骨肉の爲にならんには、我みづから詛はれてキリストに棄てらるるも亦ねがふ所なり。
Gama da so na ne, sai a la’anta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda’yan’uwana, waɗannan na kabilata,
4 彼 等はイスラエル人にして、彼らには神の子とせられたることと、榮光と、もろもろの契約と、授けられたる律法と、禮拜と、もろもろの約束とあり。
mutanen Isra’ila. Su ne Allah ya mai da su’ya’yansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawura.
5 先祖たちも彼 等のものなり、肉によれば、キリストも彼 等より出で給ひたり。キリストは萬物の上にあり、永遠に讃むべき神なり、アァメン。 (aiōn )
Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin. (aiōn )
6 それ神の言は廢りたるに非ず。イスラエルより出づる者みなイスラエルなるに非ず。
Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Isra’ila ne suke Isra’ila na gaske ba.
7 また彼 等はアブラハムの裔なればとて皆その子たるに非ず『イサクより出づる者は、なんぢの裔と稱へらるべし』とあり。
Ba kuwa don su zuriyarsa ne dukansu suka zama’ya’yan Ibrahim ba. A maimako, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.”
8 即ち肉の子らは神の子らにあらず、ただ約束の子 等のみ其の裔と認めらるるなり。
Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama’ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim.
9 約束の御言は是なり、曰く『時ふたたび巡り來らば、我きたりてサラに男子あらん』と。
Ga yadda aka yi alkawarin nan, “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za tă haifi ɗa.”
10 然のみならず、レベカも我らの先祖イサク一人によりて孕りたる時、
Ba ma haka kaɗai ba,’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku.
11 その子いまだ生れず、善も惡もなさぬ間に、神の選の御旨は動かず、
Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa,
12 行爲によらで召す者によらん爲に『兄は次弟に事ふべし』とレベカに宣へり。
ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.”
13 『われヤコブを愛しエザウを憎めり』と録されたる如し。
Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.”
14 さらば何をか言はん、神には不義あるか。決して然らず。
Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan!
15 モーセに言ひ給ふ『われ憐まんとする者をあはれみ、慈悲を施さんとする者に慈悲を施すべし』と。
Gama ya ce wa Musa, “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai, zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”
16 されば欲する者にも由らず、走る者にも由らず、ただ憐みたまふ神に由るなり。
Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah.
17 パロにつきて聖書に言ひ給ふ『わが汝を起したるは此の爲なり、即ち我が能力を汝によりて顯し、且わが名の全世界に傳へられん爲なり』と。
Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.”
18 されば神はその憐まんと欲する者を憐み、その頑固にせんと欲する者を頑固にし給ふなり。
Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.
19 さらば汝あるいは我に言はん『神なんぞなほ人を咎め給ふか、誰かその御定に悖る者あらん』
Waninku zai iya ce mini, “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?”
20 ああ人よ、なんぢ誰なれば神に言ひ逆ふか、造られしもの造りたる者に對ひて『なんぢ何ぞ我を斯く造りし』と言ふべきか。
Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’”
21 陶工は同じ土塊をもて、此を貴きに用ふる器とし、彼を賤しきに用ふる器とするの權なからんや。
Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?
22 もし神、怒をあらはし權力を示さんと思しつつも、なほ大なる寛容をもて、滅亡に備れる怒の器を忍び、
Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka?
23 また光榮のために預じめ備へ給ひし憐憫の器に對ひて、その榮光の富を示さんとし給ひしならば如何に。
Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka
24 この憐憫の器は我等にして、ユダヤ人の中よりのみならず、異邦人の中よりも召し給ひしものなり。
har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai?
25 ホゼヤの書に『我わが民たらざる者を我が民と呼び、愛せられざる者を愛せらるる者と呼ばん、
Kamar yadda ya faɗa a Hosiya. “Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba; zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,”
26 「なんぢら我が民にあらず」と言ひし處にて、彼らは活ける神の子と呼ばるべし』と宣へる如し。
kuma, “Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba,’ za a ce da su, ‘’ya’yan Allah mai rai.’”
27 イザヤもイスラエルに就きて叫べり『イスラエルの子孫の數は海の砂のごとくなりとも、救はるるはただ殘の者のみならん。
Ishaya ya ɗaga murya game da Isra’ila ya ce, “Ko da yake yawan Isra’ilawa yana kama da yashi a bakin teku, ragowa ce kaɗai za su sami ceto.
28 主、地の上に御言をなし了へ、これを遂げ、これを速かにし給はん』
Gama Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a bisan duniya da sauri kuma ba da ɓata lokaci ba.”
29 また『萬軍の主われらに裔を遺し給はずば、我等ソドムの如くになり、ゴモラと等しかりしならん』とイザヤの預言せしが如し。
Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa. “Da ba don Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana zuriya ba, da mun zama kamar Sodom, da mun kuma zama kamar Gomorra.”
30 然らば何をか言はん、義を追ひ求めざりし異邦人は義を得たり、即ち信仰による義なり。
Me za mu ce ke nan? Ai, Al’ummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya;
31 イスラエルは義の律法を追ひ求めたれど、その律法に到らざりき。
amma Isra’ila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba.
32 何の故か、かれらは信仰によらず、行爲によりて追ひ求めたる故なり。彼らは躓く石に躓きたり。
Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen binta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.”
33 録して『視よ、我つまづく石さまたぐる岩をシオンに置く、之に依頼む者は辱しめられじ』とあるが如し。
Kamar yadda yake a rubuce, “Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe da kuma dutsen da yake sa su fāɗi wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.”