< マタイの福音書 14 >
A lokacin nan ne, Hiridus mai mulki ya ji labarin Yesu.
2 侍臣どもに言ふ『これバプテスマのヨハネなり。かれ死人の中より甦へりたり、さればこそ此 等の能力その内に働くなれ』
Ya ce wa barorinsa, “Wannan Yahaya mai baftisma ne; ya tashi daga matattu. Saboda haka wadannan ikoki na aiki a cikinsa”.
3 ヘロデ先に、己が兄弟ピリポの妻ヘロデヤの爲にヨハネを捕へ、縛りて獄に入れたり。
Domin Hiridus ya kama Yahaya, ya daure shi, kuma ya jefa shi a kurkuku saboda Hirudiya, matar dan'uwansa Filibus.
4 ヨハネ、ヘロデに『かの女を納るるは宜しからず』と言ひしに因る。
Ya ce masa, “Bai kamata ka dauke ta a matsayin matarka ba.”
5 かくてヘロデ、ヨハネを殺さんと思へど、群衆を懼れたり。群衆ヨハネを預言者とすればなり。
Da Hirudus ya kashe shi, amma yana tsoron jama'a, domin sun dauke shi a matsayin annabi.
6 然るにヘロデの誕生日に當り、ヘロデヤの娘その席上に舞をまひてヘロデを喜ばせたれば、
Amma da ranar bikin haihuwar Hirudus ta kewayo, diyar Hirudiya tayi rawa a lokacin har ta burge Hirudus.
7 ヘロデ之に何にても求むるままに與へんと誓へり。
Sai ya yi mata alkawari har da rantsuwa cewa ta roki komenene ta ke so, zai ba ta.
8 娘その母に唆かされて言ふ『バプテスマのヨハネの首を盆に載せてここに賜はれ』
Bayan ta amshi umurni daga wurin mahaifiyarta, ta ce, “Ka bani kan Yahaya mai baptisma a kan tire.
9 王 憂ひたれど、その誓と席に在る者とに對して、之を與ふることを命じ、
Sarki ya husata da rokonta, amma domin rantsuwar da ya yi kuma domin mutanen da ke a wurin bukin tare da shi, sai ya umurta a yi haka.
Ya aika aka yanke kan Yahaya acikin kurkuku.
11 その首を盆にのせて持ち來らしめ、之を少女に與ふ。少女はこれを母に捧ぐ。
Sai aka kawo kansa bisa tire, aka mika wa yarinyar, ta kuwa kai wa mahaifiyarta.
12 ヨハネの弟子たち來り、屍體を取りて葬り、往きて、イエスに告ぐ。
Sai almajiransa suka zo, su ka dauki gawar su ka je su ka yi jana'iza. Bayan haka, su ka je su ka fada wa Yesu.
13 イエス之を聞きて人を避け、其處より舟にのりて寂しき處に往き給ひしを群衆ききて町々より徒歩にて從ひゆく。
Sa'adda da Yesu ya ji haka, ya fita daga cikin kwale-kwale zuwa wani kebabben wuri. Da taron suka ji haka, suka bi shi da kafa daga biranen.
14 イエス出でて大なる群衆を見、これを憫みて、その病める者を醫し給へり。
Sai Yesu ya zo gabansu, ya kuma ga babban taron. Ya tausaya masu ya kuwa warkar da marasa lafiya dake cikinsu.
15 夕になりたれば、弟子たち御許に來りて言ふ『ここは寂しき處、はや時も晩し、群衆を去らしめ、村々に往きて、己が爲に食物を買はせ給へ』
Da maraice ya yi, almajiransa su ka zo su ka ce masa, “Wannan wuri jeji ne, dare kuwa ya riga ya yi. Ka sallami taron domin su je cikin kauyukan nan, su sayo wa kansu abinci.”
16 イエス言ひ給ふ『かれら往くに及ばず、汝ら之に食物を與へよ』
Amma Yesu ya ce masu, “Babu amfanin tafiyar su, ku basu abin da za su ci.”
17 弟子たち言ふ『われらが此處にもてるは、唯 五つのパンと二つの魚とのみ』
Suka ce masa, “Muna da gurasa guda biyar da kifi biyu ne kawai.”
Yesu ya ce, “Ku kawo mani su.”
19 かくて群衆に命じて草の上に坐せしめ、五つのパンと二つの魚とを取り、天を仰ぎて祝し、パンを裂きて、弟子たちに與へ給へば、弟子たち之を群衆に與ふ。
Sai Yesu ya umarci taron su zauna akan ciyawa. Ya dauki gurasa biyar da kifi biyun. Ya dubi sama, ya sa albarka ya gutsuttsura ya kuma ba almajiran. Almajiran suka ba taron.
20 凡ての人 食ひて飽く、裂きたる餘を集めしに十二の筐に滿ちたり。
Dukansu suka ci suka koshi. Sai suka dauki gutsattsarin gurasa da kifin, kwanduna goma sha biyu cike.
21 食ひし者は、女と子供とを除きて凡そ五 千 人なりき。
Wadanda su ka ci kuwa kimanin maza dubu biyar ne, ban da mata da yara.
22 イエス直ちに弟子たちを強ひて舟に乘らせ、自ら群衆をかへす間に、彼方の岸に先に往かしむ。
Nan take sai ya sa almajiran suka shiga kwale-kwalen su haye zuwa dayan gefen kafin shi, domin ya sallami taron.
23 かくて群衆を去らしめてのち、祈らんとて竊に山に登り、夕になりて獨そこにゐ給ふ。
Bayan ya sallami taron sun tafi, sai ya haura kan dutse domin yayi addu'a. Da dare yayi, yana can shi kadai.
24 舟ははや陸より數丁はなれ、風 逆ふによりて波に難されゐたり。
Amma yanzu fa kwale-kwalen na tsakiyar tekun, kuma da wuyar sarrafawa saboda rakuman ruwa da iska na gaba da su.
25 夜明の四時ごろ、イエス海の上を歩みて、彼らに到り給ひしに、
Da asuba (wajen karfe uku na dare) Yesu ya nufo su yana tafiya akan teku.
26 弟子たち其の海の上を歩み給ふを見て心 騷ぎ、變化の者なりと言ひて懼れ叫ぶ。
Da almajiran suka ganshi yana tafiya akan tekun, sai suka firgita suna cewa, “Fatalwa ce,” suka yi kururuwa cikin tsoro.
27 イエス直ちに彼らに語りて言ひたまふ『心 安かれ、我なり、懼るな』
Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, “Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro.”
28 ペテロ答へて言ふ『主よ、もし汝ならば我に命じ、水を蹈みて御許に到らしめ給へ』
Bitrus ya amsa masa cewa, “Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan.”
29 『來れ』と言ひ給へば、ペテロ舟より下り、水の上を歩みてイエスの許に往く。
Yesu yace, “Zo” Sai Bitrus ya fita daga jirgin yana tafiya akan ruwan zuwa wurin Yesu.
30 然るに風を見て懼れ、沈みかかりければ、叫びて言ふ『主よ、我を救ひたまへ』
Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”
31 イエス直ちに御手を伸べ、これを捉へて言ひ給ふ『ああ信仰うすき者よ、何ぞ疑ふか』
Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, “Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?”
Bayan da Yesu da Bitrus suka shiga cikin kwale-kwalen, sai iska ta daina kadawa.
33 舟に居る者どもイエスを拜して言ふ『まことに汝は神の子なり』
Sai almajiran dake cikin kwale-kwalen su ka yi wa Yesu sujada suna cewa, “Hakika kai Dan Allah ne.”
Da suka haye, sun iso kasar Janisarata.
35 その處の人々イエスを認めて、あまねく四方に人をつかはし、又すべての病める者を連れきたり、
Da mutanen wurin suka gane Yesu, sai suka aika da sako zuwa dukan yankin, kuma suka kawo masa dukan marasa lafiya.
36 ただ御衣の總にだに觸らしめ給はんことを願ふ、觸りし者はみな醫されたり。
Suka roke shi don su taba gezar rigarsa, kuma dukan wadanda suka taba shi sun warke.